Chapter 15

882 91 13
                                    

Fitowar ta daga wanka kenan da rigar wanka a jikinta , Muhsin ya turo kofar tare da shigowa . Sayawa tayi tana kallon shi, shima haka, shagwabe fuska tayi tare da rumgume shi tana mai shagwaba ,bakinshi yakai dai dai kunnenta yace "I'm sorry Amnah " tare da daukarta cak ya kwantar da ita a gado. Hannun ya sa ya Cire rigar wankan dake jikinta, kiss ya fara yi mata a cibiya har zuwa bakinta.......

Washe Gari.

Tura kofar dakin tayi a hankali ta shigo daga kitchen take tana taya masu aiki yin abinci dan ita gwanar aiki ce. Farha dake faman sa siket wanda ya Kasa wuce wa ya maseta saboda ta kara hips ta marairaice fuska tace " Adda badai kiba nake ba? " Smiling tayi tare da karasowa cikin dakin ta zauna bakin gado " Haba Farha to in ma kinyi kiba Sai mi? You look sexy autar Ummi " ta fada tare da kashe mata ido daya. Pillow Farha ta Dauka tare da jefama Islam wadda take mata dariya tace " Adda aure zakiyi fa haka zaki ma mijinki? "

Dariyar da take yi ya bace jin abinda Farha tace, take fuskarta ta koma ta damuwa . Farha ta lura yadda mood in Islam ya canza jin ta ambaci auren da zatayi da sauri ta zauna kusa da Islam tare da riko hannunta tana fadin " Adda you are making a big decision , aure ba abun wasa bane think twice dan Allah, We all love you and bamaso muganki cikin damuwa so please Adda you don't have to marry him if you don't want to dan Allah Adda don't force yourself please. "

Kallonta Islam ta saya tana yi dole ne ta boye damuwar ta, murmushi ta kakalo " kinji ki da wani zance waye yace maki banason Alhaji Salisu? Auren soyayya zamuyi kinji ko? " Girgiza kanta Farha tayi alaman bata gamsu ba " Ni ban yarda dake ba, kawai dai kin fada ne. " Ummi ce ta turo kofar ta shigo tare da sallama a bakinta. Amsa mata sukayi, Farha ta mike ta ida sa siket inta.

"Tabb aure kuma? " Ladingo da Talatu suka tambaya a tare . "Eh Auren ta nakeso inyi kuma sai aure ta dankau Islam tawa ce nima haka nata ne. " Inji Mansir da ke zaune a kan dakalin kofar dakinsu, Talatu da Ladingo da Faty kuma suna zaune a kan tabarma itakuma Maman Aisha tana zaune a bakin murhu tana iza wuta.

Ladingo tace "Yanzu kai Mansir wannan mai kama da farar aljannu zaka aura ? In banda abinka ai kafi karfinta su dako asali basu dashi. " Maman Aisha ce tai saurin cewa " A'a suna fa da asali Ladingo yanzu haka sun tafi maiduguri wurin dangin su batun maganar auren Islam. " Ba Mansir kadai ya razana ba harda faty, Ladingo da Talatu dan a cewar su bata da mai sonta. Talatu ta tabe baki da fadin " Aikin banza yanzu haka wani bakauye ta samu mara ilimi dan nidai nasan wayenyen mutum bazai auri karuwa ba. " Faty itama ta karba " Aiko dai ai saidai bakauye kuma Jahili zai iya auren Islam baku ga shiyasa basu gayama na ba ? Boye boye kawai suke " can ta Kalli Mansir tace " Yaya Mansir kafi karfin Islam wannan kazamar ai Sai kazami ka bari cikin abokai na gasu nan hadadu sai ka zaba. " Cewar Faty cike da bakin cikin Islam 😂.

Mansir ya mike yana kunfar baki yace " Islam tawa ce ba'ayi wani da namiji ba dazai aure ta Sai ni kuma bawani namiji daya isa ya kwace man ita ." binshi da kallo su duka sukayi ba warda ta iya furta kalma daya dan sun san Mansir yanzu da wata tayi magana ko zagin Islam to mutum zai sha duka tunda an bata mai rai.

" Mami am going out ." yafada yana shigowa dakin Mami, dagowa tayi daga karatun newspaper da take tare da sakar mashi murmushi tace " Where are you going to? Yanzu baza ka spending time inka dani ba Fauzi? Common today is Thursday so please spend your time with me ." zauna wa yayi kusa da ita tare da hauda hannun shi kan kafadarta sai zuma kamshi yake yasa white kaftan saikau ya fito a farin balaraben shi " Mami am sorry I have to leave but in na dawo zamuyi fira. " kallonshi kawai Mami take dan yana tuno mata da Khalifa, " Adawo lafiya. " tare yimai peck a goshi. Mikewa yayi shima yayi mata peck a kumatu sannan yace Ameen ya fice.

Fitarshi kenan Farha tashigo dakin ba tare da ta ganshi ba, zaunawa tayi kusa da Mami " Good Morning Mami . " Amsa mata tayi fuska a sake ,tafi sabawa da Islam " How was your night? " Farha ta dukar da kanta tace " It was cool. " Mami ta bude wani page na newspaper datake karanta tace " That's nice ."

Shiru ne ya kewaye palon bayan yan mintutika Farha tace " Mami dama da wata magana nazo. " Daka gani kasan she's nervous. " Am all ears. " Mami tafada still her eyes were on the newspaper she was reading.

" Dama maganar auren Adda ne the truth is she never liked that Man she is just pretending besides the fact that nayi rashin lafiya ya biya kudin operation ina kuma we don't have the money to pay him back that's why she decided to accept his proposal .Mami she's your granddaughter you like what's best for her right? " kada kanta Mami tayi alamum eh Sai Farha tacigaba da magana " To Mami pleasa stop wannan auren dan Allah for her happiness. "

Sayawa Mami tayi tana tunani dan tasa anyi bincike akan Alhaji Sani kuma in bazata manta ba soho ne, itama tanasan farincikin Islam dan shikadai Islam ke bukada harda su Farha kuma Khalifa ma zaiji dadi maybe ya yafe mata. Ita yanzu so take ta kyautata ma iyalin Khalifa ko Allah zai yafe mata abunda tai ma Khalifa inta, wasu hawaye suka zubo saboda batasan da zubowar su ba, hannun takai ta share sannan ta Kalli Farha tayi mata murmushi ta mike ta wuce dakinta, itakau Farha da kallon tabi Mami mi Mami ke nufi kenan? Ta yarda?

"Mi aure kuma? Zaka kara aure kace fa? "Tafada cike da bala'i shiko Yana zaune akan kujera ya zuba ma dankareriyar tv ido ya mata banza tun sanda yace mata aure zai kara. "Alhaji dakai nake magana fa aure fa kace to wallahi badai a gidan nan ba dankau nayi ma alkawali in har ka sake aure to Sai na kashe matar. " dukda haka bai kalle ta ba danshi yayi alkawali sai ya auri Islam ba gudu ba ja da baya. Itakau matar tashi Tana gama fadar haka tai dakinta.

Dan Allah kuyi hakuri Baku jini ba kwana biyu.

Minister's Son Where stories live. Discover now