👉🏽MIEMAH 👈🏽 page 28
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
🍃🍃🍃🍃🍃🍃
🌾🌾🌾🌾
🌺🌺🌺Typing 📲
Story and written ✍ by
Khadija yusuf abba
Follow me on wattpad @khadija yusufbaba 🤟🏽🤟🏽🤟🏽Bismillahir-rahmir-raheem
***************************************
Hawaye ne ke tsiyaya daga idon yah Abdul, pulse dinta ya ta6a yaji yana motsi alamar bata mutu ba, ajiyar zuciya ya sake. Nan ya fara bata duk wani taimakon da xai bata dan shi har cikin ranshi yake yarda da wannan matar tana da alaka da MIEMAH. Allah yasa dai ta farka da wuri ta bashi labari game da boss.
Tabbas boss ta cika muguwa axxalumar mata, bai ma san wane irin hukunci xai mata in ya cafke ta ba, duk hukuncin da xai mata gani yake bai kai matsayin laifin ta ba..
Boss
Hello boka, kaji wa'annan lusarayen da na tura kashe afra sun kasa, basu kashe ta har suka hadu da abdul ya kashe wasu daga cikinsu, gashi yanxu haka sunce afrah tana tare dashi xata iya to amin asiri wlh, kuma kasan Abdul ba mutunci ne da shi ba.Karki damu kareema, afrah baxata ta6a iya tona miki asiri ba har sai ta dawo Nigeria, mun riga da mun rufe mata baki baxata iya tona miki asiri ba, kuma babu ita babu dawowa Nigeria har sai lokacin da kika tono abinda kika bunne a garden din nan kika kina shi sannan xata ji tana son dawowa Nigeria.
Dariya boss tayi tare da cewa har naji dadi wlh dan da nayi xaton afrah xata fadawa Abdul sirri nah. Daga haka sukayi sallama.
Riyadh
A hankali ta bude idonta tare da suke su akan yah Abdul. Murmushi tayi mishi shima ya mayar mata.Tashi tayi tare da kishingida tace "yaro ya sunanka? "ABDULRA'OUF". Ya bata amsar. Murmushi tayi tare da cewa "nice name, amma saedae kana min kama da dan kanwata". Murmushi kawae yah Abdul yayi ba tare da yace komai ba.
"Ko kasan sadeeq muhd zaid? Cike da murmushi yace "na sanshi amini nah ne ma sosai". Murmushi tayi tare da cewa "masha Allah"
Dan gyara xama yah Abdul yayi tare da cewa "yah sunan danki da ya bata, kuma a wane gari a Nigeria kika xauna?"
Murmushi mom afrah tayi tare da shafa kan yah Abdul tace "bana son in baka labarin komai game dani, bawai dan ban yarda dakai ba, saedae dan kawai bana son ko kadan in tuna abinda ya faru a baya, abinda ya wuce ya riga da ya wuce, amma kar ka damu tabbas xaka san wacece ni watarana, a jikinah nake ji mijinah da dana suna raye, insha Allah watarana xanga mijinah da dana cikin kwanciyar hankali, a jikinah nake ji xam sake rayuwa da mijinah! Ta karashe maganar cike da kuka mai ta6a xuciyar mai sauraro.
Lallashinta yah Abdul yake yana bata hakuri tare da karfafa mata guiwa har ya samu tayi shiru sannan yace. "Mom dan Allah xan miki wata tambaya amma dan Allah ki daure ki bank amsar ta in kin sani.
Murmushi tayi tare da cewa "insha Allah xan fada maka in na sani"
Pic din miemah ya dauko ya miko mata tare da cewa "kinsan wannan? Kar6a tayi tayi murmushi tace "sunanta Miemie, 'yar kanwata ce, amma yanxu haka a Australia take". Amma mom ba 'yan biyu aka haifesu ba?
Girgixa kai tayi tare da cewa "ita kadai aka haifeta"
Yah Abdul ya shiga damuwa, to meyasa ake samun me kama da Miema da yawa ne, gashi kamansu daya da maryam bayan babu wani relation da suka hada, gashi kuma matar nan ta kira ta da wani suna na daban kuma tace a Australia take, that means akwai wata me kama da Miema kenan wacce har Ba'a iya banbancesu, tabbas dole ne ya sake tsananta bincike wajen binciko ainihin iyayen miemah!
YOU ARE READING
MIEMAH
Historical FictionLabarin wata yarinya ce yar gidan shugaban kasa da take da tsiwa tun tana karama, hakan ne ya jawo mata yawan maqiya masu son ganin bayanta, Wanda har sukayi nasarar batar da ita daga Cikin ahalinta, ta fada wani ahalin na daban, ku biyo ni dan jin...