👉🏽MIEMAH 👈🏽 page 25
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
🍃🍃🍃🍃🍃🍃
🌾🌾🌾🌾
🌺🌺🌺Typing 📲
Story and written ✍ by
Khadija yusuf abba
Follow me on wattpad @khadija yusufbaba 🤟🏽🤟🏽🤟🏽Bismillahir-rahmir-raheem
***************************************
Ihu suka kwala ganin halin da MIEMAH ke ciki ga kuma sun ga lokacin da aka tafi da afrah. Da gudu su Aisha suka fara bin motar suna cewa a dawo da afrah.Ita kuwa maryam kan Miemah ta nufa da gudu tana jijjigata amma babu alamun numfashi ko kadan, ihu ta kwala tana cewa "wlh sun kasheta, sun kasheta itama kamar yanda suka kashe uncle farhaan". Ta karashe maganar tana kuka mai ban tausayi.
Shaheed ne ya karaso tare da daukan MIEMAH suka koma cikin asibitin da ita. Duk bin bayanshi suka yi. Maryam daga waya tayi ta kira yah Abdul.
"Yah Abdul sun kasheta, shikenan sun kasheta itama kamar yanda suka kashe uncle farhaan............... What?! Maryam me kike fada ne haka? Wa suka kashe? A rikice yake maganar. Itama maryam cikin rikicewa tace "MIEMAH, MIEMAH, MIEMAH suka kashe yah Abdul kuma sun tafi da Afrah.
Innalillahi wa inna ilaehi raaji'uun, shine kalmar da yake furtawa. Duk karfin xuciya irin na yah Abdul durkushe wa yayi a wajen yana kuka, shknn itama sun kasheta kenan. Yah hakeem ne yayi saurin karasowa "Abdul wai meke faruwa ne? Sun ci nasara akan mu a karo na biyu, sun kashe MIEMAH, sun dauke AFRAH. What?! Me kake fada Abdul.
Daedae lokacin aka fara announcing time din jirgi yayi. Dama a airport suke xasu tafi London. Nan kuwa suka shiga jirgi ya daga xuwa London har yanxu hawaye bai daina tsiyaya daga idon yah Abdul ba. Shi ya zaiyi da rayuwar shi in ya rasa Miemah? Tabbas shima zai iya mutuwar.
Can kuwa asibity Likitoci sun dukufa akan MIEMAH wajen ganin sun ceto ranta. Kusan five hours sannan suka samu ta dawo hayyacinta, amma duk da haka tana da bukatar jini. Daedae lokacin su yah Abdul suka iso.
Al'ameen shima tuni ya mike jin halin da MIEMAH take ciki amma kallo daya xaka mishi ka gane yana jin jiki. Da aka nemi jini cewa yayi a deba a jikinshi, amma bashi da lpy sosai shima kanshi yana bukatar Karin jinin hakan yasa aka gwadi na yah Abdul aka saka mata.
After 5hrs, a hankali take bude idonta har ta sauke su tarrr akan yah Abdul murmushi tayi tare da juyawa taga maryam tace ''Miemie kinga ko? Ai dama na fada miki matar nan muguwa ce axxaluma, kinga abinda tayi min ko? Juyawa tayi taga yah Abdul tare da cewa "yah sadeeq nikam ka tafi US dani dan in na xauna anan xata kashe ni aunty kareema da madam iyabo mugaye ne axxalumai.
Gaba daya babu mai fahimtar abinda take fada dan a tunanin su dukan da aka yi mata akanta ne ya Shafi kwalwarta. Dr. Ne yaxo yayi mata allurar bacci nan kuwa bacci ya kwashe ta.
Juyowa yayi ya kallesu tare da cewa "ya kamata ku kula sosai kar a sake mata duka akai irin haka, dan in irin haka ya sake faruwa xata iya loosing memory dinta. (Loosing memory ga miemah na nufin xata manta da rayuwarta dasu yah Abdul ne, xata tuna ainhin rayuwarta). Da haka dae doc din ya fita ya barsu suna ta jimamin yanda xasu nemo boss.
Yah Abdul maganganun MIEMAH kawae yake ta wassafawa. "Yah sadeeq, Miemie, aunty kareema, madam iyabo". Tabbas duk yanda akayi wadannan mutanen suna da alaka da rayuwarta na baya.
Normal ta farka sae dan abinda ba'a rasa wa. Radadin dauke afrah da sukayi shi yafi komai yi mata ciwo, hakkin afrah kadae ya ishesu, sun kashe mata iyaye, itan ma baxasu barta ba. Ihu ta kwala tare da cewa "yah Abdul kar ka raga musu, kar ka raga musu ko kadan, sun tafi da Afrah pah me xasu yi mata, karsu cutar da ita!
YOU ARE READING
MIEMAH
Historical FictionLabarin wata yarinya ce yar gidan shugaban kasa da take da tsiwa tun tana karama, hakan ne ya jawo mata yawan maqiya masu son ganin bayanta, Wanda har sukayi nasarar batar da ita daga Cikin ahalinta, ta fada wani ahalin na daban, ku biyo ni dan jin...