Part 15

16 1 0
                                    

👉🏽MIEMAH 👈🏽

                  Page 15

🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
   🍃🍃🍃🍃🍃🍃
        🌾🌾🌾🌾
              🌺🌺🌺

Typing 📲
      Story and written ✍ by
Khadija yusuf abba
 
Follow me on wattpad @khadija yusufbaba 🤟🏽🤟🏽🤟🏽

Bismillahir-rahmir-raheem

***************************************
Dariya farouk ya sheke dashi tare da cewa "that's good, stubborn girl a cikin Colbert ".  Shiko Al'ameen harara ya watsa mata tare da shigewa motarsa ya bar wajen.

Ihun da miemah ta kwala ne ya jawo hankalin yawancin mutane xuwa wajen.

Dariya farouk yake sosai, sae da yayi mai isarsa sannan ya mika mata hannu yace "xo badan halinki ba amma kar ki 6ata min jiki da kwata pah!  Hannu ta mika masa ya kamo hannunta ta fito gaba daya jikinta ya 6aci. Gsky yau MIEMAH tasha kunya sosai wanda bata ta6a shan irinsa ba, ga mutane nan sae dariya suke mata shima farouk sae kunshe nashi dariyar yake.

***wannan shine laifin da AL'AMEEN yayi wa MIEMAH wanda har take cewa baxata ta6a barinshi ba sae ta Rama**** 🤔ko wane irin mataki MIEMAH xata dauka🤔.

Haka nan take tafiya simi-simi har suka karasa gida, taci sa'a compound din bb kowa, kowani ma'akaici ya gama aikinshi ya tafi me gadi ma ya shige dakinsa.

A haka ta shiga main parlor. Da maryam taci Karo, cike da tashin hankali maryam ta taso tana fadin *sis me ya faru?  

Farouk ne yayi dariya tare da cewa ''je ki kaita ta wanke jikinta first tukun sae kixo in baki labari.

Hakan akayi maryam ta kaita bathroom ta hada mata ruwan wanka sannan ta fito, MIEMAH dae yau bb bakin magana gaba daya sai sussunkuyar da kai take.

Maryam falo ta koma wajen farouk dan jin abinda ya samu miemah.

Xaune ta sameshi ya daura kafa daya kan daya yana cin abinci cike da nishadi. Yah farouk me ya samu MIEMAH?

Dariya ya sake yi sannan ya bata labarin abinda ya faru. Nan itama ta fara dariya dan ta gane Al'ameen ne ya jefa miemah a Colbert.

Labarin fadan Al'ameen da miemah ta bawa farouk, shima dariya ya fara tare da cewa "that's good, wannan shine daedae da ita ai". Fitowa tayi cikin shirin doguwar Riga na atamfa da yar mayafinta hannunta janye da trolley dinta. Ajiye trolley din tayi sannan ta hau stairs din da xae kaita side din Ammi. Sallama tayi wa Ammi akan xasu koma kano. "MIEMAH ya naga kamar wani abu yana damunki?" Tayi tambayar with full of concern. In akwai abinda yake damunki ki fadamin mn.  Dan murmushi kadan MIEMAH tayi tare da cewa "Ammi bb komai pah". To Allah ya kiyaye hanya. Dama ta gama sallamarsu tun jiya. Kamo hannunta tayi suka fito main falo inda suka samu maryam ma ta jawo trolley dinta farouk kuwa yana gefe yana ta chat.

Ko takanshi basu bi ba suka ja trolley dinsu suka wuce xuwa parking lot. Ammi sae ja musu kunne take akan kar suyi tukin hauka tare da yi musu fatan sauka lpy.

Haka nan suka tafi, yau maryam ce ke driving. Tafiya suke tamkar kurame, sam basu saba tafiya irin haka ba dan in suna tafiya sukan saka kida suna tafiya suna miming  suna rawa suna ihu suna dariya amma yau dae tsitt kk jinsu.

Maryam ce tayi breaking silence din ta hanyar cewa "sis kiyi hakuri da abinda Al'ameen yayi miki, ki mance dashi dan Allah don't let that small thing change your mood, kinji dear, sorry pls".   Hawaye ne ya fara tsiyaya daga idon Miemah, da sauri maryam ta gangara gefen titi tare da yin parking tana cewa "haba sis, kuka kuma?? Abinda na dade ban gani a fuskarki ba sae akan Al'ameen xakiyi kuka". Tana maganar ne tare da share mata hawayen. Kuka mai karfi ne ya kufcewa miemah tare da kifa kanta kan cinyar MARYAM tana kuka cike da shessheka tace " na tsane shi! Na tsane shi!! Na tsane shi MARYAM!!!! Ya toxarta ni a idon al'ummah, ya jefa ni cikin kwata a gaban bainar jama'a, banyi tunanin xan hadu dashi ba, wlh da ban fito ba!!!    Kuma baici bulus ba sae na dau mataki akanshi. Itama maryam kukan takeyi tare da rungume miemah tace "kiyi hakuri besty, ki fita harkarsa kkinji" dakyar maryam ta lallashi miemah  har tayi  shiru sannan suka cigaba da tafiya. Sae kusan magrib sannan suka isa kano.

MIEMAHWhere stories live. Discover now