👉🏽MIEMAH 👈🏽
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
🍃🍃🍃🍃🍃🍃
🌾🌾🌾🌾
🌺🌺🌺
Page 2
Typing 📲
Story and written ✍ by
Khadija yusuf abbaFollow me on wattpad @khadija yusufbaba 🤟🏽🤟🏽🤟🏽
Bismillahir-rahmir-raheem
***************************************
Cike da farin ciki aunty kareema ta fito da abincin a hannunta, tana murna a xuciyarta tana cewa har miemie ma gwara ta mutu kowa ya huta, in ta kashe twins kuma next target din ta yah sadeeq ne, in shima ta salwantar dashi shknn burinta ya gama cika tasan bakin cikin haka xai iya kashe ummie, to shknn ta huta ta xamo ita kadae ce a gidan sae yanda taso.
Tun kafin ta karaso miemah taje ta tare ta ta karbi abincin daga hannunta taxo ta ajiye a dining, cike da xumudi miemie tace "laah sis ashe gaskiyarki da kk ce baxaki ci fried rice ba, nima wlh dankalin ya burgeni kawo mana muci da wuri". Miemah ma cike da murmushi tace "to ukty, nima na qagu inci abincin nan". Abbie dae tuni ya bar wajen ma, aunty kareema ce take xaune tana ta xuba murmushin mugunta. Ta taso ta iso wajensu ta basu peck a chick sannan ta fara serving dinsu, miemie dae murmushi tayi miemah kuwa tsaki tayi tare da goge inda aunty kareema ta sumbace ta. Ko ta kanta aunty kareema bata bi ba taci gaba da serving dinsu saboda tasan tabbas in taci abincin nan, to saedae wata badae ita ba. Tana gama serving dinsu miemie ta dauki spoon ta debi abincin takai bakinta, da sauri miemah ta buge hannunta abincin ya xube tare da cewa "ukty tashi mu tafi an fasa cin abincin nata, muje muci abincin ummie mu". Cike da bacin rae miemie ma ta fara magana saboda yau 'yar uwar tata ta kure ta "wae ke sis meke damunki ne, to baxa aci abincin ummie ba ni wannan nake son ci". "Wlh miemie baxa kici abincin nan ba" cewar miemah "wlh sae naci" cewar miemie. Aunty kareema ce tayi saurin cewa (ganin miemah tana kokarin rusa mata budget dinta) "ke miemah ki barta taci mana tunda tace tana son ci" wata uwar harara miemah ta watsa mata tare da cewa "ke kuma wa ya sako ki cikin maganar nan🙄, ni kinga aunty kareema bana son shisshigi fa😒". Ta karashe maganar tare da murguda baki. Cikin hasala aunty kareema ta fara magana "wae ke wace kalar yarinya mara kunya ce........ " kafin ta karasa maganar ta taji sauqan miyan sauce din da tayi musu gaba daya a jikinta, cike da mamaki da takaici da bakin ciki ta dago kanta tana kallon miemah da ta tsaya ta riqe kugunta da hannu daya, daya hannun kuma riqe da flask din miyar da ta watsa wa aunty kareema, kafin tace komai miemah ta fara magana cike da huci "ina dae ni kika kira da mara kunya, shiyasa na nuna miki halin marasa kunyan, nan gaba wannan dirty mouth din naki ya qara fada min bakar magana sae na yanke sa😏". Ita fa miemie mamakin yar uwar tata takeyi da shegen tsiwa, ita dae tana tsaye ne tamkar mutum-mutumi coz she's totally speechless. Itama aunty kareema haka take kallon miemah with full of surprise, yanxu kam yarinyar nan ta fara bata tsoro, kuma tabbas lamarinta da aljanu, in ba haka ba yarinya yar qarama da shegen rasar kunya haka, tsawan da miemah ta dakawa miemie ne ya dawo da ita hayyacinta"ke miemah dallah xo mu tafi" ta fada tare da jan hannunta suka fice suka bar part din. Aunty kareema tamkar tayi ihu dan bakin ciki hanyar bedroom din abbie ta nufa ba tare da ta gyara jikinta ba saboda so take ta nuna masa rashin da'ar da miemah tayi mata, tana shiga dakin ta samu baya ciki, karar ruwan da taji a bathroom ne ya tabbatar mata da cewa wanka yakeyi, don haka ta xauna a kan sofa tana jiran fitowarsa, xamanta bai wuci da 5mins ba taji wayar sa dake kan bedside drawer tana ringing, tashi tayi taje ta duba ta ga number ne bb suna, kamar baxata dauka ba dae har ya yanke aka sake kira a karo na hudu sannan ta dauka tasa a kunnenta, ta daya bangaren akayi sallama cike da ladabi, bayan sun gaisa ne ake cewa "dama daga makarantar su miemah ne, daxu tasa bawon ayaba a malamar su ta fadi, to a halin da ake ciki dae yanxu muna asibiti kuma malamar taji ciwo sosae a kugunta har sae anyi mata aiki mah. Dan jimm kadan aunty kareema tayi, can ta sauke numfashi tare da cewa "kuyi hakuri bb komai ina xuwa yanxu insha allah i will handle everything " da haka sukayi sallama, ta sauke wayan daga kunnenta tare sake murmushin mugunta kana tace "miemahhhh sunanki matacciya" sannan tayi saurin ficewa daga bedroom din abbie, ta shiga wani spare room dake cikin part din, direct bathroom ta nufa tayi wanka, ta burma katon hijab akan towel din dake jikinta sannan ta fice daga part din abbie, tana fita daga part din driver da body guard dinta suna jiranta, nan suka bude mata motar ta ta shiga sukayi driving dinta xuwa part dinta.
