CHAPTER FORTY: CHAOS

511 42 16
                                    

Tare suka fita suka shiga mota hannunta ya rike da nashi yana wasa da zoben hannunta dayan hannun nasa kuwa wayace ya rike a kunne.

Kallansa tayi saidai batace komai ba ta share. Sakin hannunta yayi ya rike kafadarta da hannun nasa ya kalleta ya dage mata gira.

Dauke kanta tayi tafara kallan waje she feels like this man is hiding something from her. Parking sukayi cikin godan KAWU.

Bata tsaya jiran saba ta fita tayi tafiyarta zuwa gidan mama. Tana shiga gidan tace Masha Allah wankin angone amma kamar gurinda za'ayi wata hadaddar walima.

Aunts dinsa da uncles dinsa dake gurin taje ta gaida sannan ta shiga ciki haduwa tayi da baba akan hanya ta duka ta gaidashi.

Yana murmushi ya amsa h sannan yace ayita hakuri haka aure yake. Bayan ya wuce ta shiga ciki ta gaida mama.

Aisha shine kikayi tafiyarki daga dawowar ku? Aa wlh mama kayana naje dauka sai kawai na shirya daga gida.

To shikenan yanzu za'a fara ku nemi guri ku zauna tafada tana kallan aisha with guilty eyes. Mikewa tayi ta fita ta zaune a inda taga sauran.

Suna zaune suna kallo aka fito da angon bayan an gama nadashi. Bayan ya zauna KAWU ya shigo ya zauna.

Tashi angon yayi yaje ya zauna a kasa kan tabarmar dake gaban KAWU. Hannunsa ya rike yayi masa addua sannan yayi masa nasiha.

Yace tashi ka koma gurin zamanka. Yan uwa daya bayan daya aka fara zuwa ana sanya mishi na chefane a aljihun babbar rigarsa.

Mikewa su aisha sukayi suka sanya mishi a aljihun suka koma suka zauna. A nan fa aka fara kida.

Wakar sangaya aka sanya musu daidai lokacinda KAWU ya mike zai wuce mufeeda da wata cousin dinsu suka rikoshi.

Tsakiyar filin suka kaishi suka fara rawa. Kallanshi mufeeda tayi tabi sautin daidai inda matar ke cewa "yar baba da KAWU yar dangice"

Murmushi yayi ya rike hannunta yana nunata yana cewa ke ko? Janye hannun mufeeda tayi ta rike KAWU tana mishi baitinta.

Ai ba komai duk matanane ku yafada lokacinda wakar ta kare. Chasu sukayi har akayi kiran sallah magrib sannan mutane suka dan rage sukaje sallah.

Aisha ce zaune tana tinanin ya zata koma gida ta chanja ma dinner cause taga alamun cewa Alhaji ba shida niyyar dagawa sai bayan isha ita kuma dolene tayi make up.

Fatima ce ta fito rikeda baby tace aisha baki tafi gida ba? Eh wlh waishi nake jira amma naga alamar sai bayan isha zai tafi.

To muje mana saimu ajiyeki a gida tunda kema sai kinyi make up. Bin Fatima tayi suka shiga motar.

Gaisawa sukayi da Mudassir sannan ya tada motar ganin yakama hanyar arkilla yasa tace aa fa mun dawo nan tafawa balewa.

Sauri yayi yay u-turn kamin ya karasa wuceshi yace ashe harkun koma. Eh wlh dawowar nan da mukayi muka koma chan.

A gate suka tsaya sukayi horn fitowa daya daga cikin masu gadin yayi ya kalla motar. Jidda glass din bayan inda take tayi tai mishi hannu.

Matsawa yayi kamin ya karasa kaiwa ya hangota yace sorry hajiya we had no idea it was you.

Da saurinsa kamar zaisha kaye yabar gurin suka bude gate din suka shiga. Parking yayi a entrance din ta fito.

Kallan wayarta tayi ta kalla fatima tace anya you will make it time? Naga har eight ta kusa kuma sai kun koma har bado won't you be late?

Karki damu it's good to be fashionably late. Murmushi tayi sannan tayi musu godiya ta shige cikin gida.

Tana shiga ta cire kayanta ta sake alwala sannan ta sanya hijab taje ta budewa mai makeup din kofa ta shigo.

DAN GIDAN MODIBBO Where stories live. Discover now