chapter 40

367 19 4
                                    

♠♣♠♣♠♣♠♣
     ♠♣♠♣♠♣
            ♠♣♠♣
                  ♠♣

*BAN TSANESHI BA*

♠♣♠♣♠♣♠♣
      ♣♠♣♠♣♠
            ♣♠♣♠
                 ♠♣
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN  OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*story*
          *and*
*written*
    *by👇*
    
*Asmy jafar*
*(Ummu abdulhakim)*

               &

*zainab mukhtar*
      *(ummu maryam)*
*Aminan juna*👭🏻

*WATTPAD @Asmyjafar*

🅿️-4️⃣0️⃣

____________Tsaye take a tsakiyar falon har zuwa lokacin idanun ta na kan kofar, zuciyar ta na raya mata taje ta tsaida shi ta bashi haƙuri, wata zuciyar kuma tana raya mata ta bishi kawae suje dan tasan ko da taje ba lallai bane umma ta barta ta bishi, kuma ma ba zata iya zuwa rokar umman ba, yayin da ɗayar zuciyar ke bata shawara da tayi haƙuri kawai taje tayi kwanciyar ta, tare da tunano mata wahalhalun da tasha a hannun anty Hajara lokacin zaman ta gidan shi.

        Tsaye take cikin rashin sanin abinyi har taji tashin motar shi, zubewa tayi a nan gurin cike da zargi da ganin laifin kanta, tana ganin kamar ita ce sanadin shigar shi damuwa, tun da ya daɗe yana biyar ta akan ta koma gidan shi taƙi, hakan yasa ta ɗora laifin kacokan a kanta.

Da ƙyar dai taja ƙafafun ta ta nufi sama jikin ta a sanyaye.

          Tun daga nesa ya hango mutum duk a tunanin shi Hajara ce sai dai yana ƙarasowa yaga saɓanin hakan, dan kuwa daga yanayin shigarta ya tabbatar ba matar shi bace, lokacin da ya ƙaraso da nufin buɗe kofar ya ganta a daidai bakin kofar ta daura hannun ta a handle din ƙofar ta ja wata irin uwar foster fuskar nan cike da make-up ga ɗinkin jikin ta ya matseta sosai ƙirjin nan rabi duk a waje, ga su tirtsa tirtsa dan daman zee ba dai breast ba akwai su kam mashaallah.

     Tsaye deeni yayi yana kallon ikon Allah ganin ta riƙe handle din ƙofar, bai tanka taba sai ma ƙoƙarin saka key yake yi a inda zai buɗe.

     Shafa hannun shi zee tayi cike da salo da makirci irin nasu na yan duniya, da sauri ya ɗago fuskar shi suka yi ido huɗu da ita, wani irin mugun kallo mai nuni da gargadi yayi mata, har a ranta ta tsorara da irin kallon da yayi mata sai dai batajin zatayi wasa da wannan damar da Allah ya bata.

    Ɗago idon ta tayi cike da karairaya tana fari da idon zata yi magana sai ganin tayi ya buɗe ƙofar yana ƙoƙarin shiga ciki, fasa yin maganar tayi da sauri tabi bayanshi gudun kar ya rufe ƙofar, ai ko ta makara dan da iya ƙarfin shi ya tura ta baya ya rufe ƙofar, ji kake bamm!!

Dogon tsaki ya ja tare da wucewa dakin shi kai tsaye, a ranshi yana raya dole ma yayi wa hannun shi wankin tsarki tunda ya taɓa wannan najasar, dan shi a gunshi ga baki ɗayan ta najasa ce.

    Tsaye zee take a inda ya barta cike da tsananin takaici da ɓacin rai, in ranta yayi dubu to dukan su sun ɓaci, wata irin shaƙiyiyar dariya tayi a cikin halin ɓacin ran, wanda ita kaɗai ta san ma'anar ta, juyawa tayi da nufin tafiya a ranta tana ci gaba da ƙarfafa wa kanta akan niyyar da take son aiwatarwa, a fili ta furta "naso in bika da lalama deeni amma naga alamar kai ba hakan kake so ba, to zaka san ka wulaƙantani ne, zan tafi yanzu, amma ka sani zan dawo, lokacin da zan dawo kuwa toh shirina zan dawo wanda duk iya taurin kanka ba ka isa ka tsallake ko bijire min ba. Murmushin mugunta tayi tare da barin gidan gaba ɗaya.

BAN TSANESHI BAWhere stories live. Discover now