Chapter 20

903 104 16
                                        

Cikin fushi ya Mike yama manta da Box in yabar library in, hannunshi rike da hoton Khalifa. Yana bukatar bayani, dakin Mami ya nufa straight tare da fadawa dakin kai saye  . Mami dake shirin kwanciya yanzu ta gama Shafa'i da wutir tana ninke sallaya taga Aslam ya fado dakin ta idanuwanshi taf da kwalla da alamu kuka ya gama yi, saye yai mata yama kasa furta komai Sai hoton da yake kokarin nuna mata.

Da kyar ya fusgo magana " who's this man? " Wani irin mumunar faduwar gaba taji gabanta yayi, tayaya ya gano da Wannan hoton?  Shin yasan komai? yanzu itadai Allah yasani bata shirya fada mai komai ba saboda sanin halinshi da tayi in yai fushi kulle idanuwa yake ya zuba rashin mutunci kuma bai ganin kan kowa da gashi.  To indai ya gano asalin tarihin family in nan ai sai ya sa sun gane kurun su saboda shi duk inda gaskiya take nan yake,  bai damu da kai dan uwansa bane kai in har ya gano gaskiya har Mom sai yayi punishing inta yanda ya kamata.

Itakan ta bata jin zai iya sassauta mata, ita dai gaskiya soron shi take. Dama tasan wata rana dole asirinsu ya tonu, tasan wata rana dole a samu wanda zai samunma Khalifa justice. Kuma tasan in har Aslam ya gano gaskiya zai samun ma Khalifa justice, kuka ta fashe dashi, hannunshi yakai a kafadarta ya jawo ta ya rungume ta .  Duk da yana cikin fushi da ita she's still his Mami bazai iya jure ganin sohowa kamarta ba tana kuka haka " Shhhhh Mami ya isa haka kibar kuka kinji. " yafada yana shafa mata baya alamun lallashi .

" Haba Mami banace kibar kuka ba I just wanna know , Did I re-open your old wounds? " Yace bayan yayi breaking hug in, idanuwa ya zuba mata yana jiran amsa.

Saida kukan tayi ta dago jajayen idanuwanta ta zuba mai " Aslam Shidin dana ne he's your father's twin brother......" Cike da mamaki ya kase ta " Amma Mami miyasa........." Itama da sauri ta kase shi " Hear me out, shidin Uncle inka ne amma he's late tun 23Years back " Kuka ne yadan sake kufce mata , maida kukan tai taci gaba " Amma bashi da iyali, shi baiyi aure ba accident yai ya rasu. "

Wasu hawaye ne suka zubo mai inama ace uncle inshi nada iyali daya nuna masu so daya jawo yan uwanshi kusa dashi sunyi rayuwa tare cikin hadin kai , kara hugging in Mami yai yana lallashin ta " Dan Allah Mami stop crying amma miyasa Baku gayamana ba nida Muhsin? "

Mami kau ji tayi inama ace Duk abubuwan dasu ka faru bai faru ba, ita yanzu gashi nan ta sake yin wani laifin sai yaushe zata bar yi ma Khalifa ba daidai ba?  Wani kuka mai cin rai ta fashe dashi. Shiko Mr fauzi ganin haka yasa ya mike ya dauko allura yai mata nan wani bacci mai nauyi yai awon gaba da ita.

Jikinshi yayi matukar yin sanyi haka ya fito daga dakin ya wuce dakinshi, hoton ya zuba ma idanuwa yacigaba da kallon Khalifa , a daren rannan sam baiyi bacci ba haka ya raya daren yai sallah kuma yakai ma Allah kukan sa na Allah ya jikan Khalifa yasa ya huta .

"Alhamdulilahil lazi ahayana ba'ada ma amatana wa ilaihil nushur. "  Tafada tana kallon window safiya mai sanyi bata San maiyasa ba ta tashi da wani irin farin ciki. Zaro idanuwa ta fara yi ganin duk sun riga ta tashi, Farha ce tafi to daga toilet daga ita sai towel daga gani wanka tayi . " Lafiya kike ta mazurai saika ce maiya Adda? " Harara ta wasa mata " mazurai kuma? "

" Eh mana gashi you over slept fadi man gaskiya Adda kodai duk murna ce tasa ki haka. "

" Murna nami kuma? "

Wani shu'unin murmushi Farha tayi sannan tace " Murna mana yesterday at the party I heard Mami said kizo ta hada ki da wani so who's the lucky guy? " Juya idanuwanta tayi sannan ta mike daga kan gado tana nufar kofar toilet " Uwar gulma ke mi zai hana ki gaya mun labarin saurayin nan naki. "

Zaro idanuwa Farha tayi "Wane saurayi kike cewa Hajiya Islam. "

" Wannan dan gayun kanin celebrity innan wanna arrogant jerk innan. "

" Oh wai Muhsin kike cewa ai Muhsin ba saurayi na bane wannan yafi karfina Adda kinsan su yan gayun nan  sai suyi tama mutunci suna kiranka sunaye wanda zaka dauka kamar so na soyaya suke ma amma ba haka suke nufi ba kinsan tashin Us. "

" Au ashe dai kin fara yin hankali. " Cewar Islam tana shigewa toilet itakuwa Farha baki wangale ta saya tana kallonta har ta shige toilet .

Da wani irin ciwon kai ta tashi, dafe kanta tayi tashiga toilet tayi brush sannan tafito ta kama hanyar fita daga dakin, gaban kofar dakinshi ta saya tana dafe kanta saboda wani irin ciwo yake mata  . Murda handle in tayi ta shiga, zaune ta ganshi cikin farar singlet da farin 3 quarter sai Bluetooth dake sanye a kunnenshi yana typing a Max Book.

Dafa shi yaji anyi, dago wa yayi ya kalleta "Good morning. " kawai yace mata yaci gaba da typing. Tasan sarai fushi yake da ita " Am sorry I have my reasons ." tace hawaye na zubo mata dan ita tama rasa ya zata yi da rayuwar ta ga karyar da taimai she's feeling guilty tama rasa ya zatayi. Mikewa yayi ya zaunar da ita yasa hannu ya share mata hawaye " Ni banaso ina ganin hawayen ki Mami ya  isa haka. " Mikewa yayi zai bar wurin ta ruko mai hannu " Dama inaso nayi magana dakai. "

Zama yayi kan gado yace " Am all ears. "

" Akwai wata yarinya dana keso kayi employing a company inka inaso tayi ma aiki a masayin PA inka Dan Allah ."

Duba time yayi a iWatch dake daure a hannunshi " Okay abama Adeel takardunta ni I have a flight to caught up in 30 minutes. " mikewa tayi tazo gabanshi ta shafa fuskar shi " Zaka tafi saboda kana fushi? Duk sanda kazo nan ba haka kake tafiya ba, in zaka tafi kana fadin " Mami I will be leaving in two days. Amma yanzu da banzo nan ba da saidai na ganka kazo yi man bankwana? Haba Aslam dan Allah kabar fushin nan. "

Mikewa yayi ya rike hannunta " Mami is better if I leave. " itama rike hannunshi tayi " To shikenan tunda haka kake so nasan in ka tafi zaka rage fushi dani shiyasa kake son tafiya ko? " Daga kanshi yayi alamun eh " It's okay I wish you a safe flight don't forget to call me when you arrive. "

"Okay Mami. " yafada yana hugging inta.

Wallahi saboda comments nayi updating, your comments keeps me going.

Hurairaytu 🍹🍹🍹🍸🍸🍸🍸

Minister's Son Where stories live. Discover now