Chapter 24

859 126 18
                                        

Kallon da yayi mata yasa tasha jinin jikinta , bude bakinta taiyi tace " No ba haka bane , dama nazo na sanar dakai anyi booking appointment in , Kuma na kira ka baka daga ba sai nayi deciding nazo na sameka shine ta shigo ta ganni . " Kallon security in yayi yace "Get out ." Bayan fitar security in yace ma Islam " Kije Adeel ya baki number ina, Kuma kar ki sake shigomin office inba nina nemeki ba, don't reach your limits ."

"Okay." Tace ta fita, maido kallonshi yayi kan Amnah yace " What you did was totally wrong, stop accusing people akan abinda baki sani ba , daga yau bazan sake daukar shirmen nan naki ba !!!" Hauda hannunta tayi akan kirjinshi tana kokarin ta rumgume shi tace " Okay I'm sorry bazan kara." Tura ta yayi yace " I wanna be alone ." Daukar jikarta tayi ta fice , ta sani Sarai in bata fita ba to bata mata rai zaiyi .

Maiduguri ,

Lunch sukeyi a dining table ba wanda ke magana , shide Muhsin ba magana zai ma Ummi ba , Kuma bazai gaishe taba .

Mami ta rasa yarda zata bullo ma al'amarin , tanaso tayi introducing Ummi wurin Muhsin amma tarasa ta'ina zata Fara , shin ta gabatar dasu koko ta bari saita kira Aslam , wata zuciyar tace ta bari saita kira Aslam , sai tai sticking to wannan shawarar . Ummi Kuma on the other hand Sam she's not comfortable, tasan Mami wants to make up for everything she did, ita harga Allah ta yafe ma Mami , Kuma tana jin dadin yadda Mami ke treating insu especially Islam , ta lura Mami duk tafi son Islam .

Farha Kuma itadai cin abincinta take hankali kwance , amma tanaso tasan mike sakanin Mami da Muhsin ? Shin suna da wata alaka ita da Muhsin ? Murya Muhsin ce ta maido ta daga tunanin da take " Mami nizan tafi ." Mami tace "to saika dawo ."

Sannan Mami tace ma Farha " wane country ne kika fiso kije ?" Farha tai murmushi tace " Parris , city of love."

" Wow kin iya zabi , Ajimobi zaizo anjima zaku je ke da Ummi ayi maku komai na shirin tafiya ." Ai Farha batasan lokacin da ta hugging Mami ba " Thanks alot Mami , I love you so much." Tayi mata peck , Ummi tace "Zaifi kema idan kika biyo mu Mami keda Islam sai ai ma ogan nata magana ." Mami tace " Nima zanso haka amma yanzu ki fara tafiya keda Farha inkun dawo sai Islam ta zabar mana wani country in , sai muje mu duka . Kinga ita Islam yau ta Fara zuwa wurin aiki a bari sai nan gaba ." Ummi tace " To shikenan hakan ma yayi , Allah yasa ka da Alheri ." Da "Ameen." Ta amsa mata .

Suna gama cin abinci Farha tayo daki ta buga ma Islam kira , bata wani dade da ringing ba Islam ta dauka , Muryar Farha ta jiyo " Yeyyy Adda kinsan me ? " Islam tace " Bansani ba amma daga jin Muryar ki you're in a good mood."

Farha tace " Yes I'm happy , I'm soso happy ."

" Kinga go straight to the point , I just came back from work , and kinsan mi ? I had a horrible day ."

" Ayya miya sameki ? Karki cemin aikin ba dadi ?."

" Farha ba zaki gane ba , wato wurin akwai marasa mutunci dayawa kinsan mi ? ." Farha ta bata rai tace " Badai rashin mutunci akayi maki ba ? " Islam ta kwanta kan gado tana fadin " Ba sau daya ba sau biyu." Nan ta bata labari komai , ai karku so kuga yarda ran Farha ya bace , farincikin da take ciki ya bushe saima tafalfasa da zuciyarta keyi , inama ace zata wanga Lala da Amnah , ashe Islam tayi gaskiya da take ce mata Farha ki rage son Amnah Fauzi Kuma ki rage ganinta a masayin Role Model , baki santa ba sosai , Baki san ya take da addinin taba , Kuma Baki san yarda take gudanar da rayuwarta ba , saidai kice Allah ya Baki kudi ki dinga sa kaya masu kyau irin nata kinasa gold tunda naga kina son gayu .

Farha tace " Ni ke kika fi bani haushi , wallahi nidai bazan dauki wulakanci ba , Lala take kowa take ta guje ranar da zan hadu da ita dan saita gane ta mari yayar Farha Khalifa Fauzi . Ita Kuma Amnah Fauzi saina wulakan tata a gaban jama'a , just wait and see, I will soon come to Abuja zasu gane basu da wayau , banzaye asararu ."

Minister's Son Where stories live. Discover now