Chapter 18

986 101 6
                                        

 

Ummi ce cikin lace purple tayi kyau itama tafito daga dakinsu tana hanyar tafiya kitchen taji tayi karo da mutum, "auuu" cewar warda tayi karo da ita. Dagowar da Ummi zatai ta ga fuskar da bazata taba mantawa da ita ba a duniya, fuskar da ta lalata mata rayuwa fuskar da ta raba ita dasu Islam farinciki, Allah sarki rayuwa wasu mutanen suna mugunta kamar bazasu mutu ba.

Girgiza kanta Mom tashiga yi mi take gani haka? Badai Afrah bace no no it can't be her Afrah kuma? Can sai ta tuno dacewa an gaya mata tazo ita da shegun ya'yanta , to mi suka zo yi?  Shin Afrah bata dadaraba kenan? Lallai dole ta dau mumunan mataki akan Afrah. "Allah zai sareni da yarana daga shairin ki Sarah. " cewar Ummi kamar ta san abunda Sarah ke shirin yi masu.

"Mstwww wane shairi kuma kike magana munafuka, bayan kin kashe mijinki shine kika dawo ki amsa gado koh? "

Murmushi takaici Ummi tayi wannan wane irin zalinchi ne? Ka aikata abu kuma ka lika ma wani? Wanin ma wanda ka zalinta? Kai jama 'a. " Sarah ni ba yarinya bace shiyasa ni ba zan biye maki ba amma kisan wani abu guda daya duk abinda kika shuka shi zaki gurba, kuma ki gode ma Allah da har yanzu yaranki basu san asalin labarinmu ba I mean what happened 18 years back. " Dam!  Haka Mom taji gabanta ya fadi " Let me warm you for the last time if my children get to know about what happened 18years back especially Mr fauzi toh I won't spare you and your children kina jina? "

"what's going on here? " cewar Dad da shigowarsa kenan yaji hayani yan Mom amma baiji abunda tace ba kuma baiga face in warda take ma masifa ba, juyo wa Mom tayi jin Voice in Dad aikuwa shine tam yau tata ta kare tunda ga Dad ga Afrah waje daya .

" kayi ma matarka warning tafita harka ta what else does she need? She has already ruined my life and my childrens ." Umma ta fada ma Dad. Sai yanzu da Ummi ta kalleshi tayi magana sannan yaganta , jikinshi ba karamin sanyi yayi ba Allahu akbar yaushe raban shi daya sa ta a ido. Ya bude baki zaiyi magana kenan itakuma tabar wurin,  maida kallonsa yayi kan Mom dake faman jabza mai harara dan ta harbo jirginshi dama haryanzu yana nan da soyayar Afrah.



"Mami kinga yanda kikai kyau kuwa?  You look gorgeous wow Mami wait ina wayata " inji Islam tafada tana neman wayarta, smiling Mami tayi "Careless girl ki duba can dakinku mana maybe you left it there. " fita tayi zata je can dakinsu ta duba ,tazo fita kenan saiga Mom tazo shigowa, baya tayi danta ba Mom damar shigowa tunda ta girme ta wannan matar har Ummi ma ta girma . Mom sayawa tayi ta Kasa wucewa tana kallon Islam wannan yarinyar ko ba'a fada ba yarinyar Afrah ce hmmmm ta sauke numfashi tare da shigewa dakin.

Islam da tazo wucewa ta parlo mi zata gani Farha ce da Wani daga gani shine kanin celebrity in nan Muhsin right? Gasu nan zaune kowa sai danna wayarshi ga tv sai aiki take. Gyaran murya tayi su duka suka dago suna kallonta " am Farha have you seen my phone? "

Farha ta girgiza kanta alamun a'a shikuwa gogan ko da ya dago ya kalleta sai ya maida hankalinsa kan wayarshi . Tafiya tayi taje daki don duba wayar sai ta ganshi a kan madubi dauka tayi ta fito tai kitchen nan taga Ummi tare da matar Malam Salisu suna fira cookers na aiki , itama zama tayi dayake suna zaune a kan dinning table in kitchen in.


Mr Fauzi ne ya shigo dakin Mami lokacin daga Mom Sai Mami a dakin,  zuwa yayi yai hugging in Mom " kun iso lafiya Mom?" shafa sajensa tayi "Lafiya lau Aslam ya kake? " Breaking in hug in yayi tare da zuwa inda Mami take ya daura hannunshi a kan kafadarta " Mom ai kema kinsan ina lafiya Mami won't let anything happen to me. " yafada cikin thick accent inshi . Mami tai murmushi tace "mu tafi I think everything is ready mu ake jira a fara ."

Kowa ya hallara a baban falon wanda yasha decorations party irin na turawa ko daga ganin yanda sukai organising inshi, maza sunsha suit mata kuma gown wasu jumpsuit wa inda ba musulmai ba sunsa dangalalun riguna irin na party. Waiters suna yawo da tray na Cup in glass an sa champagne kowa a saye suna sha irin yanda turawa keyi. Mc yayi announcing shigowar celebrant , Da sauri Big h ya fara daukar su hoto tana saukowa daga bene ita da Mr fauzi ya sakala hannunshi cikin nata .

Nan kowa ya fara yi masu hoto , Islam da Farha na wuri daya shikuma Muhsin yana wuri daya da Amnah da wasu maza itadai Ummi tana kitchen suna kallon ta tv in kitchen  , Mom da Dad suna wuri daya da wasu business Men sai minister mace. Farha na ganin Mr fauzi ne yake saukowa bene da Mami nan ta fara fadin "oh my God Adda are you seeing what am seeing?  Mr fauzi ne fah. " tana kokarin zuwa wurinshi.

Da sauri Islam ta riko ta "Haba Farha to ko kince Zaki je wurin shi securities bazasu bari ba calm down okay  ."  dawo tayi ta nusu dan gaskiya Islam ta fada mata ko tace zataje securities bazasu bari ba.

Bayan Mami ta yanka cake anyi pictures sudai su Islam bayin Allah basu samu yin hoto da Mami ba saboda duk masu kudi wurin so bama zasu iya kusawa ba.  Mami ce ta hango Islam saya ta rike Cup na Glass da champagne a ciki tana kallon mutane she's not comfortable tasan bata saba zuwa inda manyan masu kudi suke ba, itakuma Farha tana video da wayarta. "Excuse me " tafada ma mutanen da take tare dasu ta tafi wurin su Islam.

" Islam zo nayi introducing inki da wani. " tafada tana riko hannun Islam nan suka fara tafiya itadai Farha ta bisu da kallo can kuma ta cigaba da video in da take.

Mr fauzi saye dasu Habeeb da Adeel sai wasu ssamari kowanen su rike da Cup na champagne suna hira shi Mr fauzi ya zura hannun daya cikin aljihun wadonsa dayan hannun kuma ya rike Cup sai securities zagaye dasu yan matan wurin kowa sai admiring insu yake. Nan Islam taga Mami na kokarin kaita, gabanta taji ya fadi badai shi za ayiwa introducing inta ba? Tab wannan arrogant jerk in.


Minister's Son Where stories live. Discover now