chapter 32

695 99 18
                                        


Tunda ta dawo gida take tunanin abunda ya faru sakanin ta da Mr Fauzi was he jealous of her ? Sai Kuma abunda Mom tafada mata ya Fara dawo mata kawai sai ta shiga girgiza kanta tana fadin " I should stay away from him , he's my boss and nothing else . Dole na nisance shi in naje office nasan aiki ya kaimu apart from that kuma babu komai sakanina da shi . Dole nai haka ko saboda mahaifiyarsa . "

Turo kofar akayi aka shigo , Ummi ce ta shigo ta zauna gefenta tace " what's bothering you ?" Murmushi Islam tayi tana kokarin boye damuwarta " Bakomai Ummi kawai Ina tunanin aiki ne ." Saida Ummi ta Dan jima tana nazarin Islam sannan tace " Miyasa baza ki fada min damuwarki ba ? "

" Bafa wani abun bane kawai harda Kuma stress ." Ita Allah yasani batason tada ma Ummi hankali dan idan taji abunda Mom tayi mata sai ta tada hankalinta .

" Kinsan kin canza sosai Islam ? Zaki iya tuno lokacin da duk wani damuwarki ni kike gayamawa haka nima ? I'm not only a mother to you but a friend also , I was always a friend and I'll always be . I was that friend that you confide in , lokacin baki da wata kawa . "

Kwantar da kafadarta Islam tayi a kan kafadan Ummi " eh Ummi ai kinsa I'm terrified about the idea of sharing my emotions with anyone else because I fear that they won't care enough , won't provide me with the advice I need . Sai kuma na tuno I have a friend that I have known for 23 years now . She's a great person with admirable traits , the kind of traits that one would look for in a friend and that friend is you Ummi , thank you for always being there for me thank you . "

Murmushi Ummi tayi " In banda abunki ai Uwa itace babba kawa , yanzu gaya mun masalarki . " Numfashi Islam ta sauke " Yau a office Maman Mr Fauzi tazo sai ta samemu Yana man murmushi sai na gaishe ta bata amsaba na fita na basu wurin ashe maybe wannan murmushin da yayi man upset her sai da tazo tafiya ta Fara maganganu marasa dadi harda cewa in rabu da danta otherwise she will become my worse nightmare . "

Ummi tace " And how do feel about it ? Zakiyi abunda tace ? "

" Ummi she's serious fa lokacin da take fadin haka of course mana zanyi abunda ta fada . "

" Sai kika tunomin da kaini , Allah ya jikan Mami nima haka ta dinga threatening Ina akan in rabu da Khalifa haka shima mahaifina Papa ya dinga threatening Khalifa ya rabu Dani Amma dayake soyayyar da muke ma juna is so strong and unbreakable we fought for our relationship , duk wa'inan threats in bai sa muka rabu da junanmu ba , Islam inaso kisani ba'a bakanta ma wani dan a farantawa wani , your happiness should be number one on your list . Kiyi duk abunda yake saki faran ciki indai bai saba ma Allah ba da mazansa , always do whatever makes you happy . Ba sai kin fada min ba nasan you're in love with Aslam Kuma I hope shima he feels the same for you . Kinsa kuwa wannan shine abunda Abby yake so ya gani ? Da ace Khalifa Dana da rai to da sai yafi kowa farinciki Dan lokacin da kina Baby yake cewa ke din ta Aslam ce Kuma baida wani buri daya wuce yaga kun auri junanku . "

" Kina tunanin zan bar burin nan na mahaifinku ya tafi a banza , mu samman yanzu da Allah ya kawo opportunity , ni kaina ina so ki aure Aslam in shine mafi alkhairi , Abby da ni da Mami Kai harda ma Dad believed you and Aslam are made for each other . So karki bari Sarah tayi nasara akanki , you're a strong woman Islam get up and fight for what you want . " Tana gama fadar haka ta fita Islam tabi bayanta da kallo tana nazarin abunda ta fada mata .

Karar shigowar message taji , daukar wayar tayi sai taga Mr Fauzi ne ashe , shiga message in tayi ,

Hello Islam , are you free ? I just wanna talk to you .

