👉🏽MIEMAH 👈🏽 page 13
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
🍃🍃🍃🍃🍃🍃
🌾🌾🌾🌾
🌺🌺🌺Typing 📲
Story and written ✍ by
Khadija yusuf abba
Follow me on wattpad @khadija yusufbaba 🤟🏽🤟🏽🤟🏽Bismillahir-rahmir-raheem
***************************************
Gaba daya ta wanke masa fuska da lemo, dariya yaji kasa-kasa ta bayansa, juya wa yayi cike da hasala, Husnah da maryam ya gani suna yi masa dariya ashe akan idonsu akayi komai.Takowa yayi xuwa garesu, Suma duk a tsorace suke ganin yanda ransa ya 6aci.maryam ya kalla tare da fara magana cikin kuncin abinda miemah ta masa. "Kije kice wa wannan kwailar 'yar uwar taki wlh ta tsoraci haduwarmu na gaba dan baxata ji da dadi ba, kullum sae ta watsa min lemo, rannan kuma ta 6ula min tayar mota, kice mata Kar ta bari mu sake haduwa duk inda ta ganni ta nemi hanyar guduwa Kar ta bari mu hadu". Nan dai yayi wa maryam warning masu xafi akan meemah, itama jikinta sae rawa yake dan a tsorace take se gyada masa kai kawae take, husnah kuwa tuni ta sulale ta shige gidansu. Umarni ya bata akan ta janye motar MIEMAH daga wajen. Nan kuwa ta janye ya samu ya wuce.
Tana shiga gidansu husnah ta samesu suna xaune suna ta dariya, harara ta bisu dashi gaba dayansu tare da cewa ""besty kin jawo rigima shine kk barni ko? Ke kuma friend har da guduwa ki barni a wajen in ma kasheni xaeyi ya kashe ni ko🙄". Husnah tace "keee ni rabani da wannan masifaffen mutumin, Kar kiga yanda 'yan cikina suke juyawa lokacin da yake magana sam baiyi kama da renon Nigeria ba amma akwai masifa". Dariya suka sake gaba dayansu miemah tace "ku kuke jin tsoronsa shiyasa yake Rena ku................ Maryam ce tayi saurin katse ta ta hanyar cewa "kul miemah, kinga yanda kika tsorata kuwa da kika ganshi🤔? Husna ce ta fara dariya tare da cewa "wlh kuwa musamman ma lokacin da ta ruga a guje ta shigo gida" aikuwa nan suka fara mata dariya. Haushi ne ya kamata ta fara magana "ai wlh in muka sake haduwa dashi sae na nuna masa true color Dina". "Aa MIEMAH ina rabaki, kinga irin warning din da yayi akan ki kuwa?. Nan ta fada mata warning din AL'AMEEN. To ni ina ruwa nah dashi, ki koma kice masa shima Kar ya sake mu sake haduwa dan haduwarmu baxae mishi kyau ba. . Cewar miemah. Maryam dafe kirjinta tayi tare da cewa "wa! Nidin? (Ta fada tare da nuna kanta) nidae in kin ganni a lahira kaini akayi, ta yaya xan fara tarar guy dinnan da maganar nan? Ni wlh kwarjini yake min, Sam Bana iya mayar masa da magana, gashi da shegen izza Kaman ya hada dangi da gidan sarauta. Kedae da kika ga xaki iya sae Kije amma badae ni ba kam."
Tsaki miemah tayi tare da cewa "matsoratan banxa kawae". Husnah ce tayi murmushi tare da cewa. "Amma fa guy din ya hadu wlh karshen ne". Tsaki miemah tayi tare da cewa "sae ki aure shi ae". Harararta husnah tayi tare da cewa. "Ina da sadeeq me zanyi dashi". Sadeeq din da kk cewa har yanxu bai kar6i soyayyar ki ba shine kike ta wahala a kanshi, ni wlh husnah kina bani mamaki, da kyanki da iliminki da dukiyarki amma ki tsaya namiji yana ja miki aji, tukun wae ma shidin dan gidan uban waye ne???? Maryam ma ce "nima gskiya ina son sanin waye wannan sadeeq din da kika nace masa?". Murmushi mai ciwo husnah tayi tare da gyara xamanta ta fara magana "duk yanda xan fada muku baxaku gane ba, yah sadeeq ya hadu fiye da yanda kuke tsammani, d'ane ga tsohon shugaban kasa *alh muhd zaid* su biyu iyayensa suka Haifa, shine babba sae kanwarsa miemie wacce take Australia amma bata ta6a xuwa Nigeria ba ma tun da ta tafi dan a wajen dangin ummie su take, ummie su kawar mommy na ne, tun lokacin da naje hutu gidan shima ya dawo daga US na ganshi tun daga lokacin naji ina kaunarsa amma shi Sam yace a matsayin kanwa ya dauke ni", ta karashe maganar idonta yana xubda hawaye". Ayya Allah sarki Allah ya juyo miki da hankalinshi kanki, miemah ya kamata ki bawa yayanki Satan amsa dan har yanxu ya kasa furta abinda ke ranshi😉. Dan dukan wasa miemah takai wa Maryam tare da cewa "yayanah me tsada ne barikiji, saedae ke ki furta abinda ke ranki. Dariya sukayi gaba dayansu kafin suka fara rehearsal din rawar.
