Part 29

9 1 0
                                    

👉🏽MIEMAH 👈🏽 page 29
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
   🍃🍃🍃🍃🍃🍃
        🌾🌾🌾🌾
              🌺🌺🌺

Typing 📲
      Story and written ✍ by
Khadija yusuf abba
 
Follow me on wattpad @khadija yusufbaba 🤟🏽🤟🏽🤟🏽

Bismillahir-rahmir-raheem

Duk abinda kaga ya samu bawa haka allah ya kaddara masa a rayuwarshi, sae mutum yayi hakuri ya dau jarabtar da Allah yayi mishi, insha Allah xaiga sakamako mai kyau.

NUSAIBA UMAR FAROUK & AMMI HAIFA wannan page din naku ne, na gode kwarai da kaunar ku gareni, kuma sauran ban mance da ku ba, ina nan xuwa gareku kuma ina alfahari da ku a duk inda kuke, Allah ya bar kauna.

***************************************

A

Life goes on, haka xamar tasu dae yake, suna nan suna cigaba da renon cikinsu dan yanxu haka ya girma ya kai wata biyar.

     Xiyarar baxata suka shirya wa su MARYAM. Nan suka shirya suka tafi London. Ai kuwa su maryam sunyi farin ciki sosai da ganin su MIEMAH. Nan aka xauna ana hirar yaushe gamo.

      Maryam kam yau da lpy gobe babu saboda cikin yana wahal da ita sosai, gashi yayi wani girma sosae, dakyar take tafiya duk tayi nauyi. Miemah sai sannu take mata.

      Besty tashi mu shiga kitchen muyi girki. Cewar maryam.

     Harararta MIEMAH tayi tare da cewa "wlh besty ke yar yawa ce, girki kuma ki duba pa kiga yanda muke, to ni da lpy nah ma banyi girki ba bare yanxu da nayi nauyi.

     Kama baki maryam tayi cike da mamaki tace "🤔 yah Ameen din me yake ci?

      Yatsine fuska MIEMAH tayi tare da cewa na 'yar aiki mana, dan nidae bani da time din da xanyi mishi girki. Ta fada tana kara turo Daurin kwalinta gaban goshi.

     Miemah me yasa? Me yasa baxaki yiwa mijinki girki ba kika barshi a hannun 'yar aiki, nasan dae xuwa yanxu kam wlh baki isa kice min bakya sanshi ba.

      Harararta tayi tare da cewa ke wlh besty dadi nah dake saurin gane abu, to miye a ciki dan naki yi mishi girki. Gskyar ki ne wlh na tsunduma kogin kaunar yah Ameen amma kawai bana so ya sani ne, so nake na wahal dashi tamkar yanda yah Abdul ya wahala lokacin da ya rasa ni.

      Ikon Allah, Miema duk akan yah Abdul dama kike yiwa yah Ameen rashin mutuncin nan, to wlh in yah Abdul yaji wannan abinda kike aikatawa baxaiyi alfahari da ke ba, sannan kuma xaiji haushinki sosai.

     Xaro ido MIEMAH tayi cike da mamaki tace "dan na wulakanta yah Ameen yah Abdul xai ji haushi nah?

     Yes, saboda kar ki manta yah ameen amanar uncle farhaan ne, sannan kuma uncle farhaan a yah Abdul ya barwa amanar yah Ameen, shi kuma yah Abdul ya baki amanar shi shine kike wulkantawa sannan kuma kike tunanin yah Abdul xaiyi alfahari dake🙄, to in baki sani ba ma gwamma ki sani yah Abdul xaiji ya tsaneki ne sabida kin kasa rike mishi amanar da ya baki.

      Hawaye ne ke tsiyaya daga idon MIEMAH!  Na bari wlh maryam na dena daga yau. (Ita pah Miema duk abinda yake da relations da yah Abdul tana mugun girmama shi) na yarda xan bawa Al'ameen kulawa sannan kuma xan tarairayeshi kamar kwai tun da dai shi din amanar yah Abdul ne.

      Murmushi maryam tayi tare da cewa "better"

Ni xan kori 'yar aikin mah!

     Aa Miema maganar koranta ma duk bai taso ba, ki barta ta xauna tare da ke ko ba komai xata tayaki koda da gyaran gida ne tunda dae ga situation da kike ciki, besides in kika koreta ma a ina xata samu kudin da xata nah biyan bukatun kanta?

MIEMAHWhere stories live. Discover now