MIEMAH page 33
Typing 📲
Story and written ✍ by�Khadija yusuf abba🌼🌼🌸🌸🌸🌸💮💮💮💮💮💮🌱
Gaba dayansu dagowa sukayi suna kallonta cike da mamaki, yah Abdul din ma kallonta yake cike da mamaki, Abbie ne yayi karfin halin cewa "MIEMAH kin sanshi ne?"
Murmushi tayi tare da cewa "ina shine Abdul din da Miemie xata aura? Shiyasa da na ganshi na ganeshi ae, juyawa tayi tare da kallon Miemie tace sis yau kinyi xa6e mai kyau wlh kun dace sosai". Murmushin jin dadi Miemie tayi yau yar uwarta ta yabe ta.
Numfashi yah Abdul ya sauke a hankali, shifa a tunanin shi MIEMAH ta dawo hankalinta ne, ashe dae da saura.
Miko mishi hannu tayi suka gaisa sannan yace "can we be a friends? Murmushi tayi tare da cewa "sure bro". Shima Murmushi yayi tare da cewa "thanks sis"
Mikewa yan matan sukayi su dukansu suka fice suka bar su Abbie.
Yah Abdul yace "dawowar tunaninta baxaiyi wuya ba tunda muna tare, xanyi kokari cikin labari ina sako mata rayuwarta ta baya, xan ajiye duk wani aiki da nake yi in bata time Dina har xuwa lokacin da xata dawo daedae"
Murmushi Abby yayi tare da cewa "Abdul bani da bakin gode maka, saedae nasan Kaidin alkhairi ne ga rayuwata, kuma garkuwa ga ahali na, Allah ya saka maka da alkhairinsa Abdul ". Ameen Abbie.
Da gudu Miemie ta rungume miemah tana cewa "sis yau ina cikin farin ciki wlh". Harararta MIEMAH tayi sannan tayi tafiyarta ta barsu wajen.
Kamo hannun ashnaah Miemie tayi suka xauna sannan ta bata labarin MIEMAH da yah Abdul ya basu.
Mamaki ne xalla a idon ashnaah, ayya Allah sarki Miema ashe har tayi aure ta haihu, Miemie wannan abin akwai sihiri a ciki wallah kuma akwai wacce nake xargi, cikin sauri ta mike tace bari naje na samu yah Abdul din Allah yasa bai tafi ba"
Cikin sauri Miemie ta riko Ashnaah tana cewa "Ashnaah kin dai san xato da xargi duk babu kyau ke yanxu waye kike xargi akan wannn lamarin kuma ma kina da tabbacin wannan sihiri ne?
Dallah malama sakar min hannu bana bukatar wa'azinki, ki fada min in ba sihiri ba miye wannan, tsawon shekaru goma sha biyar aka rasa Miemah kuma an mance da ita ma tamkar Ba'a ta6a halittar ta ba sae lokaci daya a tuna da ita, kuma a hakan ma a hannun arm robberies aka same ta, ni wlh nasan akwai sihiri sannan kuma ana neman rayuwarta. Tana fadin haka ta fice da gudu idanunta na xubda hawaye.
A parking space ta hangoshi da yah sadeeq, cikin sauri ta karasa garesu. "Ashnaah me ya faru ne? "Yah sadeeq, ina son magana da yah Abdul ne!
🤔to xa'a iya yin maganar a gabana ne ko kuma in baku waje? Aa yah sadeeq give us some space. Murmushi sukayi shida yah Abdul sannan sukayi sallama.
Mota suka bude suka shiga. "yah Abdul Miemie ta fada min komai game da alakar ku da MIEMAH, amma ni sae nake ganin akwai asiri a ciki.
Jijjiga kai yah Abdul yayi tare da cewa "kwarai kuwa akwai asiri, dan Miema lokacin da take tare damu ta mance wacece ita saboda tayi tunanin su mom ne suka haifeta, kuma a gaskiya dae Miemah ta mutu har anje an binne ta amma sae gata naxo na hadu da ita anan, wannan abin yana mugun daga min hanakali, kuma duk tunanin da xanyi nayi amma na kasa gano ta yanda akayi hakan ya faru.
Murmushi ashnaah tayi tare da cewa "muhada hannu kawae, ni jami'ar sirri ce amma kaf familyn mu babu wanda ya sani, kaima na fada maka ne sabida naga alamar kaima jami'in sirri ne, nasha gudanar da aikin sirri ba tare da sanin kowa ba kuma ina samun nasara Kasancewar babu wanda ya san aiki nah, yanxu ma haka akwai wacce nake suspecting game da batan Miema, ba ma batan Miema kadae ba akwai wani gaggarumin bincike da nake yi a kanta.
YOU ARE READING
MIEMAH
Historical FictionLabarin wata yarinya ce yar gidan shugaban kasa da take da tsiwa tun tana karama, hakan ne ya jawo mata yawan maqiya masu son ganin bayanta, Wanda har sukayi nasarar batar da ita daga Cikin ahalinta, ta fada wani ahalin na daban, ku biyo ni dan jin...