👉🏽MIEMAH 👈🏽 page 32
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
🍃🍃🍃🍃🍃🍃
🌾🌾🌾🌾
🌺🌺🌺Typing 📲
Story and written ✍ by
Khadija yusuf abba
Follow me on wattpad @khadija yusufbaba 🤟🏽🤟🏽🤟🏽Bismillahir-rahmir-raheem
***************************************
KANO TA DABO
Kowa ganshi cikin alhini da jimamin babbar rashin da aka tafka musu yake.Maryam kullum cikin kuka take, ta rungume Yaran duka uku ita take kula da su.
Al'ameen kam har yanxu yana gadon asibity bai san inda kanshi yake ba, shi kuma yah Abdul ya farfado amma baya iya cewa komai saedae kawai yayi ta kallon mutane da ido.
Ranar suna kawai rada wa Yaran suna akayi ba tare da anyi wani biki ba.
Yaran Miema biyu mace da namiji, macen an sa mata suna FATIMA mai sunan mom ana kiranta da AFNAN. shi kuma namijin mai sunan yah Abdul ne ana kiranshi da RA'OUF.
Yar maryam guda daya da suka bar mata kuma sunan ammi aka saka mata ana kiranta da AFREEN. Haka maryam take kula da Yaran nan cikin so da kauna.
ASIBITY
Da gudu Miemie ta nufi dakin da Miema take, fitowarta kenan daga toilet taga Miemie. Da gudu ta karasa ta rungume ta idonsu yana tsiyayar da hawaye. "Ukhty shine kuka tafi kuka barni a asibity ni kadai ko?Am sorry habibty naje ni yin wanka ne, daedae lokacin yah sadeeq ya shigo da gudu ta tafi ta rungume shi tana dariya atce "yah sadeeq mutan america, shine ka tafi ka barni ko?
Rungume ta shima yayi tare da shafa kanta yace "am sorry sis, Abbie ne yace kar in tafi dake". Ya fada yana nuna mata Abbie dake gefe, da sauri ta karasa wajen Abbie ta rungume shi, haka kawae itama taji hawaye na tsiyaya daga idon ta, suma duk hawaye suke.
I miss u Abbie. Sumbatar kumatunta yayi tare da cewa "miss u more habibty"
Xuwa Miemie tayi ta kama hannunta suka fice daga dakin su Abbie suka biyosu a baya. Dr fairouz mamaki ne ta kusan kashe shi ganin Miemie da Miema, dama miemie yan biyu ne bai sani ba?
Hada Ido sukayi da miemie ta dauke kai sama kamar bata ganshi ba, suna hada ido da miemah kuwa ta maka mishi harara, cikin sauri ya dauke kanshi. Shidae ya banu da wa'annan yara, sam ya kasa tantace wacece Mimi a cikinsu, Dan itama Mimin ta rikide ta koma miemah.
Mota suka shiga yah sadeeq ya jasu xuwa gida. Da gudu miemah ta shiga falon, da ummie ya fara cin karo, rungume ta tayi cike da farin Ciki , itama ummie matseta tayi a jikinta tamkar wacce xa'a sake kwace Mata ita idanunta suna fidda hawayen farin ciki...
Ummie nah i miss u. Miss you more darling. Ashnaah ce ta taho da murnarta tana cewa "welcome back abokiyar fada". Harararta miemah tayi tare fa cewa "ke ashfeeq, bana ciki da iyayin tsiya, wai welcome back sai kace wanda nayi wani tafiya mai nisan nan"
Harararta ashnaah tayi tare fa cewa "ke wlh ba'a abin kirki da ke ko kadan to ke dae kika sani ni babu ruwana"
Ashnaah da miemah tun asali basa xaman minti goma ba tare da sunyi fada ba.
Yah sadeeq ne yace "kukan iyayen tsiwa ya kamata kusan kun girma pah"
Miemie ce ta kama hannun miemah sannan ta kama na ashnaah ma suka wuce bedroom.
Wanka miemah tayi sosai sannan ta saka Riga da siket na lace purple, su din ma lace din suka saka, ai kuwa sun fito sun haska sosai tamkar taurarari. Fitowa sukayi suka nufi dinning area.
YOU ARE READING
MIEMAH
Historical FictionLabarin wata yarinya ce yar gidan shugaban kasa da take da tsiwa tun tana karama, hakan ne ya jawo mata yawan maqiya masu son ganin bayanta, Wanda har sukayi nasarar batar da ita daga Cikin ahalinta, ta fada wani ahalin na daban, ku biyo ni dan jin...