chapter 44

360 13 14
                                    

♠♣♠♣♠♣♠♣
     ♠♣♠♣♠♣
            ♠♣♠♣
                  ♠♣

*BAN TSANESHI BA*

♠♣♠♣♠♣♠♣
      ♣♠♣♠♣♠
            ♣♠♣♠
                 ♠♣
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN  OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*story*
          *and*
*written*
    *by👇*
    
*Asmy jafar*
*(Ummu abdulhakim)*

               &

*zainab mukhtar*
      *(ummu maryam)*
*Aminan juna*👭🏻

*WATTPAD @Asmyjafar*

*SADAUKARWA GAREKU DUKKAN KU MEMBERS NA ƘUNGIYAR MU MAI ALBARKA (PERFECT WRITERS ASSOCIATION🌞) ALLAH YA KARA MANA HADIN KAI DA KAUNAR JUNA YA KARA DAUKAKA🙏🏻 SON SO FISABILILLAH😍*

*_____________________________*

*👍🏻👍🏻👍🏻JINJINAR BAN GIRMA GARE KI SHUGABA TA GARI ANTY SAFNA JAWABI ALLAH YA KARA GIRMA ANTYNMU😍🥰*

🅿️-4️⃣4️⃣

_____Koda Jidda ta fito bata tarar da yaya Deeni a falon ba, sai dai ta wuce kitchen ta haɗa mai komai har ruwan sha sai da ɗora sannan ta fito falo ta zauna zaman jiran shigowar shi.

Wayarta ta fitar tana dandannawa lokaci zuwa lokaci kuma tana kallon ƙofar shigowa ko zata yi sa'ar ganin ɓullowarshi sai dai sam bai shigo ba.

Ta ɗauki tsawon mintuna a zaune kafin daga bisani wayar ta, ta hau ruri, sunan Yaya Deeni ne ya bayyana hakan yasa ta latsa wayar tare da kangawa a kunnen ta.

"Ki kawon abinci a ɗaki nah yanzun nan. Daga haka ya katse wayar batareda ya bata damar yin magana ba.
Warware gyalen da ke kanta tayi tare da rufawa a jikin ta sannan tayi hanyar waje tana riƙe da tiren da ta ɗora abincin a kai.

Knocking ƙofar tayi a hankali amma shiru ba'a bata damar shiga ba, sake ƙwankwasa wa tayi nan ma shiru hakan yasa ta tura ƙofar a hankali tare da shiga cikin ɗakin.

Kwance yake akan katifar ɗakin, sanye da gajeren wando da singlet fara kar yayi kwanciyar rub da ciki yana latsa wayar da ke hannunsa.

Da sallama ta shiga sannan ta ajiye tiren hannun ta agefe. Gaidashi tayi tare da ƙara yi mai ya jiki sannan ta shiga ƙoƙarin gabatar mai da abinci.

Ƙasa ya sakko  ya tankwashe ƙafafun sa tare da sanya plate ɗin a tsakiya. Ganin ta haɗa mai komai har ya fara ci yasa ta miƙe dan komawa cikin gida kafin Umma ta neme ta.

"Koma ki zauna, wa ya baki izinin tafiya ne? Ko nace ki tafi? Yaya Deeni ya faɗa yana mai kure ta da farare kar din idon shi, tsaye tayi tana wasa da yatsun hannun ta tana ɗan murmushi, hannu ya miƙa da nufin ya janyo ta tayi baya tana yar dariya tare da cewa" Umma zata neme ni fa Yaya, bai kula ta ba sai ma janyo ta da yayi ya zaunar da ita kusa da shi duk rabin jikin ta na kanshi, a haka ya cigaba da cin abincin, sai da ya kusa rabi sannan yace "af🤭 na manta ai kin ga buɗe bakin in baki kar kice na miki rowa, ya faɗa yana nufar ɗan ƙaramin bakin ta da spoon din hannun shi.

Kaucewa tayi tana girgiza "Ni fa a ƙoshe nake, ta faɗa cike da zallar Shagwa6a har da marairaicewa.

"Ban yarda ba sai kin ci, Yaya Deeni ya faɗa yana cewa" oyah haaa, dole ba dan taso ba ta karɓa har suka gama sannan ya gyara mata zama da kyau a jikin shi.

BAN TSANESHI BAWhere stories live. Discover now