CHAPTER THIRTEEN: COMFORTABLE

600 55 5
                                    

Parking tayi a harabar assibitin UDUTH. Jakarta ta dauka hadeda wayarta sannan ta kashe motar ta fito. Locking motar tayi sannan suka nufi hanyar amenity sabuwa. Gurin was clean and alright. Room seven suka shiga yan uwa suka gani masu yawa a dakin. Gaida manyan sukayi har kasa kamin suka mike. Baby ta karba hannun mufeeda tana kallanta. Wayarta ya dauka tayi snapping baby din sannan ta bada ita hannun wata Yar uwar mijin zainab din da shigowar su kenan. A nan taji ba a uduth din ta haihu ba problem aka samu wanda hakan yayi sanadiyyar turosu uduth. Murmushi tayi lokacinda ta duba time kamin tayi ta dago tace to mu zamu wuce sai kuma mun dawo.

Sallama sukayiwa sauran sannan suka fita. Suna tafiya sukaji ana sallama juyawa sukayi suka kalla mazan guda biyu. Dan Allah idan bazaki damu ba kidan bani number ki. Bai dace mu tsaya a nan mu-am Sorry please matar aure ce tafada tana yi gaba. Amma bakiyi kama da matar aure ba yafada yana shan gabanta. Harta buda baki zatayi magana aka kirata. Dubawa tayi taga Alhaji me. Dagawa tayi tace salamu alaikum. Bayan ya amsa yace kun fito? Eh gamu zamu mota. Okay kawai yace am dama I was thinking in ajiye mufeeda gida ko kuwa idan mun dawo driver zai maida ita? Kizo gida zan kira Sagir ya dauketa. Kashe wayar tayi sannan tabi ta gefen mutumin ta wuce. Har mota yabisu tsaki mufeeda tayi tace wai baka ganewa ne? Ba Kaji lokacinda tayi waya da mijinta ba. Mufeeda shiga muje idan yanaso yayi conforming yabimu gida ya ganema idansa.

Saida sukayi nisa sannan ta kula ashefa mazan binsu sukeyi. Kinga mufeeda binmu sukeyi ya za'ayi? Babu kome muje gida ba yaya na nan ba? Mufeeda wayarta ta fidda ta shiga insta

ALHAJI's POV
He didn't think much about it lokacinda tayi maganar. Bayan yayi tinani yaga kuma she is right shiyasa ya harta ya fita. Yana waje bayan ya sallami Umar da Yusuf tight friends dinsa ya kirata kamin ya koma cikin gida. Yana fitowa daga wanka yaji karar shigowar text. Dubawa yayi yana gama karanta text din ya dannawa wata number dayayi saving da Deputy kira. Ana dagawa yace I——-

Aisha kuwa kara gudu tayi dan suyi sauri su koma gida. Horn tafara saki to her luck aka bude kamin ta karasa isa. She wa an surprises ganin bataga taron mopols dinda ke gidan ba. Tana parking taga mota tayi parking a bayanta kamar ance mata daga kanki ta hango Alhaji tsaye a bakin kofar gidan. Tafiya yake towards motar bayansu amma ita gabanta ke faduwa. Sai yau ta kara ganin hugeness dinsa kallo daya was enough to tell her he was stiff.

UNKNOWN POV
kai Ismail bakada wayau shiyasa mata ke fooling dinka yanzu wannan din tayi ma kamada matar aure fada kawai tayi. Abubakar banaso a samu matsala idan matar aure cefa kasan za'a samu matsala idan mijinta ya kula. Idan ma ya kula ba sanin mu zaiyi ba kawai saimu tsere sai kace bakada hankali. Take motar Abubakar yayi suma suka shiga gidan sukayi parking. Fitowa sukayi suna magana idan Ismail suka sauka kan Alhaji dake nufarsu. Kai Abubakar kaga wani kato tafe? Tsaki yayi yace wlh Ismail ka cika tsoro in—kaniya daganin wannan za'ayi madaki katti. Ka rigada kaja mana wallahi wannan duk dangin ku babu mai iyawa dashi. Shiga mota sukayi Abubakar yayita kokarin kun nata amma taki tashi. Yana isa yayi knocking a glass din driver's seat. Ganin abun iskanci zai zama yasashi dagewa da elbow dinsa bugu daya glass din ya tar watse.

Kwalarsa ya ciwo daga cikin motar ya fiddashi ta window din kamin yayi jifa dashi. Nuna Ismail yayi yace fito ko naka yafi zama worst. Salun alun ya fita daga cikin motar tun kamin yayi magana ya sauka on his knees yace maigida bata nayima bayani. Wallahi tun lokacinda tace matar aurece nace masa ya kyaleta. Wallahi ni ganin kawai nayi ya shiga gidan nan. Belt dinsa ya cire ya nufi Abubakar dake gefe ganinsa ya nufesa yasashi mikewa yaci na kare. Amma out of nowhere yaga mopols sun fara fitowa. Jibgarsa yayi kamar ya samu jaki yana cikin dukansa aka bude gate mota ta shigo. Plate number din ya kalla ya gane Sagir ne. Kallansu Sagir yayi kamin yace Ismail? Me kakeyi a nan? Wallahi kaddara Sagir. Dan Allah ka gaya masa wlh dawowa ta daga makaranta banyi kwana ukku ba. Ko yanzu Abubakar na raka assibiti.

DAN GIDAN MODIBBO Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang