Chapter 29

779 94 6
                                    

Tana jin mosin mutum tai saurin zuwa inda Mami take ta sugunna tana kukan munafinci , Mr Fauzi yana shigowa yaga yanda Mom keta kuka ga Mami kwance sai bacci take . Karasowa yayi gaban Mom ya mikar da ita Yana fadin " Subahanallah What's wrong with you Mom ?" Girgiza kanta ta shiga yi tana kuka tace " Aslam Mami ta tafi, ta mutu ." Sauke hannunshi yayi dake akan kafadadunta ya kalli Mami sannan ya maido da kallon shi kanta , sai da yayi kusan minti uku Yana kallon Mom sannan yace " Mami bacci takeyi ba mutuwa tayi ba , Mom Dan Allah kibar kuka ." Yafada Yana share mata hawaye , Mom tace " A'a Bimbim , Mami ta mut...... " Ai bai bari ta karasa abunda take son fada ba yabar share mata hawaye yace " Mom Mami bata mutu ba bacci takeyi ."

Mom tace " Wai miyasa baza ka yarda da abunda nake fada ma ? A gabana ta mut....." Bai San lokacin da ya daga mata murya ba " Will you keep quiet ? Nace maki bacci take !!!" A razane Mom ta kalleshi , shi kanshi sai bayan ya gama fadar magana yai realizing Wanda yai mu magana haka . Lumshe lemon green eyes inshi yayi Yana dana sanin abunda yayi , hauda hannuwanshi yayi a kan kafadadunta Yana fadin " I'm so sorry Mom , I didn't mean to raise my voice on you . Dan Allah ki yafe min ." Dukda taji zafin abunda yai mata hakan bai hanata cewa " Ko da ace baka nemi gafara ba ni na yafe maka Bimbim , na gane duk cikin so kayi hakan . Allah yayi albarka stay blessed Son ." Murmushi yayi ya rumgume ta Yana fadin " I love you more than anything in this world Mom , you're my first love ." Sosai maganarshi tayi mata dadi shiyasa itama tai hugging inshi sosai . Bayan yayi breaking hug in yace " Kije ki huta ni zan zauna a nan ." Murmushi tayi mai sannan ta fice , shikuma Kara lullube Mami yayi sannan yai mata peck a goshinta sai ya zauna kan kujera Yana kallonta tana ta baccinta , anashi  zatonshi bacci take .

Mom na zuwa dakinta ta zauna tana murmushin mugunta tace " Ai gara da kika mutu Mami , yau saboda ke abunda nafi so a duniyarnan ya daga min murya . Duk Wanda Aslam yakeso sosai sai na tabbatar dana aika shi ko ita lahira saboda Ina soron kar yafi sonta fiye Dani . Mami  you deserve to die Kuma kin mutu saboda kina neman ki lalata min abunda na dade Ina ginawa shekara da shekaru . Sannan Kuma Aslam Yana sonki sosai Kila ma yafi sonki fiye Dani , shiyasa kika cancanci mutuwa ." Wayarta ta dauka ta shiga Kiran Muhsin .

Muhsin da Amnah ne zaune a daki suna cin popcorn suna kallo a Netflix , wayar Muhsin ya dauki kara ya duba caller ID in yaga Mom saiya dauka " Muhsin nasan kana tare da Amnah kuzo dakin Mami yanzu ." Tana gama fadar haka tai hanging up , Muhsin yace ma Amnah " Muje dakin Mami Mom na kira." Yafada Yana mikewa itama mikewar tayi suka fito .

Bada jimawa ba saiga Doctor Umar ya shigo , Mr Fauzi ya sashi ya duba condition in Mami . Bayan ya dubata ya gane sam babu rai a gangar jikinta yace ma Mr Fauzi " Allah daya bamu ita ya karbe Mr Fauzi , Mami has answered Allah's call , Allah ya rahama mata amma tadan jima da rasuwa ba bacci take ba ." Ji yayi kafuwanshi bazasu iya daukar shi ba , zama yayi akan royal bed in da take ya kalleta Yana gani Doctor Umar ya lulube ta daga kafuwanta har saman Kai da farin blanket , sam ji yayi ya kasa magana , kenan ashe gaskiya Mom ta fada dazu ? Doctor Umar ya dafa kafadarshi yace " Ni zan jira a palo ." Yazo fita kenan saiga Muhsin da Amnah sun shigo , Doctor Umar yace " Allah ya jikan Mami ya rahama mata , Allah ya baku hakurin rashinta ." Muhsin yadan firgita itakuwa Amnah kuka ta fashe dashi ta juya tai dakinta , Muhsin karasawa inda take yayi ya kalli gawarta sannan ya Kalli yayanshi dayai shiru Yana kallon gawar . Ko ba'a fada ba kasancewa kukan zuciya Mr Fauzi yake wanda yafi komai ciwo , Muhsin yaji tausayin yayanshi Dan yasan duk yafisu jin mutuwarta danko Dad dake danta baxai ji mutuwarta ba kamar Mr Fauzi . Zama yayi gefenshi ya dafa kafadarshi yana fadin " Nasan you're in pain right now , Inaso kasan cewa Mami is in a better place Insha Allah , As a well spent days brings happy sleep , so a life well spent brings happy death ."

Dad ne ya turo kofa Mom na biye dashi a baya , Cak Dad ya saya ganin yanda aka lulube Mami yasan mi hakan ke nufi , Muhsin ne yace " Dad Mami has kicked the bucket , I'm sorry for your lost ." Zuwa yayi gaban gawar tata ya bude face inta saiga hawaye , daurewa yayi ya share hawayen yai mata peck a goshinta sannan yai mata addu'a  . Mr Fauzi ma yayi mata addu'a sai yayi mata peck a goshinta da kumatu , haka shima Muhsin sannan Mr Fauzi ya lulube mata fuska .

Minister's Son Where stories live. Discover now