Replying inshi tayi ,

Yeah sure , at the office ?

Ba'a jima ba ya turo mata Reply ,

No , I will send a driver to pick you up if you don't mind .

Dan tunani tayi sai ta rubuta ,

Okay I'll be waiting . Sai ta rubuta mai address in insu .

Mom tunda ta koma gida hankalinta yake a tashe , what if her son has feelings for that trash ? Kasa zama tayi sai Kai da kawowa tana tunanin abunda zatayi Dan ta bata ma Islam suna a mutunci a idanuwan Mr Fauzi Dan ita yarinyar tasan for sure zata rabu da danta ko saboda rashin mutuncin da tayi mata dazu . Amnah ce ta shigo kallo daya zakayi mata kasan cewa ran ta a bace yake , " Mom you saw what happened earlier yanzu wane mataki zaki dauka ? "

Zama Mom tayi taja hannun Amnah ta zauna tace "kibar komai a hannuna. " Amnah tace " you better do something Mom otherwise Ni da kaina zanyi maganinta . "

" Karkiyi komai you might end up doing something stupid kibar komai a hannuna kinaji na Amnah ." Mikewa Amnah tayi ta fice tabar dakin , Kallon wayarta Mom tayi , wani murmushi ta saki sannan ta dauki wayarta ta nemo wata number ta shiga kira .

Farha dake kwance tana faman chatting taji karar door bell , mikewa tayi taje ta bude kofar . Delivery man in ya miko mata katon box in tare da paper da biro yace mata tai signing , karba tayi tai signing shikuma ya juya ya tafi . Katin dake jikin box ta bude tana karantawa " Hope you like the dress . " Sai taga Kuma sign na Mr Fauzi dakuma sunan shi a kasa .

"Wow yeeeyyyy Adda !!!" Tafada tana nufan hanyar dakin Islam harda dan gudunta , Islam dake saye gaban mirror tana shafa powder tasa wani light blue material ammai dinkin A shape taji farha ta banko kofar tana fadin " Adda kalla abunda Mr Fauzi ya aiko maki , yeeeyyyy can't wait to see what's inside . " Ajiye box in tayi kan gado ta mika ma Islam catin , bude catin Islam tayi ta karanta . Smiling tayi taje ta bude box in , zaro ido tayi tana kallon dress in itakuwa Farha sa hannu tayi ta ciro dress in tana hauda ta a jikinta tana " OMG Awwwwwn Dress in is so so so beautiful Kuma designer ne ."

Islam cike da mamaki take kallon dress in , Dan haduwa dress in ya hadu ga wani kalli kalli da dress in keyi amma ai dress in designer itakuwa Ina ita Ina sa designer ? " Farha ki maida dress cikin box in I can't accept this is too much ." Wani kallo Farha tai mata tace " haba Adda ya za ai kice a maida ai ba'a maida hannun kyauta baya munsan rigar nada sada sosai kuma siyan irin wa'inan rigunan albazaranci ne amma ai ya riga da ya baki . "

Karbar dress in tayi ta cire kayan jikinta tasa ka , sakin baki Farha tayi saboda bata taba ganin Islam tayi kyau haka , itakanta Islam da taga kanta a madubi sai data yaba kyan da tayi . "Adda wannan haduwa haka ai nasan Mr Fauzi can't take his eyes off ." Tafada tana daukar Islam picture, " Adda walahi kinyi kyau red never looked good ."

Makeup kit inta ta dauko ta zaunar da Islam tai mata simple makeup aiko ba karamin kyau tayi ba . Text message ya shigo wayarta sai taga Mr Fauzi ne yace mata driver in ya iso . Farha ta rakata har wurin mota driver ya fito ya bude mata ta shiga ya rufe motar yaja suka tafi . Ummi kuwa daman bata gida ta fita Islam ta Gaya mata tace zata fita Mr Fauzi na nemanta , itadai Ummi ta dauka ma ko aiki ne .

Zanyi updating zuwa gobe in Allah ya kaimu saboda wannan short chapter ne .

Minister's Son Where stories live. Discover now