👉🏽MIEMAH 👈🏽 page 7
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
🍃🍃🍃🍃🍃🍃
🌾🌾🌾🌾
🌺🌺🌺Typing 📲
Story and written ✍ by
Khadija yusuf abba
Follow me on wattpad @khadija yusufbaba 🤟🏽🤟🏽🤟🏽Bismillahir-rahmir-raheem
***************************************
MIEMAH ce kwance a bakin rafin nan, wani dattijon bafulatani ne hannunsa dauke da jarka yaxo diban ruwa, ganin yarinya kwance a bakin rafin ya sashi tsayawa tare da duba ta, amma dae bata yi Kala da 'ya'yan dake cikin rugar ba gata kyakkyawa da ita, nan fah tsoro ya kama sa, he start thinking kodae aljana ce 🤔, kasancewar sa nutsattsen dattijo yasa yayi jarumta ya dauke ta ya nufi gidansa da ita. Da sallama ya shiga tare da shimfideta a tabarmar dake tsakar gidan. Inna wuro, inna wuro sunan da yake ambata kenan, ta cikin dakin ta amsa da na'am ganinan fitowa. Turus ta tsaya ganinsa da yarinya "hardo daga ina ka samo wannan 'yar turawan kuma" labarin yanda yaga miemah ya bata, tare da cewa "kinga allah yayi wa miemo rasuwa, gashi allah ya sake bamu wata 'yar, yanxu ki dauke ta ki kaita daki, ki jika mata sassaken magarya ki bata tasha ko xata dawo hayyacinta". Amsawa tayi da "toh, wlh yarinyar kuwa ta shiga raena, da gani ma sa'ar miemo ce, Kaga wani abin mamakin kuma🤔 kamarta daya da maryamu yar matar imraana baturiyar nan, eh wlh kuwa kodae itace?? Aa wannan kam jinin turawa ce". Sannan ta dau miemah ta shige da ita cikin daki.
Abuja
Tsafi gaskiyar mai shi, tabbas asirin aunty kareema ya kama, cikin dare dae aljani burunbutu ya dauke miemah daga ahalinta yaje ya wullar da ita a rugar babban RAFI. Washe gari da safe, haka dae suka tashi gaba dayansu babu wani mai walwala da yawa, a jikinsu suke ji they missed a precious thing a rayuwarsu amma sun kasa tuna ko menene, hatta da 'yan aikin gidan sun mance da wata halitta miemah. Yah sadeeq ma dae haka yake, a haka ya shirya ya bar Nigeria xuwa US inda xae yi karatunsa saboda ji yake gaba daya 9ja tayi masa xafi. Miemie kam tafi kowa shiga damuwa, duk da karancin shekarunta takan xauna tayi ta tunani ko xata tuna abinda take missing. Ta saba da 'yar uwarta sosae lokaci guda taxo ta rasa ta ba tare da tayi noticing hakan ba, gaskiya abin da ciwo.Ta bangaren Abbie da Ummie ma pah abin babu sauki ko kadan, domin kullum cikin tunani suke, basu da rest of mind ko kadan, abbie kam ga stress din mulki, ga kuma tunanin dake cin xuciyarsa ta can kasa gaba daya dae abin bb dadi, ahalin suna cikin wani hali.
Aunty kareema kuwa duniya sabuwa, cin karenta take babu babbaka, damuwarta bai wuce yanda abbie yake cikin damuwa ba, saboda ita dae da gaske take sonsa har cikin ranta bata so ta ganshi cikin damuwa. Tunda sun gama da sarki ismail yanxu kam shikenan ae, so take ta shirya ta fi babbar masarauta domin amsar MULKIN.
BABBAR MASARAUTA
Tabbas anyi babbar rashi a cikin babbar masarauta, amma dae har yanxun basu da tabbacin cewa sarki ismail mutuwa yayi domin kuwa har yau Ba'a samu gawarsa ba, gashi sun rasa Al'ameen basu san inda ya shiga ba, damuwarsu dae ta taru ta xama da yawa kullum cikin bincike suke.
Suna cikin wannan hargitsin aunty kareema ta tsiro da maganar amsar MULKIN BABBAR MASARAUTA! Sarki ABDALLAH yayi mata tasss tare da cewa "kul, ko bayan raina ban yarda mace ta mulki babbar masarauta ba, macen ma mara tunani irin kareema ba (shifa har ransa baya jin kareema a matsayin 'ya), tunda dae Ba'a san inda ismail yake ba, ko yana raye ko baya raye allahu a'alamu, gashi Al'ameen ma an rasa sa, to daga yau na nada ABDULAZEEZ kanina a matsayin sarkin babbar masarauta har xuwa lokacin da AL'AMEEN xae bayyana a basa mulkinsa! Bana so in sake jin wata magana ta biyo baya, na gama magana". Haka ya kira masarautar Australia ya sanar dasu hukuncin da ya yanke kuma sunyi na'am da hakan
Aunty kareema tayi bakin ciki sosai da aka nada ABDULAZEEZ a matsayin sarkin babbar masarauta, haka taxo ta tasa GIMBIYA azrah a gaba tayi ta mata kuka tare da surutai, ita dae dole sae an bata mulkin. "Haba kareema, ya kike so nayi ne, kina dae ga halin da nake ciki, ga ishak nan shima hanyar da ya xa6a kenan, ya bar kasar ma gaba daya yabi mace kasarsu saboda lalacewa, da yana nan ai da shi xa'a nada, nidae kawae kiyi hakuri ki bari komai ya lafa sae mu nemo mafita, amma yanxu in na tari sarki ABDALLAH da maganar nan xae iya sa6a min nima". Dakyar dae ta lalla6a kareema ta hakura ta koma abuja.
YOU ARE READING
MIEMAH
Historical FictionLabarin wata yarinya ce yar gidan shugaban kasa da take da tsiwa tun tana karama, hakan ne ya jawo mata yawan maqiya masu son ganin bayanta, Wanda har sukayi nasarar batar da ita daga Cikin ahalinta, ta fada wani ahalin na daban, ku biyo ni dan jin...