chapter 41

340 17 3
                                    

♠♣♠♣♠♣♠♣
     ♠♣♠♣♠♣
            ♠♣♠♣
                  ♠♣

*BAN TSANESHI BA*

♠♣♠♣♠♣♠♣
      ♣♠♣♠♣♠
            ♣♠♣♠
                 ♠♣
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN  OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*story*
          *and*
*written*
    *by👇*
    
*Asmy jafar*
*(Ummu abdulhakim)*

               &

*zainab mukhtar*
      *(ummu maryam)*
*Aminan juna*👭🏻

*WATTPAD @Asmyjafar*

*DEDICATED TO NADIYA AHMAD BELLO ALLAH YA ƘARA BUDI GODIYA DUBU🥰*

*Godiya ta musamman gare ku👇*
*Sis nafisat alwasa*
*Sis adama aliyu*
*Allah ya bar ƙauna😍*

*My anty and momcy miss you so much😥💔*

*@SIS HAUWA JAFAR ALLAH YABADA SA'AR EXAMS DAKE DA KULLIHIN MUSULMI BAKI DAYA🙏🏻*

🅿️-4️⃣1️⃣

_______________zaune dibis jidda tayi a bayin tana mai tariyo abinda ya faru a tsakanin su, jikin ta duk ya mace, sosai ya saukar mata da kasala ga fitinan nen ƙamshin shi da ya tafi ya bar mata, ta ɗauki lokaci kafin tayi wankan tayi brush ta fito.

Itama jikin ta duk yayi laushi haka ta fito daga bayin. Miƙewa tsaye baby tayi tana tafa hannu a lokaci guda take cewa "innalillahi wa Inna ilayhi raji'un..." Bakin ta a bude tace "jidda dama kina toilet din ne uncle ya shiga? Ke da uncle ne a toilet daman?

Ko kallon ta jidda batayi ba sai ma nufar inda kayan ta suke tayi tana duddubawa.

Ganin da baby tayi jidda ta share ta taƙi kulata yasa tace" munafurcin banza munafurcin wofi, wai Ni zaki yiwa irin na yan bariki kin wani share Ni kamar ba ki aikata abinda nake magana akai ba, daman tabarmar kunya ai da hauka ake naɗe ta.

Sai lokacin jidda ta juyo ta kalle ta, dariya tayi sannan tace "akwai haramcin yin hakan ne iyee malama baby? Kin wani ta sani a gaba kina kira min kunya, a ina kunyar take ne?
"A'a'aaa Ni kam daina dangan tani da abin kunya malama. Jidda ta faɗa cikin son ta rainawa babyr hankali, har da sakin wani makirin murmushi.

Riƙe baki baby tayi tace" Eh lallai kam kin faɗi haka amma zaki maimaita a gaban umma, daga haka ta shiga ƙoƙarin miƙe wa kamar da gaske gun umman za taje, da gudu jidda ta faɗa kanta suka yi baya gaba ɗayan su, magiya ta shiga yi mata akan kar ta faɗa.

Cewa baby tayi to Ni kam ɗaga Ni kar ki karya ni ki rage min sadaki gara ke an riga da ankwashe ki, dariya suka yi dukan su sannan baby tace" kinsan Allah jidda wlhi uncle bashi da kunya Ni fa bana tunanin ma yanda kuke ɗin nan ya iya yi maki wani kallo ma bale a kai ga wani abin amma ƙememe dan rashin ta ido shine zai biki a toilet ya kalle, Kuma a gidan umma🤔kai uncle said abarshi, Bai ko jin nauyin muzo mu ganku tare shine da ya fito ya wani fuske irin kar inga damar shi ɗin nan, kai uncle anga boss🤣🤣

Murmushi kawae jidda tayi ba tare da ta tanka taba ta ci gaba da shiryawa.

Yaya salim ne zaune a office ɗin yaya deeni suna tattaunawa, gayamai abinda ke faruwa a tsakanin shi da Hajara yaya deeni ke yi, tare da cewa" ta kai maƙurar hakurin shi anzo gun da bazai iya zurewa ba dan rainin hankalin yayi yawa.

BAN TSANESHI BAWhere stories live. Discover now