Kasancewar ruwan da akayi jiya da dadare yasa garin yau da sanyi Alhamdulilah . Saboda sananin dadin yanayin garin yasa Islam tayi bacci sosai har ta kai ga ta tashi ba da wuri ba , "Inalillahi ." Ta fada da karfi saboda ganin lokacin da ta tashi 11:53 , a firgice ta fada toilet tana fitowa tasa kaya , ko breakfast bata saya yi ba ta fada mota sai Fauzi company .
Tana parking ta fito da sauri tana salati a cikin zuciyarta dan tasan yau mai saving inta wurin Mr Fauzi sai Allah . Yau kam zagi da cin mutunci ba irin Wanda ba zata sha ba , ita soro ma take ji kar ya koreta . Da fargaba haka ta tunkari kofar office insa tasa pin ta shiga tana zuwa second door ta danna doorbell taji shiru a zatonta ko bai nan , juyawa tayi ta fice office inta .
Tana zuwa office ta kirashi sai da Kiran ya kusan karewa sannan ya dauka , " Assalamualaikum sir good morning this is your PA talking to you ." Shiru taji ya manta , kamar ba zaiyi maganaba saiji tayi yace " come to my office Now !!! Yana gama fadar haka yai ending call in . Jiki ba kwari haka ta tunkari zuwa office inshi , tai knocking ya bata izinin shiga . Tana shiga ta iske shi cikin red suit da glass a idanuwanshi yana duba wasu takardu , kamshin turarensa da sanyin Ac ya hade wurin dadi kamar karta fita ji take Ina ma ace nan zataita zama .
"Sir gani ." Yi yayi kamar baiji taba ya cigaba da duba takardun, sai daya gama abunda yake ita kau tana nan saye kamar gunki sannan ya dago yace mata " Why were you late this morning ? " Rasa abun ce mai tayi kawai tace " I'm sorry sir ." Kulle idonsa yayi sannan ya bude , ya sa'ni ya tambayi mutum abu maimakon a bashi amsa sai a canza topic , baya son wannan abun kwakwata .
"I'm asking you why were you late this morning ? Don't make me repeat myself !!!" Tanajin yace haka tace " Sir I woke up late." Kallon agogon hannunshi yayi yace " Daga yau karki sake zuwa min makare I won't take your stupid excuses do I make myself clear ?"
" Yes sir Insha Allah ." Takardun da ya gama dubawa ya dauka ya jefo mata , Wayarsa taga ya shiga dannawa yace "Get out ." Dukawa tayi ta kwashe ta fice , tazo fita suka ci karo da Habeeb . Takardun suka zube kasa , ita ta duka ta kwashe takardun tana dagowa taga mutum na binta da harara , Habeeb yace "Are you blind ?" Dukar da kanta tayi ta zirziza kanta , Allah sarki Islam shine Wanda yaci karo da ita amma kunga shi yake tura mata laifin . Gaskiya mutanen wurin nan basu da mutunci , Adeel ne kawai mai mutunci da sanin darajar Dan Adam . " Mstwww " Habeeb yai saki ya shige office in , sannan itama ta kama hanyar shiga office inta .
Maiduguri ,
Yana sauka tasha ya samu masu mashina da yawa ya nufesu yace gidan Fauzi ya hau mashin da jikarshi sai gidan Fauzi .
Tun a bakin gate ya Fara kokonton anya nan su Islam suka zo to wai dama Kakarsu nada kudi haka ? Ya sallami mai mashin ya tunkari castle gate , wani soja yace " hehe where do you think you're going ? " Mansir yace " oga no turanci me ." Sojan ya gane mi Mansir ke nufi kasancewar sojan Yana jin hausa . Sojan yace " Ina zaka ne ?" Mansir ya washe hakoransa Yana fadin "Wurin matata ." Sojan ya daure kamar bai ta dariya ba yace " Matarka a nan Kuma ?" Yana ma Mansir kallo sama da kasa , Mansir yace " Eh matata ." Sojan yace " Kai dalla bace daga gurin nan ko in bata ma rai idiot ." Shi kansa yasan duk rashin jinsa baikai sojan nan ba ko shima kanshi yasani shiyasa bai mai gardama ba ya juya ya tafi.
Mansir sai daya samu wata inuwa ya zauna yana hangen gidan Fauzi yace " Ina nan ba inda zani ko da Islam ta fito zan ganta ban damu in kwana a nan ba ."
" Ummi zan fita walk ." Cewar Farha , itakuma Ummi tana saye a gaban kitchen Island tana chopping vegetables . " A dawo lafiya ." Amsar da Ummi ta bata kenan ta cigaba da abinda take . Airpod tasa a kunne ta tana jin wakar I can't stop dancing by Becky G . Taga inuwar mutum yan binta a baya , juyowar da zatayi taga Mansir ne .
Da sauri ya zakayo yazo gabanta Yana washe mata jajayen hakoran shi , " Fara ya kike Ina matata ?" Cike da mamaki take kallonshi " Mansir miya kawo ka nan ? Tayaya kasan muna nan ?" Mansir ya daure fuska jin abinda Farha tace " Kamarya miya kawo ni nan ! Matata na biyo ko zaki hanani ganinta ne ? " Farha itama ta daure kamar bata taba dariya ba " Kai Mallam dalla bari yiman sa'wa tunda ba haihuwata kayi ba !! Kuma ka shiga hankalinka inba haka yanzu zansa ai maka shegen duka a gurin nan !!!" Shiru Mansir yayi daukau ya San halin Farha sosai , ko da suna katsina kowa na soron shi amma Banda Farha , itadai Farha wata irin macece wadda bata da soro sau da yawa yaso ya Zane ta amma yan gidan sukan hanashi ita su turata daki amma dukda haka bata barin yimai rashin mutunci .

YOU ARE READING
Minister's Son
NonfiksiEvery human being has a destiny to fulfil. Birth signals the beginning of the journey towards the fulfillment of an individual's destiny. To a large extent , each individual, consciously or unconsciously determines the outcome of his or her d...