Chapter 30

901 97 9
                                    


A kwana a tashi abun ba wuya har anyi sadakar arba'in na Mami . Jiya akayi sadakar yau su Ummi da Farha suna hada kayansu domin komawa katsina , Islam dake tayasu daka ganta kasan ba da son ranta take so su tafi ba . Farha da Ummi duk sun fahimce cewa Islam bata son su tafi , " Adda karki damu kullum zamu dinga waya kinsan dai dole mu tafi bai kamata muzo mu zauna a nan ba kinsan yarda Abuja take da tsadan rayuwa . " Ummi ma tace " in Banda abun ki Islam tayaya zamu zauna a nan ? Kinsan yarda garin nan yake da tsadar rayuwa Kuma ni ba sana'a ba ga karatun Farha yanzu zata shiga jami'a shifa ?"

" Ummi albashi na zan iya kula daku har in dauki nauyin karatun Farha , Zan iya sa Farha Nile University in Kuma kula daku Dan Allah Ummi ku zauna a nan tare Dani . "

" Dan Allah Adda zaki sani a Nile ? Dan Allah Ummi mu zauna nan please ." Cewar Farha cikin murna , Ummi ta Dan harareta " Ke Farha katsina zamu koma kinaji na ? Kekuma Islam kiyi hakuri ba zaki gane bane naga alama ." Islam tace " ai kundai yi breakfast kafin kuce zaku dauki hanya ko ? "

Ummi tace " bari na Ida hada kayan nan kuyi gaba ga Ni nan bayanku.  " Nan Islam da Farha suka fita daga dakin Ummi Kuma ta saya tana ida hada kayan .

Dad ne zaune a cikin Rolls Royce yana contemplating ko yaje gidan ko kuwa ? Already yasa an gano mai inda suke zaune . Can ya yanke hukuncin zuwa gidan amma yana soron abunda zai biyo baya in Mom ta sani , Kuma Yana soron ya Afrah za tayi reacting in ta ganshi .

Suna cikin yin breakfast sukaji karar door bell , Farha ta mike tazo ta bude kofar . Sosai gabanta ya fadi itadai duk sanda ta ganshi sai taji gabanta na faduwa ko saboda kamar shi da Abby ? " In..a wu...ni shi...go ." Dakyar ta iya fadin haka , shigowa yayi Yana fadin " muna lafiya kiyi min magana da Mamanki da sister inki ."  Ya fada Yana zama . Itakuma Farha wucewa tayi taje tace ma Ummi " Ummi ki sauri kizo ki ga Wanda yazo you won't believe this but I'm telling you the truth mai kama da Abby ne Mr Khalid Fauzi. " Kusan suman zaune Ummi tayi , mi Khalid yazo yi anan ? Badai wulakanci yazo yi masu ba ? Islam kuwa taga yanda yanayin Ummi ya chanza itadai daman tasan akwai abunda ke faruwa a family in nan Kuma Insha Allah zata gano hakan koba da sanin Ummi ba.  " Ummi lafiyarki kuwa ? Muje Yana jira fa ." Jiki ba kwari haka Ummi ta mike suka tafi .

Zaune suka iske shi yana kallon tv in dake aiki , zama tayi Islam ta gaishe shi ya amsa . Ummi tace " Ina wuni ." Shima ya amsa da lafiya lau sai ya kalli Islam da Farha yace " ya yaranki ? " Nan itama ta amsa da lafiya . Gyaran murya yayi yace " Ku danyi excusing inmu zanyi magana da Mamanku ." Tashi sukai suka bar wurin itadai Ummi duk fargaba ya cika mata zuciya Dan bata San da wani kullin Khalid yazo ba .

" Abubuwa dayawa sun faru a baya wanda Nima dasa hannuna amma Afrah inaso kisani Khalid in da kika sani da bashi bane yanzu , wannan Wanda kike gani is a change man . Nasan cewa rasa miji Yana daya daga cikin babbar kadara Afrah you're a strong woman , yanxu bansan miye plan inki ba amma nasan cewa diyarki itace PA in Aslam . To ke miye naki plan in ? Zaki zauna da ita a nan ? "

" No it's better nida Farha mu koma katsina saboda bansan abunda kuke kullawa ba kaida Sarah itakuma Islam Allah zai kareta daga shairin ku . "

Murmushi Dad yayi irin na manya yace " Nasan ai is hardly ki yarda Dani saboda abunda ya faru a baya , kamar yanda na fada maki rasuwar Mami ta man wa'azi sosai Islam da Farha kamar yayana suke nima  I want the best for them .

Murmushin gefen baki Ummi tayi tace " Daga baya kenan , yanzu kasan cewa kamar yayanka suke Khalid ? Bayan Kai dasa hannun ka aka depriving insu rights insu , sukai rayuwa kamar yaran talakwa alhalin mahaifinsu mai arziki atajiri ne , ka gaji na cin arzikinsu ne ? "

" Komai yana da lokaci , arzikinsu za a maido masu Insha Allah . Akwai wani gida dake Maitama na Khalifa ne Mami ta kara modernising inshi zan turo driver yanzu ya kawo maki takardun gidan . Kina iya zama ciki keda yaranki tunda gidan naku ne . "

Minister's Son Where stories live. Discover now