CHAPTER SEVENTEEN: OLD HOUSE

580 50 8
                                    

Tana shiga dakinta kwantawa tayi kan gado hawaye na bin idanta. She tries so hard to be nice to him to get along with him. Why does he keep pushing her away? He is the first man she ever pursued why? Because he was her husband and she saw no shame in it. Who knew he would still be deeply in love with a dead woman. For the first time she thought anci amanarta hadata auren nan dashi. Why? Because dama ace wacce yakeso was alive it would have been a totally different thing but it had to be worst. He was still in love with a woman who was dead.

Yes taga picture din tsohuwar matar shi and ba alphari ba ko kyan banzan ta fita bare ayi maganar jiki. Why is he so infatuated with a dead woman? Dame ta fita? Kyan hali ta fita dashi ko meye? That he is not ready to give her a chance. Danne kanta tayi da pillow as she thought back to their fight. Batasan abinda ya sata jin takaici ba amma she is right. Duk wanda ya shigo gidan ya fita cewa za'ayi ta magance shi ta maidashi mijin hajiya har abinci shi yakeyi. Ba za'ayi tinanin dan ra'ayin kansa ya shiga ba.

Meanwhile Alhaji kuwa bin inda ta wuce da kallo yayi. He didn't mean to offend her sannan koda wasa bai taba comparing dinta to Jawaheer ba. Why? Sabida yasan they are two different people with different personalities and different home upbringing. Aisha macce ce san kowa kin wanda ya rasa. She is nice and innocent but he needs time to adjust to her kindness. The words like love and kindness never existed in his first marriage. This is his first time experiencing it. But he never thought he would hurt her in the long run. Kiran numberta yayi ya jira har tayi picking up.

Aisha kuwa tana jin kukan wayar taki ta daga. Jin kawai tayi ana knocking a kofar dakin nata kara kwancinta tayi taki ta amsa. Jin kawai tayi an bude kofar hadeda sallama. Karasawa tayi bakin gadon yayi tsaye yana kallanta kamin yayi murmushi yace dan kina fushi dani shi zai hanaki amsa sallama na? Chan tayi tinani taga hakan ba daidai bane ta amsa sallamar. Zauna muyi magana kinji ganin batada niyyar zama yasashi zaunarda ita.

Kallanta yayi ita kuma ta maida kai kasa. Fushi kike dani? Aa tafada tana gyara zamanta. To me yasa dana kira wayanki baki daga ba kuma kinaji Ina knocking kika kyale? Banji ba tafada. Am sorry about what happened in the kitchen earlier. Aisha I have been used to that type of life throughout my first marriage. I need you to give me sometime to adjust. It's just a matter of time and things flow naturally.

Kallansa tayi how come yau itace namiji ke bawa hankuri namijin ma wai mijinta? Someone a lot older than her. Ba komai it's alright I was caught up in the heat of the moment. Kallanta yayi for a few seconds kamin yace are we good? Nodding tayi sannan tace eh. To ai shikenan ya fada sannan ya fice daga dakin. Harya kulle kofa ta tuna request din Nabeela tsayawa tayi tana tunanin should she ask him koya? Mikewa tayi ta bude kofar ta kulle. Turus tayi ganin mutum zaune a parlon ta yana kallo.

Karemishi kallo tayi tana tinani a ranta he is very fair farin yayi yawa. Quite alright suna bala'in kama da kakansa amma yafi modibbo kyau. I probably look like a teddy bear standing next to him. Shaking thoughts din away tayi sannan ta karasa ta zauna kujerar gefensa dan yana kan kujerar dake facing TV. Kamin ta buda baki yayi pausing ya juyo ya bata attention dinsa. Am dazu Nabeela tazo kuma tazo tareda masu aikin da umma ta bada azo dasu. Su ukkune sukazo the other one is elderly so she will h-ba komai sun miki?

Eh sunyi. To shikenan Allah yasa shi yafi zama alkhairi. Da muka dawo ba kije kin gaida gida ba ko? Eh ban tafi ba. Dama inaso ne to ask your permission banda gobe birthday din Nabeela inaso zanje. A ina za'ayi? A gidan anti khadi ko fati one of the am not sure daganan sai inje inga umma. Okay you can go amma goben ma zaki iya tafiya kiga umma. Smiling tayi sannan tace okay nagode.

Washegari kuwa tunda wayewar safiya tahada breakfast tana sanyeda bakin yoga pants da farar hoodie batareda ta daura dankwali ba tabar gashinta yana yawo a bayanta bayan tayi packing. Kashe gas din tayi sannan ta juya fried egg din a kula ta rufe ta ajiye kan dinning. Kofar baya data bude dan iska ya shiga taje rufewa ta tsaya lokacinda idanta suka sauka kan inda flowers suka taru kuma ba'a yanke ba. Isa tayi ta tsaya sai a lokacin ya kulada cewa part ne amma dagani ba tare akayisu da wannan gidan ba.

DAN GIDAN MODIBBO Donde viven las historias. Descúbrelo ahora