chapter 17

260 14 1
                                    

♠♣♠♣♠♣♠♣
     ♠♣♠♣♠♣
            ♠♣♠♣
                  ♠♣

*BAN TSANESHI BA*

♠♣♠♣♠♣♠♣
      ♣♠♣♠♣♠
            ♣♠♣♠
                 ♠♣

*story and written by*
*Asmau jafar*
  *(Ummu abdulhakim)*
             &
*zainab mukhtar*
        *(ummu maryam)*

🅿️-1️⃣7️⃣

..........Har suka qaraso yana biye dasu a baya sai dai kafin ya ankare tuni an bude musu makeken gate din sun shige,

"Ohh shit!

Amma babyn nan ta ita raining sense, Amma ba komai tunda Naga unguwarku Kuma Naga gidanku,

Reverse yayi ya bar unguwar,
Washe gari ma Koda suka fito exams yayi parking motorsa a harabar skul dinsu Yana ganinta yayi wuf ya fito tare da nufarta,

Sallama yayi musu, aysha ce ta amsa mai,

Gyara tsayuwa yayi tare da sakin wani shaqiyin murmushi,
Kallonsa ya maida Kan Aisha tare da cewa" qawarmu Ina wuni ya exams din?

"Lfylau alhmdllh"

"Good Amma Dan Allah ko Zaki bani aron qawarki na mintuna qalilan?

"Eh mezai hana, ta fada tana qoqarin miqewa tsaye,

"Ke miye haka ne, pls kiyi zamanki mna, ta fada tana riqe gefen rigarta,

"A'a bari in Dan Baku wuri ai bazan yi nisa ba inshallah,
Kafin jidda ta ankare har ta bar gun tana dariya qasaqasa,

Duqar da kanta tayi a qasa, saboda ganin sauran dalibai dake kallonsu Kuma ko ba haka bama ita kunyar tsayuwa da namiji takeyi,

Lura da yayi kamar a tsarge take yasanya yace Mata ta tashi su je cikin motarshi magana yake sonyi da ita,

Duka idanunta ta zaro tare da girgiza kanta alamar a'a,

Dage kafadunshi yayi alamar ko ajikinshi tare da qoqarin Zama gun da aysha ta tashi,

Da sauri ta miqe tsaye, kallonta yayi yace "ya haka?

"Ba komai Ni dai Dan Allah ka tafi kawai kaga mutane sai kallonmu sukeyi,

"To ai laifinkine baby banace muje mota ba Kika qi,

"Ni dai ka tafi Dan Allah,

"Naji Zan tafi Amma sai kin min alqawarin anjima Inna zo gidanku Zaki fito,

"Eh Zan fito"
Ta fada da sauri Dan duk atakure take Jin kanta,

Murmushi yayi yace" Wai ya hakane eye? Naga sai wani kalle kalle kike tayi kamar wata Mara gasky,

"Ba komai sai anjima,

Ai maimakon ya tafi ma sai wata maganar yasake zagulowa,

" Hmm Baby jiya Kika shareni alhalin Kuma nasan kinganni sarai, Kuma fa  har gidanku na biki, Nan ma Kika shige Kika barni ko?

"Ko so Kika yi inyi fushi in tafi abuna in barki?
Shiru tayi batace Mai uffan ba,

"Hmm to bazanyi fushiba Dan Ni kadai nasan yanda nake jinki a raina,

Sake duban gefe da gefenta tayi taga kowa na kallonsu Kuma Gashi bataga alamar zai wuce ya barta ba,
Kawai sai ta duqa ta sungumi Jakarta tana qoqarin barin gun,

"Kinga yi hakuri kiyi zamanki Ni zantafi Amma dai pls ki gayamin sunanki da kin fada Zan wuce,
Jin yace zai wuce ne yasa ta ce mishi

"HAUWA'U"

BAN TSANESHI BAWhere stories live. Discover now