Part 26

8 1 0
                                    

👉🏽MIEMAH 👈🏽 page 26
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
   🍃🍃🍃🍃🍃🍃
        🌾🌾🌾🌾
              🌺🌺🌺

Typing 📲
      Story and written ✍ by
Khadija yusuf abba
 
Follow me on wattpad @khadija yusufbaba 🤟🏽🤟🏽🤟🏽

Bismillahir-rahmir-raheem

***************************************
Afrah aka dauko aka kawo mata, kar6arta tayi  tare da kura mata ido.

      Murmushi tayi tare da cewa "kyakkyawa ce sosai, ta gado ubanta wajen kyau har naji ta shiga raina, ku barta baxa'a kasheta ba, in ta  girma xata mana amfani. A cikinku waye xai iya rike mana Ita???

     Sulaiman ne yayi saurin cewa "gani boss, xan kaita a matata, dama tana mugun son 'ya mace amma bata samu ba. "Ok ka kaita ta riketa a wajenta.

     Nan Sulaiman ya dauki afrah ya kaiwa matarshi xubaida (zuby da ta dauko Al'ameen daga babbar masarauta) tayi murna sosai kuwa ga afrah nan kyakkyawa mai saurin shiga rai.

KANO
     Kuka sosai MIEMAH take jin ba mom bace ta haifeta. Sai hakuri ake ta bata.  Shima Al'ameen mikewa yayi ya fice a falon ko side dinsu baije ba kawae parking space ya wuce ya shiga mota ya bar gidan not knowing inda xaije.

     Gyaran murya dad yayi tare da cewa "tunda dae babu aure tsakanin MIEMAH da ABDUL, na  bada auren MIEMAH ga Al'ameen. MIEMAH in na isa dake dan Allah kar kice Aa kiyi hakuri ki dauki hakan a matsayin kaddararki.

     Kuka sosai MIEMAH take "na amince dad". Tana fadin haka ta tashi da gudu ta fice.

     Dora wa yayi da fadin "sannan kuma na bada auren MARYAM ga Hakeem, shima FAROUK xa'a je a nemo masa auren Fatima tunda dae sun daidaita kansu. Shima ABDUL xan hadashi da axeema............ Mom ce tayi saurin cewa "a'a wannan hadin bai yi ba, ABDUL is totally broke hearted 💔,  bai kamata a bashi wacce basu daidaita kansu ba, ya kamata a barshi yayi jinyar xuciyar shi tukunna"    ammi ce tayi murmushi tare da cewa "kar ki damu da Abdul, baxai nuna damuwa akan hakan ba, xai kar6i duk xa6in da aka yi mishi".   Mom tace "bai kamata muyi amfani da biyayyarshi wajen jefa shi matsala ba, ya kamata mu bashi dama ya kawo wacce yake so tukunna". 

   Gyaran murya dad yayi tare da cewa "wannan haka yake ya kamata mu jinkirta mishi.  Nan aka yanka ranar aure nan da 2weeks kasancewar su MIEMAH sun kusa komawa school,  Da haka dae taro ya watse.

      Kuka sosai MIEMAH take, maryam tana lallashinta "maryam kinga dan ni marainiya ce shiyasa xa'a mun aure da wanda bana so"

     Duk lallashin da maryam ke wa MIEMAH amma taki sauraranta, ita dai kawai dan bata da uwa shiyasa xa'a mata auren dole.

     Yah Abdul maryam ta kira dan dai tasan shi kadai ne kawai xai iya lallashin MIEMAH.

.      lokacin yana kwance kan gadon asibity ana kara mishi ruwa kiran ya shigo, ganin maryam kamar baxai daga ba amma dae sai ya daga.

     Yah Abdul kayi wa MIEMAH fada sai kuka take wae dan ita marainiya ce shiyasa aka hada ta aure da yah Al'ameen.

     Dafe kirjinshi yayi idonshi yana cigaba da tsiyayar da hawaye, wato har an bashi ita ma kenan, shiknn ta fita a rabonshi. Kakalowa karfin gwiwa yayi tare da cewa "bata wayar" yana kokarin saita kanshi.

      Kukanta ne ya fara yi mishi sallama "MIEMAH kina so ki kashe ni ko?   Ai kuwa volume din kukanta ta kara tana cewa "mutuwa kuma yah Abdul??? Wlh in ka mutu nima mutuwa xanyi''

      Miemah in bakya so in mutu ki dena kuka, wlh kukan ki yana mugun tayar min da hankali ko kadan bana kaunar jin kukanki MIEMAH.

     Yah Abdul to sun raba mu pah, kasan Bama shiri ko kadan da AL'AMEEN, ni ya zanyi da raina kawai dan ni marainiya ce sai.......

MIEMAHWhere stories live. Discover now