Chapter 17

866 87 1
                                    

A hankali yake saukowa daga jirgi, wata mota dake parke kirar BMW naga ya shiga, wanda yake cikin motar ya juyo ya kalleshi tare da fadin "Well done Habeeb ya London? " Wanda aka kira da Habeeb ya kalleshi tare da sakin murmushin dake kara mai kyau kasancewarshi hadaden saurayi, baki ne shi amma ba sosai ba za'a iya kiranshi chocolate, fatarshi tana glowing da mutum ya gani yasan yana kula da skin inshi sosai, yanada Lulu eyes sai eyelashes zura zura dasuka kara mai kyau, hancin shi dogo sai kyakyawan gashin kanshi wanda ya kwanta luf luf kamar na Mr fauzi , Habeeb yace " London is fine Adeel let's go Mr fauzi must be waiting for me. " Tada motar Adeel yayi tareda fisgar motar suka bar airport in .

Waye Habeeb da Adeel?

Habeeb babban abokin Mr fauzi ne shine aminin sa tun suna US suke tare, Habeeb dandan Senator ne ya karanci Business admin tare da Mr fauzi yanzu haka shine yake jagoran companies in Mr fauzi dake London . Adeel kuma Aide in Mr fauzi ne amma tamkar aboki yake.

Habeeb ya dawo hutu sai ya taho ma Mr fauzi da designer suit inshi wanda Mr fauzi yasashi ya taho dashi dayake designer in Mr fauzi a London yake.

*********

Takaici duk yabi ya dame shi, yanzu kamar shi za'ayiwa auren dole oh shit . Tune rigar shi yayi tare da fadawa cikin swimming pool in dake gabanshi .

Islam tazo wucewa tagan shi yana cire riga ya fada ruwa ranshi a bace, girgiza kanta tayi tare da furta "Allah ya shirya ". Kasancewar tattoo in data gani a jikinshi tare da barin wurin dama wucewa tazo yi.

Habeeb da Adeel ne suka turo kofar dakin tare da shigowa suka zauna kan sofa suna kallon Mr fauzi yana swimming ta Glass door in dake dakin. Adeel ne ya mike ya ajiyewa Mr fauzi suit in shi kan gado ya koma ya zauna.

Suna cikin fira Sai ga Mr fauzi ya shigo da towel daure a ugunsa, suna ganinshi duk suka mike suna gaisawa da shi, sai da ya zauna kan gado sannan suma suka zauna , kallon Habeeb yayi tare da fadin " Guy how far? " Habeeb ya yamusa fuska alamun gajiya "Am exhausted mah nigga. " mikewa Mr fauzi yayi ya dauko dauko dan karamin farin towel ya fara goge gashin kanshi.

Wani servant ya shigo cikin yana fadin "Sir the table is ready. " Mr fauzi da ya maida hankali yana busar da gashin kanshi da hand dryer yace masu Habeeb " Habeeb Da Adeel bismillar ku. " Mike sukayi suka bi servant in ya kaisu dinning table.



Mom da Dad ne a private jet Mom tace ma Dad " Abban Muhsin I hope Mami will like my gift for her. " murmushi yayi tare da cewa " Why not? You're always her favorite daughter in law so bansan ko yanzu abu ya canza ba. " jikin Mom ne yayi sanyi dama ko can baya asiri ne take zuba ma Mami dan tafi sonta akan Afrah mahaifiyarsu Islam amma yanzu taga kamar asirin ya fara lalacewa. Yaushe rabon da tayi wa Mami asiri tun 18years back saboda burinta ya cika an kori Afrah shiyasa ta bar yi (Allah ya rabamu daga yin shirka)

Mai gyaran gashin shi yagama ya gama gyara mai haka zalika mai make Up inshi ya gama (kusan ana ma maza makeup amma ba irin na mata ba especially masu kudi da celebrities) ya sa suit inshi Masha Allah sai ya fito a farin balarenshi cikin Red suit inshi.  Links inshi masu shegen kyau , neck tie kuma Black ne agogo ma haka kirar Rolex Black sai takalma Gucci cover shoes Red (wow karku so kuga farar kafar Mr fauzi cikin Red cover shoes 😍😍😍😍) designer inshi mai shirya sa na nan Nigeria ya gama shirya shi sai ya feshe shi da turaruka kala kala yanda yake zuba kamshi zai iya tada ma mutum hankali da ruda yan mata.


Islam ce ta shigo dakin Mami dan nuna mata kwalliyarta, Mami ce zaune ana mata light makeup Islam tace " Iyee gaskiya mai makeup kar ta fini yin kyau dan kar ta kwace duka samarin da zasu zo. " Dariya duk suka kwashe dashi Mami tace " Ai karki damu ke nariga da namiki zabi. "

Islam tace " to shikenan Mami in kuma bai man ba zan kwace bazawarin da zakiyi. " duk a cikin wasa " Haba dai ai ni duk wani namiji da zanyi they are loyal. " dariya duk suka sake kwashewa dashi.

Farha ce take saukowa daga bene cikin Sky blue jumpsuit inta tayi kyau sosai Masha Allah, Mami ce duk ta sayen masu kayan da makeup ita ta biya kudin. Muhsin dake zaune cikin Sky blue suit da Sky blue cover shoes sai agogo Gucci ya sha kyau Sai zuba kamshi yake yana lasa wayarsa yaji ana saukowa daga bene kasancewar takalmanta masu sini ne, dago yai yaga Farha ce ya yanda tayi kyau saida gabansa ya fadi saboda kyan da tayi. Killer Smile inshi ya sakar mata lokacin da suka hada ido " Hey beautiful come sit here. " yana nuna mata kusa dashi, a hankali ta taho ta zauna saidai akwai Space kadan a sakanin su.

" Good afternoon. " ta gaishe shi tare da dukar da kanta Kasa tana wasa da zoben hannunta. Kallonta ya keyi bayan minti 6 ya amsa mata "How have you been? " Dagowa tayi suka hada ido sannan ta maida kanta Kasa taci gaba da wasa da zoben hannunta tare da fadin "I'm good ,you ?" dan ita harga Allah ya mata kyau ga wani kamshi mai dadi dake tashi a jikinshi dukda itama tana kamshin amma nashi yafi yawa da dadi, shiko birgeshi take yadda take dukar da kanta tana wasa da zoben hannunta, murmushi yayi "splendid " kawai yace yaci gaba da danna wayarsa.

Mami ce cikin red Cinderella gown tayi kyau kamar ba sohowa ba ga daurin tasha ga kuma Red jambaki tasha abunka da Farar Mace Sai kuma sakar gold dake wuyanta abun saidai muce masha Allah...................

Minister's Son Where stories live. Discover now