Chapter 5

959 89 0
                                        

Yana fitowa daga wanka da towel daure a ugunshi yaga Amnah ta fiddo mai kayan da zai sa, farar T-shirt da Farin sweatpants . Murmushi tai mai sannan tace Bimbin wear this sai muje kaci abinci.

Thank you. Yace yana karba, sannan ya kalleta yaga bata fita ba tananan. Can you please excuse me. Cewar Mr Fauzi.

Amnah ta shagwaba fuska tana ce mai  Bimbim please let me help you.

Ranshi yaji ya bace wato kaya zata taya shi sawa kenan. Kayan zaki tayani sawa?

Yes . Tafada tana kallon kirjin shi wanda yasha gym.

Amnah.

Na'am

Get out. Yafada a hankali.

But Bimbim.....

I said get out!!! Ya daka mata sawa.

Hawaye ne ya zubo mata da gudu ta fita.

Numfashi Ummi ta sauke jin abinda Islam ta fada mata sannan ta dago tana kallon Farha dake ta bacci. Allah ya saka ma Eyah da Maman Aisha yanzu zan saida furniture dina bayan haka ina da twenty thousand sai mugani ina zamu samu sauran kudin Allah yaci da mu. Cewar Ummi.

Ameen Ummi amma yanzu zai wuya mu samu dukda bashi ne mukeso.

Allah zai kawo mafita Islam.

Ummi nace ba mi zai hana mu gayama dangin Abbi?

Da sauri Ummi ta dago tana kallon Islam, gabanta taji yana faduwa ba sauki.

Come zauna nan kusa da mamanka yarona. Cewar Mom tana ce ma Mr Fauzi, jawo kujera yai ya zauna inda ta nuna mai kusa da ita.

So Bro how is your business going on? Muhsin ya tambaya yana cin chips da folk.

Kai baka gajiya da cin chips ne? Mr Fauzi ya tambayi Muhsin.

I don't think zan iya rayuwa inba chips kamar yadda kaima baka iya rayuwa ba coffee. Cewar Muhsin

Dariya suka yi su duka kowa ya cigaba da cin abinci, wata Maid ce tazo tai serving Mr Fauzi sannan ya fara cin abinci. Karar Spoon, Folk da table knife kawai kakeji.

Minister's Son Where stories live. Discover now