𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 37

395 17 1
                                    

♠♣♠♣♠♣♠♣
     ♠♣♠♣♠♣
            ♠♣♠♣
                  ♠♣

*BAN TSANESHI BA*

♠♣♠♣♠♣♠♣
      ♣♠♣♠♣♠
            ♣♠♣♠
                 ♠♣

*story and written by*
*𝔸𝕤𝕞𝕪 𝕛𝕒𝕗𝕒𝕣*
  *(Ummu abdulhakim)*
             &
*𝕫𝕒𝕚𝕟𝕒𝕓 𝕞𝕦𝕜𝕙𝕥𝕒𝕣*
        *(ummu maryam)*
*𝒂𝒎𝒊𝒏𝒂𝒏 𝒋𝒖𝒏𝒂 👭🏻*

🅿️-3️⃣7️⃣

___________yaya deeni na isa gidan shi dakin shi ya zarce tare da rufewa batare da ya tsaya saurarar shirmen Hajara ba,  ruwa ya watsa tare da kwanciya bayan ya karkaɗe gadon shi, wayarshi ya janyo tare da danna number jidda da ya ɗauka a wayar ta, sai dai har wayar ta yanke bata ɗaga ba.

Jidda kuwa a daidai wannan lokacin tana kwance ne a kan katafaren gadon ta tana mirgina, tunanin wannan sabon salo da yayan nata ya tsiro dashi take yi, gefe guda kuma tana cike da shaukin da ya tafi ya barta a ciki, tana ji wayar ta ringing amma ta share sai da ta ga kiran ya sake shigowa ne sannan ta janyo wayar cike da kasala da tunanin waye yake kiranta a tsohon daren nan dan sha ɗaya tayi har da kusan mintuna ashirin.

Cike da kasala ta danna wayar tare da karawa a kunnen ta sai dai bata yi magana ba, kasancewar taga baƙuwar number, a bangaren yaya deeni ma hakan ce kasance dan shiru yayi yana jira ta fara yin magana, sai da ya ji shirun yayi yawa ne sannan yace,

"Assalamu alaiki!

Toshe bakin ta tayi da sauri jin muryar yaya deeni,  sannan tace,

"Wa'alaikassalam,
Har tayi nufin gaidashi sai kuma ta fasa tana mai aiyana wani abu a ranta, fuskewa tayi tare da cewa cewar"wake magana?

"Shareta yayi kamar baiji ba, ganin ta raina mishi hankali, sake cewa tayi "waye? Shima kamar bazai amsa taba sai kuma yayi tunanin cewa yakamata fa ya ajiye matsayin yaya ya karkato da hankali matar shi kodan umma ta bashi kayan shi yayi gaba.

Cewa yayi "me kike jira bakiyi bacci ba?

Dan sauke ajiyar zuciya tayi kamar gaske sannan tace" yanzun nake shirin yi, sannan ta gaidashi, amsata yayi da lafiya, duk kuma suka yi shiru kasancewar abin ya zamar musu wani baƙon al'amari,   Katse shirun yayi da cewar duk azalzalar da kika dinga yi min na bacci kikeji amma shine har yanzu baki yi?

Shiru tayi tana murmushi, yace gayamin gaskiya auta kodai kina tunanin yayan ki ne uhhmm?

Rufe fuska tayi kamar yana gaban ta, tayi yar dariya sannan tace Allah yaya bacci zanyi da ace baka kirani ba ma da tuni nayi baccin.

Murmushi yayi yace"okay tom Bari in bar ki kisami ishashshen  bacci saboda school, amma gobe ma da safe zaki fita kamar yanda kika saba?

"Eh, tabashi amsa a nutse, gyada kanshi yayi sannan yace "ok to kijarani muje tare nima gobe akwae abinda zanyi a school ɗinku,

"Tom, tace, yace"ok toh kiyi bacci kar ki makara kinji? Na hutar da zuciyar ki da tunani na ki gayamata na haƙuri dan haka ta barki kiyi baccin ki dan gobe tun da safe zata ganni kinji autar yaya?

Rufe fuska tayi tare da kashe wayar gaba ɗaya a fili take cewa "ohhni yaya deeni kana bani kunya wlhi,

A nashi bangaren kuwa dariya yayi tare da cewa autar mu saura ƙiris, sauran ƙiris ki shigo hannuna, murmushi yayi tare da gyara kwanciya, duk da dimbin sha'awar da ke addabar shi amma haka ya hakura dan sanin halin da yake ciki da Hajara, da haka har ya yi nasarar yin bacci yana mai cike da begen yar ƙanwar tashi.

BAN TSANESHI BAWhere stories live. Discover now