After 5hrs
08:25pmSun gama shirinsu tsaf dan xuwa club, su BEIGONS ma sun karaso cikin mota guda biyu. Suma motarsu suka shige, husnah ce ke driving maryam a gefenta yayinda miemah ta hakimce a bayan mota tamkar wata sarauniya. Motar su ce a tsakiya yayinda motar su BEIGONS daya tana gabansu daya kuma tana bayansu.
Haka suka karasa club din suka shiga, nan kuwa suka samu kowa yana harkan gabansa, wasu suna shan beer 🍺, wasu suna busa hayaki, wasu suna rawa cike da maye wasu kuwa suna nan tare da samarinsu. Sam yau tsarin club din bai musu ba dan su kawae gasar rawa suke xuwa yi. Tsaki miemah tayi tare da cewa "kuxo mu tafi, Yau club din na ogan ninmu ne* haka kuwa suka fice daedae lokacin da AL'AMEEN ya Karaso wajen, yaxo wajen wani colleague dinsa ne kar6an wani documents. Miemah ce ta daga kanta, ai kuwa nan suka hada ido dashi daedae lokacin da yake fitowa daga mota. Gabanta ne ya fadi ganin yanda yake bin ta da kallon tsana! Murguda baki tayi tare da saurin shigewa mota. BEIGONS ta kira tare da basu umarni "waccan guy din nake so kubi kuyi masa dukan tsiya ta yanda baze iya Numfashi ba har sae an kwantar dashi a gadon asibity. ". An gama ranki ya dade. Abinda sukace knn husnah taja motar suna mata dariya ita da maryam.
Shiko AL'AMEEN mamaki yake tare da tsanar halin irin na MIEMAH, 'yar yarinya da ita da bata wuce 17yrs ba har ta iya xuwa club. Abokin nashi ne ya fito tare da mika mishi documents din, kar6a yayi ba tare da yace komai ba ya shige mota ya tafi.
Direct hanyar barrack dinsu ya nufa, yayi tafiya mai nisa kasancewar hanyar barrack din shiru ne ya kula da Ana biyoshi, hakan yasa shi tsayawa tare da fitowa daga motar Suma fitowa sukayi daga nasu motar. Gadan² sukayi kanshi tare da kwada masa wani karfen da yayi sanadiyyar fasa mishi goshin sa jini ya fara xuba.. Nan kuwa suka fara dambe a tsakaninsu, gaba dayansu sun jigata, amma Al'ameen yayi namijin kokari wajen kayar dasu dukansu, mutum daya yana can ta gefe ya 6uya yana video wanda umarnin miemah ce tace tana so ayi mata videon komai saboda tana so taga yanda xa'a yi kaca² da AL'AMEEN.
Bayan yayi nasarar yi musu duka gaba dayansu yadan ja gefe tare da jan Numfashi sosai, wae dama haka Nigeria take da shegen chakwakiya, tun da yaxo Nigeria bai huta ba, yace wa uncle farhaan ya dawo da wuri dan shi xaman Nigeria tana yi masa wuya sosai, to wae yanxu waye yake son ganin bayanshi da har ake turo masa yan daba. Wanda yake video ne ya kira MIEMAH ya sanar da ita abinda ke faruwa. Masifa ta fara tare da cewa "wae ku wasu irin ragwaye ne, ku goma amma mutum daya ya gagare ku, a wane waje kuke?". Address din ya fada mata, sannan ta ce "maryam, husnah kuxo muje bb lafiya wancan aljanin yayi wa guard din mu duka". Kema me yasa kika yi wannan gangancin, nidae ba inda zanje. Cewar husnah.
Kekam ai dama nasan matsoraciya ce, maryam tashi muje. Maryam tace "nidae zanje na kashe kwarkwatan ido na, dan banaso labari ya wuce ni. Dan siririn gyalensu suka dauka sannan suka fice, miemah taja motar da shegen gudu.
Alameen daga waya yayi dan kiran guard din sa su tafi da guards din su miemah, me daukan video ne yayi saurin fitowa daga inda ya 6uya ganin alameen yana kokarin tona musu asiri, wani katako ya dauka tare da make shi a kai, nan danan hajijiya ya fara dibansa ga jinin da yake ta xuba daga goshinsa yayi yawa. Baya yayi xai fadi luuuu daedae lokacin su miemah suka karaso, ko parking me kyau bata gama ba ta fito da gudu taje ta tare alameen suka fadi a tare kasancewar ya fita nauyi, kallonta kawae yake with non understandable expression, a hankali ya furta "lemon girl ashe hatsabibancin naki yakai har da ta'addanci? hararasa tayi tare da cewa "kaide kullum sae ka nuna halin, dan ma ka samu xan taimaka maka😏. Cigaba da kallonshi take kafin ta Dan rungumoshi kadan ganin numfashinsa yana shirin fita daga jikinsa, cikin sauri ta cire gyalen kanta ta daure masa goshinsa dake ta xubda jini.............. ✍
Kuyi manage, kar kuce banyi typing ba😏
Like, comment and share. Follow and vote 🗳 me on wattpad @khadija yusufbaba
Allah ya kar6i ibadunmu🙏
YOU ARE READING
MIEMAH
Historical FictionLabarin wata yarinya ce yar gidan shugaban kasa da take da tsiwa tun tana karama, hakan ne ya jawo mata yawan maqiya masu son ganin bayanta, Wanda har sukayi nasarar batar da ita daga Cikin ahalinta, ta fada wani ahalin na daban, ku biyo ni dan jin...