Chapter 42

664 86 23
                                    



Washe gari walima bayan ankai Amarya gidansu ango dake a Games Village, dagin ango sun siya bakin Amarya a naira Million 5 wanda sun bada kudin cash sannan sunyi ma Amarya like wanda kudin like in shima na Amarya ne . Kawayen Amarya ko wace an bata five hundred thousand naira kudin Makeup dana anko .

Ango ya iso wurin walimar tareda abokansa, ya zauna kan kujerar da Farha take wanda ta ango da Amarya ce , Bayan shigowar ango Mufti Menk shima ya iso yayi masu wa'azi tare da huduba, yana gamawa aka ci abinci aka rufe taro da addu'a . Faty ce ta kalli Islam tace " Toh Adda sai ayi bankwana da Amarya mu fara tafiya tunda bada ita zamu komaba." Islam kau kallon Farha kawai takeyi da ta rufe fuskarta da lafaya abokanta na pictures da ita shiko angon sun shiga ciki yana tautaunawa da Mufti Menk. Waiwaye ta dunga taga ko zataga Mr Fauzi cikin abokan angon amma sam ko inuwarsa babu.

Habeeb taga yana tunkaro su sai ta tuno Jidds na kusa da ita wurinta zaizo , yana isowa yayi masu sallam suka gaisa Jidds ta mike ta bishi suka fita, Maryam ta kalli Islam tace " Inajin saboda ke yayi avoiding zuwa ." Tabe baki Islam tayi ta mike ta nufa wurin Farha , kamo hannun Farha tayi tace " Baki ci komai ba sai tea da kika sha ko shima ba sosai ba." Farha tasa handkerchief ta goge hancinta dake zuba saboda hawayen dake zuba tun dazu daga idanunta. Islam tace " Farha dole fa ki kula da kanki ko kinaso ki dinga samu cikin damuwa nida Ummi ?" Farha da muryarta ta shake tace " Banajin yunwa ne." Dafa fuskarta Islam tayi dukda an rufe fuskar da lafaya tace " Farha kinzo gidan da ake sonki, nanda gida bashida wani banbanci. Koda akwai kadan ne, Allah ya baki sweet and loving mother in law wadda take sonki kamar yar cikinta ga kuma Adeel da zai iya bada komai nashi saboda ke he loves you to the moon and back Farha sai sister in law inki wadda takeson ki kamar ni kuma zata maye maki gurbi na so minene yasa kika damu dan kin rabu damu alhalin bawai mun rabu ba zaki iya zuwa duk sanda kikaga kinaso , wannan shine sabuwar rayuwar ki Farha kuma muma muna cikin ta so please Farha take care of yourself and your husband ki cire damuwa we're always here for you kinji ?" Murmushi Farha tayi tace " You're making me emotional, ki tashi ku tafi dan Allah yanda mutane suma zasu rage ni kowama yazo ya tafi I want to be alone with my husband." Sakin baki Islam tayi tana jin ikon Allah,Faty ce ta iso wurin tace " Amarya ki kyale Adda hakanan mu tafi gida haba sai kace aure kanki farau." Farha tace " Ai ni tafiyarku sai tafi man dadi dan Allah tatara kowa harda Adda ku tafi angode." Sakin baki itama Faty tayi tana kallonta tace " Au lallai ma yarinyar nan, ko kunyar Adda yanzu baki ji?" Islam ta mike tana fadin " Ke kike tunanin wata kunya yanzu wuce mu tafi bari mu kyaleta ta ji abinda ake ji zata nememu." Faty tace " Aikuwa toh Amarya sai munzo jin labari a samo mana yan biyu." Tana gama fadin haka suka wuce Maryam ma ta taso nan suka tatara mutanensu dama Anzo da bus 🚎 ta kwashe mutanen Islam kuma ta shiga motarta ita da Maryam da Faty , Jidds kuma tunda suka fita ita da Habeeb suna cikin motar Habeeb so sai kawai Islam ta fada mata cewa sun wuce .

Shiko gogan yana tashi yaje gym in cikin gidan yana fitowa yayi wanka yasa farar shaddda yaje Masallaci dake cikin gidan yana dawowa yaci salat a masayin lunch 🥗 ya fita shida Muhsin sukaje Fauzi Company ma aikatan wurin ba karamin dadi sukaji ba ganin shi da sukayi, ya duba yanda aiyukan wurin ke tafiya yaga komai Masha Allah Habeeb na tafiyar da company in yanda ya kamata. A nan yayi sallar la'asar yana gamawa yaje Gidan marayunsa yaga yanda abubuwa ke ciki nan ne ya samu labarin an sake bude wani gidan marayu wanda suna kula da marayu kamar nashi kasancewar gidan marayun Mr Fauzi is the best so far kafin ka samu gidan marayu dake da tsafta da kula da yaran kamar gidan marayun turawa irin na Mr Fauzi a nigeria yana wahala, to yanzu ana fada mai cewa an bude wani sak irin nasa shima so Masha Allah.

Information in wurin ya kara bukata nan aka nasar mai komai gameda wurin, Murmushi yayi sai yaji yana son ya hadu da mai wurin. Kallon Hajiya Rabi yayi yace "waye keda wurin?" Hajiya Rabi tace "wannan shine har yanzu bamu sani ba sir, kamar ana boye sunan mai wurin ." Mr Fauzi yace " miye sunan wurin ma?" Hajiya Rabi tace " IAF homes."

Minister's Son Where stories live. Discover now