Chapter 6

954 107 1
                                    

Islam tasan ta yi laifi data ambaci dangin Abbi. Itadai abun yana bata mamaki yarda ummi bata son ka ambaci dangin Abbi ko da wasa. Ko da yaushe tunanin Islam daya ne miyasa ummi take soron taji an ambaci dangin Abbi? Itadai ko da ta taso bata sansu ba, tayi rayuwar ta a Maiduguri lokacin da Abbi na raye ko lokacin bata san dangin Abbi ba saidai in tana yarinya lokacin bata da wayau.

Ummi kuma ba yar Nigeria bace tadai san Ummi yar India ce ko kallonta kai kasan baindia ce, haka zalika bata san dangin Ummi ba saboda basu taba zuwa India wurin family in Ummi ko lokacin da Abbi na raye.

Saidai lokacin da Islam tayi wayau sosai har ta shiga university dinta sannan ta damu ummi lallai sai ta gwada mata dangin ta ko gaya Mata suwaye su sannan Ummi ta gaya mata ita yar india ce kuma iyayenta gunki suke bauta mawa (Hindu) shiyasa ta rabu dasu , shine kawai abunda Ummi ke gaya mata.

Islam so nawa zan gaya maki karki sake Man maganar dangin Abbi? Sau nawa!!! Ummi ta daka mata sawa.

Ummi kiyi hakuri in na bata maki rai naga ne bamu da wata mafita da ya wuce mu gaya ma dangin........

Ya isa!!! In har kina so kada raina da naki ya bace kar in sake jin kinman maganar dangin ubanki ko mutuwa Farha zatai indai sune zasu ceceta saidai ta mutu dan bana bukatar taimakon su ko a mafalki!!! Ummi ta fada ranta duk a bace wanda Islam bata taba ganin ran ummi ya bace haka ba . To minene dangin Abbi sukayi ma Ummi da har tayi fushi dasu haka, itadai tasan Ummi mace ce mai hakuri tabbas abunda dangin Abbi sukayi mata ba karami bane.

Shikenan Ummi dan Allah kiyi hakuri bazan sake ba Insha Allah.

Saye yake yana kallon window yanda iska yake hura flowers din cikin gidanshi. Yayi nisa cikin tunani sai kawai yaji an taba shi, juyowa yai ya kallonta.

Haba Baban Muhsin me kake tunani haka ? Cewar Mom

Hmmm ina tuna baya ne . Inji Dad

kana tuna Abbi kenan?

Hmmmmm . Numfashi kawai Dad ya sauke.

Baba Muhsin let by gones be by gones , yawan tunani nasa hawan jini.

Sara. Dad yakira sunan Mom sai ya numfasa sannan yacigaba da magana wato a kullum dan Uwana yana cikin rai na, every single day....... Am feeling guilty of.........

Enough!  Don't say anything again, just keep quiet before someone hear you. Mom tafada tana dafa kafadan Dad.

Mom ! Mom ! Mom ! Mr Fauzi yake kwalla ma Mom Kira har ya shigo dakin domin gannin in tananan. Yana shigowa ya ganta sai yai mata murmushi yace There you are.

Oh sorry Bimbim let's go. Tafada tana dauko jakarta sannan ta kalli Dad tace mai we are going out to have fun with my son wanna join?

No thank you it will be better if you  go along with him,besides he is your favorite kuma kun dade baku fita ku biyu ba I know you want to be alone with him so enjoy. Cewar Dad yana bude closet dan chanza kaya.

OK Sai mun dawo. Inji Mom tana kama hannun Mr Fauzi.

Dad sai mun dawo. Cewar Mr Fauzi suna fita daga dakin.

Allah ya kiyaye.

Suna fitowa daidai zasu fito daga first floor saiga Amnah da Muhsin sun shigo wasu Maid mata guda biyu a bayan su sun rike shopping bags da alamu shopping suka fita.

Amnah ta kalli Mr Fauzi sai kawai taji inama Mom Zata yi mata tayin fitar da zasuyi. Sai tace Are you going out?

Yes dear am going out with my Son. Cewar Mom.

Muhsin yace that's nice, have fun . Yana gama fadar haka yai shigewar shi har ya haye bene .

Amnah tace OK aimun saraba Bimbim.

OK. Kawai yace mata sukai tafiyar su.

Hi loves,
I know you must be wondering wacece Islam? Miye connection din Abbi da Dad? Miyasa Ummi bata san maganar dangin Abbi ? Miyasa Mom bata son Dad yakawo maganar Abbi ko tunanin shi?

Ku biyoni domin samun amsoshin tambayarku.

Kar ku manta Minister's son yazo da lots and lots of fun 🔥🔥🔥🔥

Hurairaytu 🍸🍸🍸🍸🍸🍸🍸🍹🍹

Minister's Son Where stories live. Discover now