CHAPTER ONE: HOLY MONTH

1.7K 72 9
                                    

Zaune suke a katon parlorn su biyu. Wani tsohone akalla zaiyi shekara tamanin fari ne tas kallan farko zakasan bafulatani ne na asali. Gyara zaman sa yayi kan kujerar sannan ya kalla wanda ke zaune a kasa

 Gyara zaman sa yayi kan kujerar sannan ya kalla wanda ke zaune a kasa

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Yace "Masha Allah sai yanzu kuka karasa sallar? Eh KAWU. Dama inaso in ma magana ne akan wannan zaman dakake ba mata.

Aliyu yanzu idan ka kirga kusan shekara biyu kenan da rasuwar mai dakinka dasu yaran. Ai ko takaba kake ka isa karasawa."

Dago kansa yayi ya kalla kakan nasa kamin yace "kawu takaba sai kuma kace macce?"

"To idan ba haka ba meyene ya hanaka sakeyin wani auran? Badai mata suka kare a duniya ba bale kace babu matar aure.

Aliyu yanzu banida wani guri daya wuce inga ka sake wani aure bana san ganinka zaune galala haka.

Babu wacce kakeso muje a tambaya maka auranta?"

Girgiza kansa yayi yace "ko daya babu."

"To kana nufin a haka zaka mutu ba aure tunda ita maidakin taka ya rigaka gidan gaskiya kaine ga bature ko? Wato kayi auran zobe."

"KAWU ba haka bane dan Allah kayi hakuri kuyi yadda ya kamata" yafada dan san faran tawa kakan nasa rai.

Washe hakora yayi alamun dama abinda yakeson yaji kenan kamin yace "to shikenan Allah yayi maka albarka tashi ka kira mun iyayenka dake waje."

SU WAYE MUKA GANI A NAN?

Cikaken sunan sa shine Aliyu Sulaiman Modibbo. Jika na farko a zuri'ar Modibbo family.

Shine sanyin idaniyar kakan nasa wanda suke kirada KAWU. Cikin yaya hamsin da bakwai da Allah ya bawa Modibbo Aliyu shine jikansa na farko kuma dandan yaronsa na farin mai suna Sulaiman.

Aliyu got married upon his mother's wish to his cousin from his mothers side. Auransu da Juwairiyya za'a iya cewa bashida maraba da babu.

Ikon Allah ne ya kaddara he would have children with her. Although Modibbo nasane da zaman doya da manjan da jikansa suke da matar sa ko sau daya bai taba nuna cewa ya san hakan ba.

Aliyu is very close to his grandfather because tun yana three years old ya koma hannun modibbo.

Tare suke zama a parlorn idan modibbo zaije gona dashi ake zuwa idan inda garken shanukansa da kuma bisashe suke da Aliyu ake zuwa.

Har tazama duk inda kaga modibbo sai kaga Aliyu he practically raised him. Lokacinda aka daura auran modibbo da juwairiyya modibbo bashida lafiya sai bayan an gama aka sanar dashi.

Ranar saida aka hau sama aka fado dashi kamin aka samu ya bada blessings dinsa amma tun daga ranar ya sanya musu ido. Su goma sha bakwai suke ga iyayensu.

Maza bakwai sai mata su goma. Idan kasan modibbo lokacinda yake yaronsa dakaga Aliyu zaka dauka modibbo ne aka ragewa shekaru.

Kasancewar Aliyu din sunan baban modibbo ne dashi ya sanya ake masa alkunya da lakanin Alhaji. Allah yayiwa Aliyu kirar majiya karfi dan shi din irin mazannan ne da ake yiwa lakani da karfafan maza iyayenshi maza sukan kirashi da mai karfi ko su kirashi da giant.

DAN GIDAN MODIBBO Where stories live. Discover now