chapter 46

500 23 13
                                    

♠♣♠♣♠♣♠♣
     ♠♣♠♣♠♣
            ♠♣♠♣
                  ♠♣

*BAN TSANESHI BA*

♠♣♠♣♠♣♠♣
      ♣♠♣♠♣♠
            ♣♠♣♠
                 ♠♣
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN  OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*story*
          *and*
*written*
    *by👇*
    
*Asmy Jafar*
*(Ummu Abdulhakim)*

               &

*Zainab Mukhtar*
      *(Ummu Maryam)*
*Aminan juna*👭🏻

*WATTPAD @Asmyjafar*

*NAGODE SOSAI DA ADDU'OIN KU GARENI MASOYANA KUMA ƳAN UWANAH SON SO FISABILILLAH😍🥰❤️*

     *☆☆☆☆✩✩✩✩*

*KUMA MASOYA NAH NA WATTPAD BAN MANTA DAKU BA INA GODIYA SOSAI KUMA INA JINJINAWA ƘAUNARKU DA ADDU'OIN KU GARENI NAGODE SOSAI ALLAH YA BAR ƘAUNA*🥰😍

*SADAUKARWA GAREKU DUKKAN KU MASOYAN BAN TSANESHI BA, MUN BAKU KYAUTAR WANNAN PAGE ƊIN GABA ƊAYAN SHI KUYI YANDA KUKE SO DASHI💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻KUYI KOMAI BA KOMAI MASOYA❤️😍🥰*

🅿️-4️⃣6️⃣

______Tsaye suka yi cirko cirko suna kallon juna, yayin da Hajara ke bin Zee da kallon tuhuma, bakin ta na rawa take furta" me...me.. zan.. gani.. haka Zee? Meyakai card ɗin ki hannun miji na?

Daburcewa Zee tayi sai dai tsabar zaman ta yar duniya sai cewa tayi" ina zan sani kuwa tunda tare muka shigo dake muka ganta a hannun shi.

Duk da haka Hajara bata samu nutsuwa ba, ta kuma shiga kokwanto da zargin Zee ɗin, sai dai Kasancewar tashin hankalin da take ciki ya shafe wannan yasa bata wani tsaya bin abin ba kawai ta nufi ƙofar da zata sada ta cikin gidan.

Duk saurin da Kabiru yake yi domin cika aikin da maigidan nashi ya sanya shi baisa ya riga su isa ƙofar falon ba, kasancewar akwai tazara mai ɗan nisa daga gate ɗin gidan zuwa cikin gidan.

Ƙoƙarin buɗe ƙofar take yi, har hannun ta na rawa, sai dai jin tayi an fisge key ɗin daga hannun ta.

A fusace ta juyo har suna haɗa baki gurin kunduma mashi zagi itada Zee, sai dai sam bai kula su ba bare ya mayar da martani, a maimakon haka ma tafiyar shi yayi, duk da ya daɗe yana jiran zuwan wannan ranar ko dan wulaƙancin da matar gidan ke yi musu sai dai duk da haka ba zai kula taba kodan mutuncin uban gidan shi.

Biyo shi suka yi yayin da Hajara tasha gaban shi ta shiga surfa mishi zagi ta uwa ta uba, tare da cewa kuma maza ya miƙo mata key'n, shareta yayi ya mayar da hankali kan Zee dake zagin shi itama, sannan yace" ke ƙaramar kuruwa ki shiga taitayin ki, inkin ga ita na barta toh ke bazan barki ba, ko itan darajar maigidan taci shi yasa na ƙyale ta ba dan mutuncin ta yakai a raga mata ba, amma ke bazan lamunci ki ci min mutunci ba dan kisani.

Mukulli kuma bazan bada, ya faɗa yana karkada ɗan mukullin yace umarni aka bani kar insake ku shigar mishi gida dan haka sai ayi nan... Ya faɗa yana nuna ƙofar fita.

Hayayyako mai suka yi musamman Hajara kamar ta doke shi wai ita zai cewa bata da mutunci?

Gyada kanshi yayi yace" ƙwarrai da gaske kuwa, ko ba ke kika yi ajiya acan ba? Ya nuna mata gun da tayi surƙullen ta suka tone shida amininshi, kallon gun tayi kwarai ta tuna kenan shine sanadin shigar ta wannan halin, dawo da kallon ta tayi gun shi tare da tafa hannun ta, tace" gud, aikin ka yana kyau amma ka tabbatar zakayi nadama ba kaɗan ba, jan hannun Zee tayi tace "zo mu wuce ki bar shi kawai zamu haɗe da shi ne.

BAN TSANESHI BAWhere stories live. Discover now