👉🏽MIEMAH 👈🏽 page 24
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
🍃🍃🍃🍃🍃🍃
🌾🌾🌾🌾
🌺🌺🌺Typing 📲
Story and written ✍ by
Khadija yusuf abba
Follow me on wattpad @khadija yusufbaba 🤟🏽🤟🏽🤟🏽Bismillahir-rahmir-raheem
***************************************
Wata dariya boss ta kece dashi tare da cewa, ban hoton shegun in gani.Murmushi yayi tare da dauko hoton Al'ameen ya nuna mata, kar6a tayi tare da kura masa ido, tabbas wannan hoton Al'ameen ne, saboda tana iya hango tsantsar kaman sarki isma'il da aunty afrah a fuskar shi.
Idonta ne ya kada yayi jaxir ganinshi cikin kakin sojoji, shknn dae burin afrah ya cika, daya hoton ta duba still duka na Al'ameen din ne, hoton an daukeshi ne lokacin da sukayi passing out yana rungume jikin uncle farhaan suna murmushi cike da farin ciki, ganinshi da tayi a haka ya tabbatar mata da cewa yana rayuwa ne cikin farin ciki bashi da matsalar komai a rayuwa.
Wato dae ita kawae aka bari cikin tashin hankali, ta rasa kwanciyar hankalinta dare rana bata da hutu kullum tunaninta yanda xata ga bayansu amma su ko kadan bata gabansu rayuwarsu ma suke cike da farin ciki. Tabbas dole ne sae taga bayansu baxata ta6a saurara musu ba.
Mikomin hoton shegiyar (MIEMAH) mika mata yayi. Pic din a club aka daukeshi, lokacin sun gama gasar rawa kenan kuma ita taci gasar, tana nan cikin shigar kananan kaya tana ta xuba murmushi.
Wato dae ita ma shegiyar cikin farin ciki take, babu kunci ko kadan a tattare da ita. Lalle kuwa miemah xata kar6i babbar hukunci a gareta duk lokacin da suka gamu.
Sabi'u Mikomin hoton babban shegen, (yah Abdul). Mika mata yayi, a raxane ta mike tana nuna pic din da hannunta, wanke sabi'u tayi da mari tana cewa "amma ban ta6a sanin kai dabba bane sae yau, wawa jaki kawae, sam baka san aikinka ba, wannan sadeeq dan kishiyata ne ba Abdul ba (kar ku manta yah Abdul da yah sadeeq suna mugun kama), common mutum daya ya gagare ku samu, ya tsaya yana muku wasa da hankali, har kun fara kawo hoton sadeeq a memakonshi". Boss ki saurare ni mana na samo duk wani bayani pah da ake bukata akan Abdul, kuma wannan shine Abdul sannan kuma shine DSP A.I da muka kasa........... Sake wankeshi da mari tayi tana cewa "me yasa dabbancinka baya fada maka gaskiya, kana tunanin xan yadda da duk wani bayani da xaka ban akan Abdul ne tunda hotonshi ma ya gagare ku samu, ta yaya kake tunanin xan yadda DSP A.I shine Abdul? Abdul likita ne babu abinda ya hadashi da aikin fikira, Abdul yana da wayo he's a smart guy tamkar yanda farhaan ya fada muku, ya nuna muku akan shine DSP A.I ne dan ku dena bincike akan shi ku koma bincike akan DSP A.I. can't u see yanxu ma cewa yayi ba shine matsalar mu ba Al'ameen ne matsalar mu saboda ya rena mana wayo? Al'ameen is a softhearted man, abu kadan yana iya broken dinshi, na rantse da Allah da badan Abdul ya tsaya ya karfafa mishi girki gwuiwa akan rashin farhaan ba na tabbata da yanxu wata maganar ake ba wannan ba.
Shidae sabi'u har yanxu rike yake da kuncinsa inda ta mareshi, xagin da ta mishi yayi mugun hasala shi dan ya bakanta mishi xuciya sosai, "dabba, wawa, jaki". Tabbas xata ga aikin dabbobi "wlh wlh sae na nemo duk inda abdul yake mun Jone mun tona mata asiri, xata san ni ta mara. Muryar ta yaji tana cewa "ku gaggauta nemo min Abdul duk inda yake, da DSP A.I.
An gama boss! Da haka ta saka nikab din ta ta fice su madam iyabo suka take mata baya.
Madam iyabo kiyi wa Juliet magana ta sama mana ticket xuwa London. Ok boss.
LONDON
Ku shirya mu tafi muyo shopping din komawa gida. Miemah tace "ni wlh yau bana son fita ku shirya kawae ku tafi ni xanyi gadin gida, ok suka ce tare da shiryawa suka tafi yin shopping.
YOU ARE READING
MIEMAH
Historical FictionLabarin wata yarinya ce yar gidan shugaban kasa da take da tsiwa tun tana karama, hakan ne ya jawo mata yawan maqiya masu son ganin bayanta, Wanda har sukayi nasarar batar da ita daga Cikin ahalinta, ta fada wani ahalin na daban, ku biyo ni dan jin...