Maiduguri , Nigeria.
Private jet nasu Mr Fauzi ya sauka lafiya ga motoci nan suna jiran isowarsu, Islam kau bayan Sun iso maiduguri nan take suka saida Cap Ummi tace " Fauzi Mansion " yace "Muje ai ba wanda baisan gidan Fauzi ba a Maiduguri ." Ummi tace " to muje mana. " suna shiga cikin taxi .
Sun iso gaban Mansion din mai taxi ya ajiyesu ya kara gaba, baki bude Islam da Farha suke kallon tankamemen Mansion din dake gaban su, Farha take maganar zuciya tana cewa ashe dama haka suke da arziki shine suke rayuwar talauci a Katsina, to waima miya kaisu katsina? miyasa basa cikin Mansion suna rayuwar jin dadi tunda ga alama su Abby masu kudi ne.
Farha Allah yayi ta mace mai son rayuwa irin ta jin dadi ta ganta cikin katon gida dasa kaya irin na masu kudi saidai ta hakura tunda ba masu kudi Allah yayi su ba amma yanzu kam data ganta gaban gidansu Abby Ummi has a lot to explain to her.
Karasowa suka yi gaban gate din gidan irin na castle , Gate Mans sunkai 5 wanda kuma da alama duk ba hausawa bane daya ne kacal kuma dattijo. Daya daga cikin securities ya kalle su daga sama har kasa sannan ya daure fuska don da alama wa'inan ba masu arziki bane to mi ya kawo su nan? " Who do you want to see? " Ummi tace " Mami please hope she is around? " tabe baki yayi " You want to see Mami Hahhhhh? Madam oya leave this place now now !!" shi a cewar shi ya dauka irin mutanen nan ne masu zuwa wurin Mami maula.
Dattijon nan ya dago ya kalli Ummi tabbas wannan fuskar in bazai manta ba ta matar Oga Khalifa ce baki ya bude yai ma Ummi magana "Hajiya Afrah kece nake gani kokuwa idanuwa na ne suke Man karya? " Ummi ta kalleshi aiko Malam Salisu ne wai dama haryanzu ya na nan? Allah sarki soho mai mutumci da karamci " Nice Malam Salisu ashe har yanzu kana nan? " Malam Salisu yai Murmushi "Eh ashe ana ganinku? ." Ummi tace " Muna nan ina wuni ya iyali ya yanayin rayuwa. " Malam Salisu ya numfasa aiko yanayin rayuwa ai sai ita " Iyali Alhamdulilah suwaye nan bayanki badai Islam bace waccan har ta girma haka ." ya tambaya yana nuna Islam " ashe zaka iya gane ta eh ita ce wannan kuma Farha ce na haife ta a Katsina suke nan yaran nawa ." Cewar Ummi tana nuna Farha. "Allah sarki rayuwa Allah ubangiji ya raya su ya daiyiba su Allah ya jikan maihaifin su. " Malam Salisu yace cike da tausayin su sannan kuma yace "Ku shigo mana. " Suka shiga Ummi na fadin "Ameen Malam Salisu mun gode. " sukuma su Islam da Farha duk suka gaishe shi ya amsa cike da farinciki yana ce ma Ummi bakomai ai gidansu sune, shikuwa wannan security sai kallon su yake ba dama ya hana su shiga saboda Malam Salisu ya basu damar shiga.
Suna shiga Farha kamar tai ihu saboda haduwar gidan Islam kau sai dungurar Farha take wai takama kanta, Gidan gaskiya ya hadu iya haduwa ita kanta Islam ido bude take kallon gidan kuma ga securities ko'ina . "Masha Allah wannan irin gida sai kace a tv " Inji Farha, Islam tai dariya sannan tace To bakauya Masha Allah ." Farha ta bude baki zatai magana kenan taga an wage Castle Gate wasu dangara dangaran Motoci all black ga bakin Glass sai Fara da wata Baka da alama su ake ma convoy Sun shigo a guje Sai sukai parking a gaban entrance na shiga gidan, Bodyguards duk suka fito daga motocin wasu suka bude ma wa inda ake ma convoy kofa.
Islam, Ummi, Farha haka suka saya suna kallo Kamar gunki ko ma suce zasu wuce su shiga ciki ba hanya securities ma baza su barsu harsai wanda suka shigo Sun wuce. To their surprise waza su gani ya fito daga Farar mota? Who else but the one and only Mr Fauzi!! Aiko Farha na ganin sa gashi yasha kyau danko Sky blue sweater and Black Jeans sai Black shade na Dior ta bude baki zatai ihu saboda sabagen rudewa Islam tai sauri ta rufe mata baki. Can kuma sai taga Amani da Muhsin Sun fito daga Black Car ai Farha suma ne kawai batayi ba.
Shikuwa Malam Salisu ganin su da yayi Sun saya ga zaton shi ko suna soron shiga cikin gidan koma sunce zasu shiga securities in gaban entrance baxa su barsu shiyasa kawai ya taso ya taho wurin dan ya shigar dasu cikin gidan . "Muje in shigar daku " Ummi tace mai "to. " kawai suka bishi sukuwa su Mr Fauzi harsun dade da shigewa. Farha tace ma Islam " Adda am I dreaming koko dagaske gani a cikin luxurious Mansion kuma ga Mr Fauzi da Amnah cikin gidan? " Islam ta amsa mata " Ni madai kamar a mafalki. "
Suna shiga gaban Ummi yayi mumunar faduwa saboda dattijuwar data Gani zaune a kan Royal chair cikin wani lace mai shegen sada da sarkar gold da yan hannu sai Medicate Glass tana karatun newspaper daga gani kasan yau tana Cikin farin ciki saboda favorite grandson dinta yazo yanzu haka su Mr Fauzi da Muhsin da Amnah suna dakin su zasu yi taking in shower kafin suzo suci abinci .
Mami ta dago daga karanta newspaper din da take ta Kalli fuskar da tafi sana a duniya wato Ummi da wasu yan mata guda biyu da alama grandchildren dinta ne.
Hurairaytu 🍸🍸🍸🍸🍸🍹🍹🍹
YOU ARE READING
Minister's Son
NonfiksiEvery human being has a destiny to fulfil. Birth signals the beginning of the journey towards the fulfillment of an individual's destiny. To a large extent , each individual, consciously or unconsciously determines the outcome of his or her d...
