Miemah page 36
By khadija yusuf abba.
🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
Da sallamarta ta shigo falon, direct Wajen mom afra ta nufa tare da dalewa cinyarta.
Kallonta kawai alameen da farouk suke, tabbas wannan miemah ce, "yah Abdul, ina Yale?
Nuna mata alameen yayi yana murmushi, da sauri ta tashi ta karasa wajenshi tare da mila mishi hannu tana murmushi, shima mika mata yayi suka gaisa.
Sake nuna mata farouk yayi tare da cewa "wannan shine abokin fadan ta". Kallonshi tayi tare da hararar shi tace "ya fiye shiga shirgin da bai sashi ba"
Shima farouk a hasale yace "kema kin fiye shisshigi da tsiwa". Xaro ido tayi tare da cewa "ni kuma me ya sako ni Cikin fadar ku". Omg sai yanxu ya tuna ashe miemahr bata Cikin tunanin ta basarwa kawai yayi.
Yah Abdul to ina matar tashi? "Ta haihu ta haifi 'yan biyu amma ta mutu a Wajen haihuwar"
Nan take Yanayin miemah ya sauya tace "ayya Allah sarki Allah ya jikanta, duk da ameen suka amsa.
Ashnaah ce tayi sallamah ta shigo hannunta rike da afrah.
Dago kai miemah tayi tare da kallon afrah dake hannun hannun ashnaah "wow ASH-FEEQ daga ina kika samo wannan cute girl din?
Da gudu ta tafi Dan kar6o afrah, nan kuwa santsin tiles ya jata ta fadi kasa timm kanta ya gwaru. Wani ihu tayi tare da somewa a Wajen
Da gudu suka isa inda take, gaba daya Kowa a gigice yake, yah Abdul ne ya daga ta tare da daura ta kan kujera ya dauko ruwa ya yayyafa mata, afrah kuwa tana ganin miemah ta gane ta, kuka take sosai wai Kar momynta ta sake mutuwa.
Sauke ajiyar zuciya miemah tayi, a hankali ta fara bude idonta ta sauke su akan mutanen da ke Wajen sae jera mata sannu suke.
A raxane ta fara duba gefenta tana cewa "ina 'ya'yana? Twins Dina a ina suke?
Hamdala yah Abdul yayi tare da dafa kanta yace ''calm down miemah! Kinji ko?
Yah Abdul? Ina besty? Afrah ina didi yam take?
Da gudu afrah taxo ta rungume ta tace "mommy didi yam tana London". Xaro ido miemah tayi tana cewa "London kuma?
Da sauri yah Abdul ya dafa kanta tare da fara topa mata addu'a, nan kuwa bacci yayi gaba da ita.
Duk hamdala sukayi cike da murna, finally miemah ta dawo hayyacinta.
Afrah kam kwantawa tayi a kirjinta Wae bata so tayi nesa da ita, mom afrah ce ta jawo afrah tare da rungume ta tana hawaye, bata san da me xata saka wa farhaan ba, tabbas xata kula da afrah har karshen rayuwarta, xata bata gata da kula fiye da yanda iyayenta xasu bata, Allah ya jikan farhaan.
Itama ko afrah lokaci guda ta saba da mom afrah.
Miemah Cikin bacci ta tuna da rayuwarta gaba daya tamkar mafarki.
Farkawa tayi bakinta dauke da addu'a, kallonsu take da daddaya da daddaya Kafin tayi murmurshi ta mike tare da karasawa Wajen yah Abdul Cikin sauri ta rungume shi tare da fashewa da kuka.
Magana take son yi amma ta kasa, yah Abdul kawai take ta furtawa. Murmurshi yayi tare da raba ta daga jikinshi yana share mata hawaye yace "u don't have to say anything, kinji? Kiyi shiru kawae"
Murmurshi tayi tare da hada hannayenta biyu alamar godiya🙏.
Juyawa tayi ta karasa Wajen alameen, murmurshi kawai take aika mishi, shima murmurshin yake mata, da gudu ta karasa ta rungume shi, Kowa dake falon murmurshi yake.
YOU ARE READING
MIEMAH
Historical FictionLabarin wata yarinya ce yar gidan shugaban kasa da take da tsiwa tun tana karama, hakan ne ya jawo mata yawan maqiya masu son ganin bayanta, Wanda har sukayi nasarar batar da ita daga Cikin ahalinta, ta fada wani ahalin na daban, ku biyo ni dan jin...