Part 37

7 1 0
                                    

Miemah 37

      Calm down miemah!  Ta yaya xaka  ce min calm down yah Abdul??  Besty nah fa take kokarin kashewa, wlh impossible sae naga bayanta.

    Ku rabu da Ita, karamar kwakwalwa ce da Ita, in ta san wata ae bata san wata ba, ku tsaya ku ga yanda wasar xata kaya.

    5dayz later, an tafo da babies din dukansu Nigeria, but an mayar da afrah coz xasu dawo tare da maryam.

    Miemah tamkar xata yi hauka Dan farin cikin ganin yaranta. Gasu sun girma sunyi wayo abinsu.

    Ra'ouf dae shegen miskilanci ne dashi,  Sam bai damu da kula mutane ba, baya sakewa da Kowa sae yah Abdul, Ita ko afnan sak halin miemah ce da Ita, afreen dae bata da damuwa ko kadan, but Ita kam tafi shakuwa da ashnaah.

   Yau maryam xata duro 9ja haka su boss ma, miemah cike take da farin ciki haka ya shirya babies din sosai sukayi kyau kamar a sace su, tana fitowa falo ta tarar da husnah tare da babynta. Ai kuwa nan suka rungume juna cike da farin ciki.  "Hunsnah inah ayshah pah?

    Oh ke baki sani ba🤔, Aysha saurayinta ya rasu Ana saura kwana3 bikinsu. Ayya amman na tausayawa aysha wlh, allah ya jikanshi. Ameen ta amsa daga nan suka cigaba da hirar su.

      Cike da farin ciki take saukowa daga matattakalar jirgin fuskarta dauke da murmushi hannunta daya rike da afrah sai surutu take mata.

    Wuwwurga idonta take ko xata hango Wanda yaxo tarar ta, ta can nesa  ta hango miemah, da gudu dukansu suke son karasowa fuskarsu cike da farin ciki mara misaltuwa, tsakaninsu bai wuci taku biyar ba kibiyar da aka  harbo dan ya kashe miemah akayi Rashin sa'a kuwa ya caki maryam ta fadi a wajen.

     Wani raxanannen ihu suka saki da gudu suka karaso kan maryam. Besty kitashi, ki tashi dan allah Kar ki mutu.

    Ihu afrah tayi tana cewa mom gasu can sune, sune, sune wlh suka kashe didi yam, mommy sun kasheta😭😭.  Ta karasa magnar da kuka mai ta6a xuciya.

    Ita dae maryam dan motsa hannunta kawae take tana murmushi tana fuzgar numfashi dakyar ta furta ''besty kije ki gama da su, Kar ki raga musu ko kadan, koda na mutu yanxu banyi bakin ciki ba saboda Nasan ban bar baya da kura ba, ki cewa yah hakeem nace ya auri ashn...... Daga nan ta fara tari  numfashinta yana sarkewa, miemie husnah kuxo ku kaita asibity.

   MIEMAH  ashnaah Abdul alameeen suka shiga mota a guje suka bi bayan su boss!

     Miemah kuka take sosai tana cewa "karshe, karshe, karshe wlh tlh wannan shine rai mafi hadari da suka hallaka kuma wlh shine na karshe.

     Su kuwa su boss dama basaja suka hada, sun san dama in suka kashe maryam dole xa'a biyosu, kuma sun shirya kaisu jeji dama a je a fafata a can. Haka sukayita jam su yah Abdul har suka shige wani kungurmin daji!

   Nan Kowa yayi parking ya fito, but sun 6oye boss.

     Nan kuwa aka fara fafatawa, barin wuta kawae take ta ko ina, kowane bangare cike da kwarewa suke fadarsu.

    Nasara tana ga su miemah saboda ga alamu nan sun nuna,  boss ganin Ana karar mata da mutanen ta yasa ta fito itama ta shiga.

    Kowane bangare sun jigata sosai, Kowa dake wajen akwai tabon harbi da yanka a jikinsa. Lallai su miemah sunyi kokari sosai ta wannan fanni musamman ma ashnaah dan ta mugun bani mamaki.

    Boss ganin fah fadar tafi karfinta yasa ta fara neman hanyar tserewa, alameeen ne ya lura da hakan, Cikin sauri ya harba mata bindiga a tsakar kanta, ihu tayi tare da faduwa, Cikin sauri suka karasa gareta tare da gewayeta da bindigogi.

MIEMAHWhere stories live. Discover now