chapter 43

357 15 4
                                    

♠♣♠♣♠♣♠♣
     ♠♣♠♣♠♣
            ♠♣♠♣
                  ♠♣

*BAN TSANESHI BA*

♠♣♠♣♠♣♠♣
      ♣♠♣♠♣♠
            ♣♠♣♠
                 ♠♣
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN  OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*story*
          *and*
*written*
    *by👇*
    
*Asmy jafar*
*(Ummu abdulhakim)*

               &

*zainab mukhtar*
      *(ummu maryam)*
*Aminan juna*👭🏻

*WATTPAD @Asmyjafar*

*DEDICATED TO MY MOMCY SA'ADERHT ABDALLAH MADOUBEE ALLAH YA BADA SA'AR EXAMS MRS.....😉 Na daiyi shiru*🤣🤣

🅿️-4️⃣3️⃣

_________Basu bar gidan anty nafisa ba sai bayan magrib, ya na ajiye su ya wuce masallaci dan an fara kiran isha.

Tun daga wannan ranar sai ya zamto kusan kullum sai yaya deeni ya keɓe da jidda yayi wasannin shi da ita.

Wani lokacin ma a falon umma suke yi in ta fita, wani lokacin kuma a ɗakin su ko tsohon ɗakin shi na samar taka.

Sun yi wata irin shakuwa ta ban mamaki, kullum in ya tashi aiki yana gidan wani lokacin ma har sha daya na dare ya ke kaiwa sannan ya wuce gidan shi.

Kuma har yau kimanin kwana bakwai Hajara ba ta waiwayi gidan ta ba, amma tana tunanin zuwa gidan a gobe, dan gobe ne daurin auren nadiya, shi yasa za taje dan gabatar da aikin malam yanda ko da zata dawo daga rakiyar amarya abin ya kama jikin shi bazai tuhume ta ko ya mata fadan zama da tayi a gidan auren ba.

Tsawon Sati ɗaya kenan suka dauka suna shirya bidi'o'i kullum da kalar event din da za'ayi har sati ɗaya ya cika.

Gobe ne daurin aure kuma a goben ne za'a kai amarya gidan mijinta da ke garin Abuja.

A yau misalin ƙarfe 5 na yamma Hajara tayi wa gidan tsinke dan aiwatar da kudirin ta, saboda gobe ɗaurin auren safe za'ayi kuma ana daurawa zasu wuce kai amarya, shi yasa take so ta gama aikin kafin ta tafi.

Sauri sauri take yi dan  kuwa akwae event din karshe da zasu yi a yau, kuma zazzafa ne na rikakkun 'ya'yan attajirai hakan yasa suka kai shagalin har *unity event* can ƙarshen gari dan ma kar mutune suyi tururuwan zuwa.

Da spare keys din da ke hannun ta tayi amfani ta shiga gidan ba tare da ta tsaya amsa gaisuwar da su Kabiru da baba ke mata ba sai dai daga masu kai da tayi.

Cike da farin cikin ganin ba motar sa a harabar gidan ta ƙarasa cikin gidan dan ta tabbatar bai cikin gidan.

Tana cikin buɗe kofar da zata sadata da ainihin cikin gidan wayar ta ta fara ruri, ciro wayar tayi a jakar ta tana faɗin" nasan ma nadiya ce uwar anace yanzu sai ta iya cewa na daɗe.

Kara wayar tayi a kunnen ta tana ci gaba da buɗe kofar.

Tana ɗaga wayar Nadiya ta fara azalzalar ta, in batayi nisa ba ta dawo ta kawo mata sarkar ta, tana cikin pose dinta.

Har zata yi musu sai ta duba taga ashe sarkar na cikin jakar ta ita bata ma san tana jakar ta ba.

Cewa tayi kiyi hakuri nadiya yanzun nan zan dawo dan gani har na iso gidan ma.

BAN TSANESHI BAWhere stories live. Discover now