CHAPTER TWENTY THREE: TAILOR's SHOP

589 46 7
                                    

A nan gidan tayi magrib sannan ta kirashi yazo ya dauketa. Tana ganin kiranshi ana kiran isha picking tayi tace kazo? Eh but ki bari zanje masallaci to pray isha. Okay no problem.

Sallar isha tayi sannan tayi shirin tafiya. Ni kuwa ya maganan zuwanku NYSC? To gamu muna zaman jiran tsammani I have already made the necessary preparation sannan I went through all the procedures.

Allah yasa su kiraku am sure zaman gida yana damun ki Sabrina tafada tana kallanta. Kedai bari kasaba kusan everyday saika shiga school yanzu kuma babu inda kake zuwa. Amma kinga ko aikin anfara I won't be out everyday since gidan kawai zan zana it's not that stressful.

Eh hakane. Har mota tayi mata rakiya suka gaisa da Alhaji sannan su kuma suka wuce. Parking yayi ganin ba gane misalinta yake ba fita yayi daga drivers seat din yaje passengers seat ya bude mata kofar.

Yace oya go and drive am tired tin dazu muke zagayen wannan titin. Dariya tayi tace sorry Alhaji Allah it's just up ahead kadan. Hajiya ki fita kija motar nan am tired sai kinfi ganewa idan kika tuka.

Fita tayi ta shiga drivers seat ta sanya seat belt tana boye dariyarta. An jima ana gaya mata she is direction blind idan dai aisha ce zatayi ma kwatance ka gane to kana cikin matsala dan hauka taka kawai zatayi.

Suna tafiya kusan karshen titin da suka kai ta sanya signal tayi parking gaban wani katon plaza tace gashi. Kallan gurin yayi yace sau uku fa muna wuce wannan plaza din last tim saida nace miki ko nan ne kikace aa.

Murmushi tayi sannan tayi tapping shoulder dinsa tace sorry ban kula ba shiyasa. In a teasing tone yace sai kin biyani kudin mai da kika sani na qona.

Koda muka baro gida full tank ne yanzu ya rage da half tank. Kallan fuel gauge din tayi tana dariya tace Allah kaika shanye abunka ni ba ruwana. Kiran tailor dinta tayi tace gata waje yayi sauri yazo.

Suna dargar mai yace saita biya tace bazata biya ba wayarta tayi ringing. Ganin Saminu tailor yasata Jidda glass batareda ta daga wayar ba ta leka kanta ta window tace saminu gani a nan.

Gayen dake tsaye chan gaban plaza ya nufato su. Hajiya ina wuni? Lafiya kalau saminu ya aiki? Alhamdulillah ai ba motar dana sani bace shiyasa kikaga ban gane ki ba ba komai wlh. Yallabai sannu saminu yace da Alhaji dake kallansu.

Yauwa ya amsa. Ehem dana dinki na kawo ma anko ne nan da kwana ukku za'a fara yaushe zanzo in karba? Bude bayan motar zakaga farar leda kayan ne a ciki.

Duba kayan yayi sannan yace kizo da safe ranarda za'a fara ki karba gabadaya. Okay to nawane kudin dinkin ka. Hajiya ko wanne ki bada dubu goma.

Lafiyar ka kalau kuwa? Kallanta yayi yace hajiya kinga express ne sannan kayan aiki sun tashi. So kake in cire dan kwali muyi lissafi ne? Ni zaka chuta? Koka manta nidin ma na iya dinki nasan nawa kayan suke.

Am not telling you to do something complex something simple nake so. Idan bazaka iya ba nasan hanyar shagon auwalu. Haba hajiya ba—kaga karka kirani hajiya Dan ka chuche ni barni a Aisha na.

Tsaya yafada yana kallan saminu sannan ya daga glass din ya kalleta yace why not just give it to him idan yaci riiba shida Allah. Kallansa tayi tace haka kawai nasan gaskiya zan yadda a chucheni?

Murmushi yayi yace to nawa zai ci idan kika biyashi wannan amount din? Idan ya siya kayan bazasu wuce 2500 ba each sabida yasan banasan too much kwalliya. Meaning zaiyi gaba da 15k dina.

Okay bari inyi magana dashi. Purse dinta ta bude ta bashi 10k. Murmushi yayi kamin yace rike mun.

Yana fita baiyi minti daya suna magana da tailor din ba ya fidda wallet dinsa tana kallansa ya glass din yayi kasa da wallet din ya fidda cash ya mikawa tailor din.

DAN GIDAN MODIBBO Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon