Chapter 49

352 11 3
                                    

♠♣♠♣♠♣♠♣
     ♠♣♠♣♠♣
            ♠♣♠♣
                  ♠♣

*BAN TSANESHI BA*

♠♣♠♣♠♣♠♣
      ♣♠♣♠♣♠
            ♣♠♣♠
                 ♠♣
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN  OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*Story*
          *and*
*Written*
    *By👇*
    
*Asmy Jafar*
*(Ummu Abdulhakim)*

               &

*Zainab Mukhtar*
      *(Ummu Maryam)*
*Aminan juna*👭🏻

*WATTPAD @Asmyjafar*

🅿️-4️⃣9️⃣

____________Za ro ido Yaya Salim yayi cike da mamakin maganar shi, sannan yace "lallai kai ɗan iska ne na ƙarshe, wato ba ma taje zuwa dare ta dawo ba, a'a har kwana kake so tayi maka ko? To ba dani cikin wannan aikin ba kar kasa Umma ta cinye Ni, ina laifin taje ta wuni ka maido ta?

Kai ba fa nason iskanci fa, mutum da ma tarshi dan ka samu na laɓa ta ge fenka ina kwadayin ka sami ladar sadar da ma'aurata shine zaka wani sako Ni gaba da iskancinka, anƙi taje ta wuni ɗin kwana za tayi, cewa Yaya Salim yayi to shikenan sai kaje kayi yanda kake so ɗin nidai ba ruwana, ya ƙare maganar da dariya.
Yaya Deeni yace "ka san dai zan iya ko?  Eh ai nasan zaka iya ɗi, fiye da wannan ma saikayi shiyasa nace kaje kayi da kanka. Cewar Yaya Salim, Deeni yace "Allah ka san zan aikata ba dan wannan sarkin matsoratan ba, duk dan ita nakeyi, amma da ta nine da saidai ku ne memu ku rasa Allah.

Kwashewa da dariya Yaya Salim yayi, yaya Deeni yace "Salim meye haka? ka tsaya mana muyi magana ka wani tusani gaba kana dariya Allah ina cikin damuwa kuma ka fi kowa sanin haka, pls ya za'ayi?

Tattara hankalin shi yayi sannan yace "mafita ɗaya ce yanzu kaje ka cewa Jiddar ta kira umma a waya ta sanar da ita tanason za taje gidana, ka ga idan taje Ni kuma zuwa dare sai inkira Umma in shaida mata inaso Jidda tayi weekend a gidana, ina ga hakan zaifi dan ka san haka kawai bazan cewa Umma Jidda na gida na ba, intace da izinin wa Jiddar tafita ince mata me? In Kuma tace saida nayi son raina naje da ita sannan zan kira ta wace amsa zan ba ta? Kuma za ta iyayin zargin da wata a ƙasa tunda ka shafa min ka shin ka ji, kome nayi ganin za tayi haɗin ba ki ne.

Ta fawa sukayi cike da gamsuwa da shawarar amininnasa yace "Man kanka yana wuta fa! Ai Ni duk ban tsaya yin wannan dogon tunanin ba idona ya rufe kawai Ni dai ma ta ta ce a gabana,  dariya Yaya Salim yayi yace "an faɗi ba nauyi dai, a nata rawar jiki akan ƴar ƙanwa.
Kai sha re dallah, ni nasan yanda nakeji malam, dan haka jeka ka ga ma aikin ka, ya faɗa yana ɗan tu rashi baya kaɗan, cewa yaya Salim  yayi da kyau go be ma ra na ce, sannan sukayi sallama kowa ya faɗa motarshi suka bar gidan.

Saida suka hau titi sannan Jidda tace "Yaya ina za muje ne? Gidanmu, ya bata amsa kai tsaye. Buɗe ido tayi cike da fargaba tace "Yaya Umma zata nemeni fa, idan ta nemeki sai ki sanar da ita kin koma gidan ki, tsoro da fa ɗuwar gaba ne suka risketa a lokaci ɗaya, dan ta san halinshi sarai zai iya aikata abinda ya faɗa, amma kuma sai wani tunani yazo mata, cike da ƙarfafa wa kanta guiwa  tace "to ai Yaya ban dauko ka ya na ba da jakar makaranta, mezai hana mu juya in shiga in ɗauka sai ka jira ni a waje, kallon yaushe aka haife ki har kika girman da za ki yimin wayo yayi mata, amma sai ta ba sar tare da cewa "Allah Yaya bazan daɗe ba, ina ɗauka zan juyo.

Murmushi yayi tare da cewa "ah lallai Auta an girma, har kamar Ni za kiyiwa wayo? To ki barshi kawai zanje da kaina in hado maki komai na ki, hakan yayi miki?

BAN TSANESHI BAWhere stories live. Discover now