chapter 50

350 20 1
                                    

♣♠♣♠♣♠♣
♠♣♠♣♠♣
♠♣♠♣
♠♣

*BAN TSANESHI BA*

♠♣♠♣♠♣♠♣
♣♠♣♠♣♠
♣♠♣♠
♠♣
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*story*
*and*
*written*
*by👇*

*Asmy Jafar*
*(Ummu Abdulhakim)*

&

*Zainab Mukhtar*
*(Ummu Maryam)*
*Aminan juna*👭🏻

*WATTPAD @Asmyjafar*

*Sadaukar wa ga ilahirin members na PERFECT WRITERS ASSOCIATION son so Fisabilillah🥰 Allah ya ƙara haɗa kanmu ya ɗaukaka ƙungiyar mu.*

*Godiya da jinjina gare ku bisa ƙaunar ku ga wannan littafin, Anty Nafisat Alwasa, Adama Aliyu, sis Nafisat Ibrahim, Fiddausi, Amina Badamasi yusif, Allah yabar ƙauna🥰*

🅿️-5️⃣0️⃣

____________Haka suka rabu Yaya Salim sai faman tsokanar shi yake, komawa tashi motar yayi ya ta da suka cigaba da tafiya, saidai ta sha tsokana kafin su isa gida, har yana tambayar ta wani satin dai za tasa ke yimai weekend ko, shiru tayi bata bashi amsa ba, dan ita kanta taji daɗin wannan weekend ɗin, a ƙofar gida yayi parking dan akwai abinda yake so yayi, dan haka gaida Umma kawai zaiyi ya wuce, sai kuma aka samu akasi basu tarar da Ummar ba, hakan yasa yayiwa Jiddar sallama ya wuce tare da cewa sai ya dawo zuwa anjima. Sai gab da magariba sannan ta dawo sun gaisa har tana tambayar ta ya tabaro su Asma'un da Khalil? Tace, "duk suna lafiya, sunce agaishe ta," kasancewar lokacin sallah ya gabato yasa suka mike dan bada farali

Ranar Monday tun 7 ta wuce school kasancewar su Baby duk basu dawo ba, watakil ma sai auran Yaya Sadiq sannan za su dawo gidan.

Jidda zaune a cikin aji, ba abinda take yi sai faman raha da annashuwa, Jifa-jifa kuma sai ta saki murmushi mai sauti har da rufe fuska da handout. Abokan karatun ta duk sun lura yau tana cikin nishadi da farin ciki amma da suka tambayi dalilin wannan walwalar sai cewa tayi ba komai, dole suka ƙyaleta, ƙarshe ma suka tattara suka cafeteria.

Fitowar su keda wuya motar su Hajara na isowa da matsiya cin gudu, kallon farko da Jidda tayiwa motar gaban ta ya yanke ya faɗi amma kuma sai ta basar, kasancewar motar Zee ce, Jidda batasan motar ba, kuma gilashin baƙi ne wulik, baza ka iya hango wanda ke ciki ba.
Daidai wurin su Jidda motar ta ja birki, cikin abinda baifi ƙifta war ido ba Zee ta fito tare da janyo Jiddar da ƙarfin tsiya ta shigar da ita motar. Kasancewar akwai ɗalibai da yawa a wurin yasa hayaniya da ihun jama'a suka fara tashi, yayinda wasu samari suka bi motar da gudu a baya, wasu kuma suka ɗebi duwatsu suna jifan bayan motar, amma duk da haka bai hana masu tserewa da Jiddar ba.

Ƙawayen ta da suke tare ne suka yi gaggawar kiran number Baby, kasancewar sun san gidan su ɗaya, faɗa mata komai da ya faru suka yi. Ai tsananin firgici da ruɗewar da Babu tayi yasa komai ya kwance mata, ta rasa ta inda za ta fara, sai da Hafsah tace, "Baby kiyi sauri ki kira Uncle, waya ta ba Kati, " sannan fa Baby ta danna kiran Deeni tare da shaida mai abinda ke faruwa.

Jidda kuwa ai faɗar irin tashin hankalin da ta shiga ɓata baki ne, ba abinda ke fitowa bakin ta sai, "Ni ku sauke ke Ni, ba abinda nayi muku, Ni me nayi muku ne?" Wata irin tsawa Hajara ta doka mata tare da cewa, "ke rufe mana wannan ɗan iskan bakin na ki kafin inyi Ƙasa-ƙasa dake ana wurin," yayinda Zee tace, "ba ke ƴar iska bako? Yau za kiyi bayani dan uban ki," shiru Jidda tayi dan kuwa shine kawai mafita a gareta, sai dai bakin ta yana ɗan motsa wa alamar addu'a take yi dan neman kuɓuta daga sharrin su.

BAN TSANESHI BAWhere stories live. Discover now