👉🏽MIEMAH 👈🏽 page 31
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
🍃🍃🍃🍃🍃🍃
🌾🌾🌾🌾
🌺🌺🌺Typing 📲
Story and written ✍ by
Khadija yusuf abba
Follow me on wattpad @khadija yusufbaba 🤟🏽🤟🏽🤟🏽Bismillahir-rahmir-raheem
Kun damen😖, kun sani typing da ban shirya ba, kar ku manta nasan pah me nake yi
***************************************
Boss
Ku gaggauta kuje ku ana binne ta ku tono tah dan bana son ko minti goma tayi a cikin kasa saboda ban shirya kasheta yanxu ba! Ita kuma doc deejah ku barta Abdul ya kashe ta dan nasan shine kadae xai iya ganowa rashin gaskiyarta. Ok Boss.1hr later
Ke tanii wai ke wace kalar bagidajiya ce, naji yanxu sae neman Miemah ake gashi har yanxu afrah bata iso Nigeria ba, that means na gefen haggu kika cire ba na gefen dama ba!Jikin tani na rawa tace "am sorry boss na gefen dama ne". Tsawa ta daka musu tare da cewa "ku kaini inje in gano da kaina" nan aka tura boss akan keken guragunta xuwa garden. Ai kuwa dae tani ta kwafsa na gefen hagu ta cire.
Ba tare da boss ta ko kalli inda tani take ba tace, ku dauke ta kuje ku tsareta a ma'adana dan baxata jawon asara in kyaleta ba. Ok Boss! Nan aka kama tanii tana kuka tana magiya aka wucw da ita ma'adana. Boss pah ta jima da raba gida da ummie, yanxu ba gida daya suke ba.
Salma ce tace "boss allurar mutuwa pah kika ce ayi wa miemah, to meyasa kika ce a tono ta, ko wani tsafin xaki yi da gawar ta?
Dariyar bosawa boss ta kece dashi tana cewa "ba allurar mutuwa bane, amma kusan allurar mutuwar yake, in aka yiwa mutum xaiyi awa ishirin da hudu tamkar matacce, baxaiyi motsi ba, baxaiyi numfashi ba sannan pulse dinshi xai dena aiki, hakan xaisa ayi tunanin ta mutu, nagode Allah da Abdul baixo da wuri ba har aka wuce da ita makabarta, na tabbata da Abdul ya ganta da xai gane bata mutu ba, suma kawai dan suna cikin rudewa ne shiyasa suke tunanin ta mutu, yanxu haka wadanda na tura sun isa, kuma yanxu ake shirin binne Miemah, masu binne ta suna juyawa ni kuma su audu xasu je su tono ta dan dama sun gama siye me gadin makabartan, 2hrs kawae ya rage Miemah ta farfado daga allurar da aka yi mata shiyasa nace ana binne ta su tono ta su kawo min ita dan ban shirya kashe ta yanxu ba!
Salmah yanxu kam boss ta fara bata tsoro, wannan wane irin rashin imani ne ta saka aka binne mutum mai rai. "Boss to meyasa kika 6oyewa doc Deejah gaskiyar lamarin?
Murmushi boss tayi tare da cewa "doc Deejah bata san ainihin harkalla ta ba, nuna mata nayi miemah ta kashe min mamana da babana, ita kuma na ta6a taimakonta shiyasa take ganin xata iya yimin kowane irin taimako in na nema a wajenta, shiyasa da na bata allurar tayi wa miemah ba tare da tunanin hadarin da xata iya shiga ta dalilin haka ba, na tabbata dama Abdul baxai barta ba muddin yaji labarin a hannunta miemah ta mutu.
Tsitt salmah tayi ba tare da ta sake cewa komai ba, dole ne ta nisanta kanta da boss, dan boss bata da amana ko kadan itama makircin boss xai iya fadawa kanta wani lokacim.
Dr. Hauwa ne ta karaso wajen hannunta rike da jariran sae kuka suke abin tausayi. Cike da bacin rai boss ta fara magana "me yasa xaki kawo min jariran Miema nan, kinsan na tsani Miema da duk wani abinda ya shafe ta, dan haka ki wuce da jariran nan wajen godiya yanxu ta gama da su! Ok Boss! Abinda Dr hauwa ta fada knn ta wuce da jariran.
Da gudu salmah ta bita tana cewa ''in kina kaunar Allah kar ki kai jariran nan ayi tsafi da su, ki duba girman Allah ki bani su wlh ina kaunar su ni xan rike su.
Wani kallon banxa doc hauwa tabi salmah da dashi tana cewa "dallah matsamin daga nan, kina tunanin akan wani banxar bukatarki xanyi loosing 2millions?
YOU ARE READING
MIEMAH
Historical FictionLabarin wata yarinya ce yar gidan shugaban kasa da take da tsiwa tun tana karama, hakan ne ya jawo mata yawan maqiya masu son ganin bayanta, Wanda har sukayi nasarar batar da ita daga Cikin ahalinta, ta fada wani ahalin na daban, ku biyo ni dan jin...