Bayan ta shirya cikin kaya na alfarma asibiti ta nufa body guards dinta suna take mata baya, cike da izza take tafiya kowa sae gaisheta yake ana girmama ta kasancewarta matar president ita kuwa sae shan kamshi take. Direct dakin da aka kwantar da madam iyabo suka nupah.Da sallama suka shiga, nurse din ce ta amsa saboda dakin cike yake da yan uwan madam iyabo Christians, nan aka fara gaisheta cike da girmamawa, ita kuma tana amsawa cike da izza, bayan tayi musu gaisuwar ya me jiki ne ta nemi a bata waje dan tana son yin magana da madam iyabo, hakan kuwa akayi duk suka fice suka barsu, cike da kulawa ta sake tambayar madam iyabo "ya jikin dae madam", kwafa madam iyabo tayi tare da saka abubuwa da yawa a ranta akan miemah, alkawari tayi sae ta dau tsattsauran mataki akan miemah koda hakan xe xama silar rasa ranta ne, dama ita tun asali ta tsani twins din musammman ma miemahhhh "da sauqi"shine amsar da ta bawa aunty kareema. Dan murmushi aunty kareema tayi tare da cewa "madam iyabo, yanxu in aka baki dama kiyiwa miemah hukunci akan abinda tayi miki, shin wane irin mataki xaki dauka". Ai kuwa nan xuciya ta ciyo madam iyabo ta fara fade-fade ba tare da tasan tana yi ba "is better for u to stop them going that schl, don duk lokacin da na ganta sae na kasheta, i swear by the beautiful names of jesus , i swear by the jehovah , i wont let her go she must pay for what she have done! Dariya sosae aunty kareema take, hakanne ya dawo da madam iyabo cikin hankalinta, ta tuna da irin fade-faden da tayi, nan kuwa ta hau kame-kame "oh i didn't mean what i just said, uhm uhm, i mean miemah is like my daughter i cant take any revenge, believe me, i didn't mean mean my word🙏" ta karashe maganar cike da tsoro, murmushi aunty kareema tayi tare da dafa kafadar tace "kar ki damu madam ra'ayin mu iri daya, nima neman hanyar da xan salwantar da miemah nake, daxu na dana mata tarko, amma dake yarinyar shu'umah ce sae da tsallake, yanxu so nake na dana mata tarkon da ko ubanta bai isa ya tsallakar da ita ba". Murmushi madam iyabo tayi tare da cewa "father (bokansu na Christians) xae iya yi mana aikin da xa'a shafe labarin miemah daga duniya ba tare da an sake tuna ta ba har abada xa'a shafe labarin ta daga duniya tamkar ba'a ta6a halitta irin nata ba" ta karashe maganar cike da murmushin nasara. Itama aunty kareema murmushi tayi tare da cewa "xamu fara xuwa wajen boka murtu, aikinsa tamkar yankar wuka take" "to yanxu kamar yaushe xamu je" cewar madam iyabo "yau monday, so ran satuday xamu je mu, kinga xuwa lokacin kema jikin ki yayi sauqi sosai" da haka sukayi sallama aunty kareema ta fito ta wuce gida cike da farin ciki
WACECE MIEMAH??
Me yasa take da makiya
Me yasa ake son salwantar da rayuwarta
Me yasa manyancenta yafi karfin shekarunta
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
Mu hadu a page 3 don jin amsoshin tambayoyin nanLike, comment and share pls 🙏 follow and vote me on wattpad
Allah ya karbi ibadun mu🙏
YOU ARE READING
MIEMAH
Historical FictionLabarin wata yarinya ce yar gidan shugaban kasa da take da tsiwa tun tana karama, hakan ne ya jawo mata yawan maqiya masu son ganin bayanta, Wanda har sukayi nasarar batar da ita daga Cikin ahalinta, ta fada wani ahalin na daban, ku biyo ni dan jin...