Chapter 38

714 57 28
                                    

A fusace Dad ya sha gaban Mom cike da haushinta yace " Enough is enough Sara, kinyi abinda kike ganin kin isa toh yanzu nima zan gwada maki na isa." Yafada yana juyawa da niyyar tafiya saidai jin Mom tace "Toh Bismillah Allah ya baka sa'a amma sakamakon bazai maka kyau ba ." Yasa shi sayawa, itakuwa tana gama fadin haka ta wuce ta fita daga dakin.

Yasan Mom can be wild amma shi a ganin shi bazata iya yi mai komai ba saboda ko ba komai sun ajeye ya'ya , yayi iya abinda zai iya don nunawa Mom cewa zai yi abinda tasa shi amma ta shafa ma Ummi dasu Islam lafiya hakanan tunda ta raba Aslam da Islam a tunaninshi zata kyalesu Islam hakanan amma da alamu tana shirya wani abun don haka bazai kara barinta ko goya mata baya ba don hakan da yakeyi yana kara sata yin wasu abubuwan alhalin shi yana yin hakan don ta shafa masu Ummi lafiya inta yi succeeding raba Aslam da Islam amma yaga Sam ba haka ba yanzu Allah kadai yasan abinda take shiryawa don haka dolen shi ne yaga ya dakatar da ita.

Wata kwalbar wine ya kara fasawa ya kafa a bakinshi yana kwankwada saida ya kusan wuce Rabi sannan ya cire bakinsa, itadai Lala dake kusa dashi tana son hana shi sha hakanan don yasha dayawa ko abincin Kirki babu a cikinsa amma tana soron hana shi don kada ya juye haushin da yakeji akanta. Hannunta na kyarma ta taba shi tana fadin " Baby mai kakeson ci na dafa duk yau babu komai a cikinka sai wine."

Yi yayi kamar bai jita ba ya kara kafa kwalbar a baki sai daya shanye tas sannan ya mike jiki babu kwari da sauri Lala ta mike ta rikeshi suka shiga hawan bene har suka shiga daki. Suna shiga dakin ya fada toilet haba sai amai, da sauri Lala ta shiga cikin toilet tana mai sannu tana shafa mai baya . Bayan ya gama Lala ta cire mai riga ta tayashi gyara toilet sai ta fito ya wasa ruwa ya fito. Lokacin da ya fito Lala ta shiga kitchen tana toasting bread sai Coffee data hada mai, dakin ta nufa sai ta iske shi yana sallah. Ajiye tray in tayi ta jira shi ya gama sai taga yana addu'a harda hawaye. Batasan lokacin da itama ta fara nata hawayen ba, share hawayenta tayi shikuma ya gama addu'ar ya mike ya zauna kan couch itama ta mike ta ajiye stool a gabanshi ta ajiye tray in kan stool tace " Dan Allah kaci for the sake of our Baby." Da manakinta taga ya dauki coffee in ya sha shima toasted bread in yaci, smiling tayi sai ya lura yace " why are you smiling?"

" Am proud of my Baby's Father, don Allah don't change."

" miyasa kikace haka?"

" saboda zaka iya yima Baby mu komai amma ina soron wata rana ka chanja saboda Islam."

Murmushin yayi wanda shi kadai yasan ma'anar sa ya kamo duka hannayenta yace " I promise to be a good Father and a good husband Lala."

Murmushi tayi chan kuma sai yaga murmushin ya bace yace " what's wrong Lala ?" Lala tana hawaye tace " naji dadi sosai amma maganar ka yasa naji farincikin dana tuno maganar ka ta karshe yasa naji ya tafi sai damuwa da bakinciki ."

" why lala."

" saboda nasan baka sona, Islam kake so kuma ita zaka aura." Rumse idanunshi yayi gam, yana budewa saiga hawaye ya kara mase hannun Lala yace " You're my future wife Lala ."

Tunda safe wuraren karfe goma Barrister steve lawyer na Mr Fauzi yaje Kapadoccia restaurant ya iske Islam da lawyer inta Barrister lawal . Barr steve yasa Islam tayi signing wasu takardu ya bata wasu kaddarorin data cema Mr Fauzi ya bata ya zama mallakinta yanzu Mr steve yayi masu sallama bayan sun gama komai.

Bayan ta dawo gida ta iske Farha na kallon parasite itama Ummi da alamu tana daki tana bacci, shiga daki tayi ta wasa ruwa don yau ranar is harsh ta fito ta shiga kicin ta zubo abinci tazo Falo ta zauna chakula abincin tayi basan ci take ba don abinda takeji a zuciyarta bazata iya cin abinci ba saidai saboda yunwan dake cinta rabon ta da abinci tun jiya da rana. "Love ." Shine sunan da aka kira wata dashi a cikin tv itakuwa Islam tana jin haka tayi saurin dagowa, Tuno mata da Mr Fauzi da ita sukai da sauri ta ture plate in abincin ta ruga daki tana kuka.

Minister's Son Where stories live. Discover now