MIEMAH page 5

30 2 0
                                    

MIEMAH page 5

Typing 📲

Story and written ✍ by
Khadija yusuf abba

GIMBIYA fulani ta firgita sosae ganin afrah bata ko Numfashi, amma ganin yaron dake hannun nurse din ma sae yasa ta mance da halin da afran ke ciki ta kar6i yaron saboda tafi kaunarsa fiye da afran, tura gadon da take kwance akai akayi aka fice da ita daga ward din xuwa wani ward din domin ceto ranta. Hakan yasa kareema bata samu damar aiwatar da mugun nufinsu akan afrah da danta ba.
Masha Allah shine abinda GIMBIYA fulani ta furta ganin yaron kyakkyawa dashi sak jinsin larabawa (kasancewar asalinsu dama larabawa ne xama ne ya kaisu Australia) nan akayi wa yaro wanka. U tass aka shiryasa cikin kayan jarirai masu mugun kyau da tsada.
Likotoci sun taru akan afrah dakyar suka samu suka ceto rayuwarta amma duk da haka tana bukatar jini, a lokacin ne kuma sarki ismail ya iso cikin asibitin Wanda saukarshi a Nigeria knn, don haka bb 6ata lokaci aka gwada jininsa kuma iri daya ne da nata nan aka gwadi yanda ake bukata aka saka mata.

An sheda musu tana bukatar hutu yanxu baxa'a samu ganinta ba don haka suka wuce dakin da yaron yake, cike da farin ciki ya kar6i dannasa tare da tasbihin mika godiya ga Allah da ya axurta sa da samun 'da. Nan yayi masa huduba da MUHAMMAD AL'AMEEN.
5hrs later
Alhmdllh jikin aunty afrah yayi sauki sosae ta farka cike da kuxari, nan ta bukaci akawo mata yaron ta, aka kawo mata shi kuwa, karbansa tayi tana mai xubda hawaye tare da mika godiyarta ga Allah subhanahu wata'ala da ya axurta ta da yaron nan, wani irin kaunar yaron tare da kaunar mahaifinsa ne ke fuxgarta, bata tunanin xata iya rayuwa ba tare da daya daga cikinsu ba, daukar waya tayi ta bugawa ammah (aunty ni'imah) ta sanar da ita ai itama ta haihu "cike da farin ciki aunty ni'imah take tambayarta me ta Haifa tare da sanar mata suma yanxunnan saukarsu daga flight 🛩 suna Abuja sun samu amnah tana nakuda shine suka wuce da ita asibity. Itama aunty afrah murmushi tayi tare da cewa "ikon Allah, an aurar damu rana daya gashi muna ta haihuwa rana daya, Allah ya sauketa lpy " ameen ammah tace sannan sukayi sallama, ta kira amrah ta sanar da ita ta haihu tare da sanar mata amnah ma tana asibity tana nakuda, itama cike da murna tayi mata barka da haihuwa tare da yiwa yar uwar ta amnah fatan sauka lpy sannan sukayi sallama, nan kuwa doctor ya kawo musu katin sallama sannan suka dunguma xuwa babbar masarauta. Aka cigaba da kiraye-kirayen waya ana sheda musu karuwar da aka samu.

GIMBIYA AZRAH da kareema jin cewa aunty afrah ta haihu kuma namiji ta Haifa gaba daya hankalinsu ya tashi, gashi masarautar sae shagali ake cike da murnar karuwar da aka samu. Ba yanda suka iya haka nan suma suka shiga cikin mutane suna nuna murnarsu.

Amnah dae tana asibity har yanxu bata haihu ba tana ta shan wahala, don likotoci ma sun yanke shawarar in bata haihu ba xuwa nan da 5hrs kawae xa'a yi mata operation .
Amrah kuwa tana nan tare da jaririnta cikin koshin lpy yaronta ma kyakkyawa dashi mai kama da ita.

1 day later
Alhmdllh amnah ma ta haihu bayan dogon nakudan da tasha, ta haifi da namiji, xuwa nayi domin dubo muku yaron 😯 yaron kamansa daya sak da dan amrah, tabbas in aka hada su waje daya xa'a iya cewa twins ne, to ko dan iyayensu twins ne shiyasa suke kama haka🤔.

Allah wadaran naka ya lalace, dubi yanda ake ta rawan kafa akan yaron nan da afrah ta Haifa, amma dake ishak shi banxa ne ya kasa nutsuwa yayi auren ma bare ya haihu kawai ya tsaya biye wa matan layi" cewar GIMBIYA AZRAH cike da bakin ciki. Kareema ce tace "mama ko kin lura da abinda na lura dashi? " na me pah" cewar GIMBIYA AZRAH. Mikewa daga kishingiden da take kareema tayi sannan tace "GIMBIYA fulani ta fara son GIMBIYA afrah sosae tamkar yanda take son jaririn nan" cike da firgici GIMBIYA AZRAH take kallon 'yar tata "yanxu kareema Kennan shirinmu xae rushe pah muddin muka bar GIMBIYA fulani ta fara son GIMBIYA afrah ". Kar ki damu mamah, in dae har ni jinin ki ce na rantse miki da allah sae na ga bayan ahalinsu gaba daya, a duniya na tsani afrah da duk wani Wanda ya shafe ta, nayi miki alkawari sae na tarwatsa ahalinsu gaba daya, wannan jaririn ma sae na kashe sa, koda xai rayu to baxai ta6a rayuwa a cikin babbar masarauta ba, xan sa rayuwar sa cikin garari, na miki alkawari mamahh sae MULKIN BABBAR MASARAUTA ta dawo hannu na✊". Wani shu'umin murmushi GIMBIYA AZRAH tayi tare da dafa kafadar kareema tace "ina alfahari dake 'Yata, kina min abinda namiji ya kasa min, xan baki goyon baya Dari bisa Dari wajen gudanar da kudurinki, amma ki bari mu shiga jikinsu ayi komai da mu sae bayan suna xamu fara gudanar da kudurinmu" itama murmushi tayi tare da cewa hakan yayi mamahh. "To ya maganar aure kuma" " a'a ni mama ki barni ba yanxu ba, don har yanxu ban ga Wanda ya min ba". Murmushi kawae tayi ba tare da ta sake cewa komai ba.

MIEMAHWhere stories live. Discover now