Chapter 39

887 79 29
                                        

Turo dan karamin bakinta ta sakeyi duk ya bace da ice cream , girgiza kanshi yayi yana smiling

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.



Turo dan karamin bakinta ta sakeyi duk ya bace da ice cream , girgiza kanshi yayi yana smiling. Swimming pool in dake gabansu ya haudata kan wuyansa ya shiga ruwan da ita, dariya su duka suka dinga yi , masu aiki guda uku suka fito sukai saye daya ta rike pink towel Babba da karami na Nausheen sai Namijin ya rike white towel babba da karami na Mr Fauzi . Duck 🦆 na wasa Nanny Bonel ta ajiye cikin ruwan guda uku sai kifi na wasa,Mr Fauzi ya sauko da Nausheen daga wuyansa ya ajiye ta cikin ruwan nan ya fara koya mata swimming kamar yanda suka saba.

Bayan sun gama swimming in Nanny Bonel tayi draining gashin Nausheen shikuma Mr Fauzi ya karbi karamin towel yana goge gashin shi babban kuma ya daura a ugu, dakinshi ya nufa itakuma Nanny Bonel ta nufa dakin Nausheen da Nausheen in. Bayan sun isa daki Nanny Bonel ta kara goge ma Nausheen jikinta ta daure mata gashi da karamin pink towel inta, sai tasa mata pant da pink pj . hand dryer tasa ta ida busar da gashin ta shafa mata pink oil tasa ribbon 🎀 tai mata parking inshi. Zaunar da ita tayi kan gadon ta tare da ja mata pink blanket ta lulube mata kafuwanta tare da rage mata sanyin Ac ta fita taje ta hado mata tea tare da tea biscuits ta shigo dakin ta daura tray in kan wani dan karamin table irin wanda ake ajiyewa kan gado domin cin abinci ta aje mata.

Nausheen da take game a iPad ta ajeye ta sha tea in kadan da biscuits in , Nanny Bonel tai mata peck a kumatu ta dauke tray in tareda da kwantar da Nausheen tana fadin " sleep tight sweetheart." Nausheen tai mata bye bye tana fadin " Good night Nanny ."

Abuja Nigeria ,

Breaking News take kallo inda ake fira da Alhaji Muhammed Musa Bello Minister na yanzu na Abuja, tana gama sauraro ta mike zata shiga dakinta kenan sai ta saya tana juyowa a hankali, kallon kofar ta shiga yi rabon data shiga dakin nan harta manta , yakai kusan wata uku . Sai dai masu aiki su shiga su kula dashi , takawa tai harta isa bakin kofan, hannunta ta aza a handle in kofar ta murda a hankali tana shiga dakin, Allah sarki rayuwa kwance yake akan gado ya zama paralyzed. Ba ya iya yin komai sai an mai, a halin yanzu idanunshi da bakinshi ne kadai ke mosi. Sayawa tayi akanshi tana kare mai kallo, rabon da tasa shi a ido tun wata uku dasuka wuce.

"Hello how're you ? Get well soon huh , I miss you . Muhsin da Aslam ma haka, dan Allah ka dawo a masayin Khalid in Sarah." Tafada tana share kwalla, shidai Dad in banda kallonta babu abinda yake, abinda bata sani ba yasani cewa itace tasa yayi hadarin mota har yakai ga condition in da yake ciki. So tayi da ya mutu amma Allah ya kaddara yana da sauran kwanaki.

New York,

Nanny Bonel ta gama sa mata uniform inta na school , hannunta ta kamo suna fitowa daga daki. Saukowa suke daga stairs suka karaso parlo. Mr Fauzi da Lala suka tarar a dining table suna fira, da gudu Nausheen taje tai hugging in Pap tana " Good morning Pa." Lala na murmushi itama ta bude hannuwanta tana jiran Nausheen tai hugging amma ina Nausheen na jikin Pa inta . Dagata sama yayi cak ya ajiyeta kan kujerar dake kusa da kujerar shi . Lala kuwa taji zafin Nausheen ko kallonta batayi ba, amma inda sabo yakamata ace ta saba, Mr Fauzi yace " How was your night My munchkin ." Nausheen data dauki Bread ansa sausage a ciki takai baki ta dan ci tace " It was cool Pap ."

Minister's Son Where stories live. Discover now