Chapter 7

896 94 0
                                    

  Islam tana dawowa gida tai sallar magrib sannan ta fara karatun al Quran bayan ta gama sai ta roki Allah ta fadi bukatocinta , tana cikin addu'a sai ga Faty ta shigo ko sallama babu sai wani cika take tana basewa. Ke dalla mufuka in kin gama ki fito ana nemanki. Faty tafada tana hararar Islam tare da fita.

Islam ta shafe addu'a ta dago sai taga Faty har ta fita. Girgiza kanta kawai tai ta fito sakar Gidan ba tare da ta cire Lemon green hijab din dake jikinta. Tana fitowa taga Talatu da Ladingo sai Faty zaune gaban Talatu tana mata kitso su duka zaune a tabarma, ladingo kuma tana since Wake. Harara su duka suka bita dashi itadai ta share su tazo gabansu ta durkusa tace gani.

Hmm ni wallahi banga mi Mansir ya gani a keba har yake wani rawan jiki a kanki. Cewar Ladingo

Kedai bari ai Mansir yafi karfinta taimakon ta yayi da yace yana sonta mtswwww. Inji Talatu.

Nima dai nayi mamaki dana ga yanda yake rawan kai akan wannan ballagazar. Faty tace tana zabga mata harara.

Nifa ina ganin tausayinta yaji yaga tazama uwa guda a cikin gida babu wanda yace yana so. Ladingo tafada a tare su duka Suka bushe da dariya.

Suna cikin dariya saiga Mansir ya shigo, rigar yadi fari ke a jikinshi amma saboda dauda ta koma ash sai wando na jeans duk ya kode sai yellow slippers duk kasan ya cinye , kafa duk faso, hakoran kau kamar an zuba masu Jar kala. Sai warin hammata yake zubawa. Yana ganin Islam ya washe mata jajayen hakoransa yana fadin Matata har kin dawo daga asibitin?

Islam tai Mai banza sai Ladingo ce ta hauta da fada ke shegiya baki ji yana maki magana wai dan Kin samu yace yana son ki in banda abunki ba taimaka maki yayi ba da yace yana sonki !!!

Islam kau abun nasu ya soma bata haushi danma ba Farha bace da yanzu ta masu tas. Islam tace Ni ban taba ce mashi ya soni ba, sannan dan Allah ku ba dangi na bane ko iyayena da zaku ce dole sai na saurari shirmen sa , sannan ni dan Allah ku fada mashi ya rabu dani ance ba ayi ana dole? Tana gama fadar haka ta tashi ta shige daki don ita abun nasu ya fara isarta kawai basu bata ci balle sha kuma suba dangi ba daga makotaka amma ta yarda daya daga cikin jarabawar da Allah yai mata kennan kuma zata daure ta cinye . Tana ji suna ta zaginta tai banza dasu.

Ahhh what a great day ! Inji Mom suna shigowa first floor.

It was fun. Cewar Mr Fauzi suna hawan bene.

Yes it is , Bimbim Good night am really tired I wanna rest so yanzu in na shiga daki bazan sake fitowa ba sai kuma gobe in Allah ya kaimu.

OK Mom Allah ya kaimu. Yafada yana hugging nata can sukai breaking hug in yace Good night sannan ya haye bene.

Yana hawo third floor ya zauna palo sannan ya shiga cikin contact din wayarshi yana buga ma Amnah. Amnah dake kwance a kan gadon Muhsin daga gani sex suka gama taji wayarta na ringing.

God who is........Da sauri tai murmushi ganin Mr Fauzi sannan ta dauka Hello Bimbim.

Ina falo. kawai taji yace yai hanging Up. Dasauri ta tashi tasa kaya shiko Muhsin sai bacci yake abunshi. Tana zuwa palo taganshi zaune yana typing a wayar shi kirar iPhone 11 pro Max . Kusa dashi har ugunsu na gogar na juna , hannunta takai a kasumbarshi tana shafawa tace gani Bimbim.

Kallonta yai sai ya jawo wasu shopping bags guda biyar ya aje mata sannan ya mike yai shigewar sa daki.

Murmushi kawai tai ta bishi da kallo har ya shige daki sannan ta bude daya bayan daya. Daya kwallin Chocolate na  Amedei ,Diary Milk , Maultizers . Daya kuma Jewelry box tana budewa taga sarkar diamond da dankunne da zobe. Daya kuma Red dress ce designer na Dior ta karanta tag din taga 4.5 Million . Daya kuma Red heels ne cikin kwalli na Giorgio Armani . Daya kuma box ne tana budewa taga agogo ne na diamond na companin Gucci . Murmushi tai ta dauko wayarta ta mai SMS ta rubuta Thank you Bimbim I love you  .

Hurairaytu 🍸🍸🍸🍸🍸🍸🍹🍹🍹

Minister's Son Where stories live. Discover now