chapter 24

263 13 0
                                    

♠♣♠♣♠♣♠♣
     ♠♣♠♣♠♣
            ♠♣♠♣
                  ♠♣

*BAN TSANESHI BA*

♠♣♠♣♠♣♠♣
      ♣♠♣♠♣♠
            ♣♠♣♠
                 ♠♣

*story and written by*
*Asmau jafar*
  *(Ummu abdulhakim)*
             &
*zainab mukhtar*
        *(ummu maryam)*
*Aminan juna 👭🏻*

🅿️-2️⃣4️⃣

*___________________________________________________________* bayan sun gama sallah har sun fito masallacin ne Yaya Salim ya tsayar da Yaya deeni bayan sun gaisane yake cewa,

"Deeni meyayi zafi a tsakaninka da auta ne?

"Rasss haka gabanshi ya fadi Jin ankira sunan jidda,

"Ci gaba da magana Yaya Salim yayi yace" ko menene ya faru ai bai kamata ka barta ta fito da dare ba babu ko mayafi a jikinta, gashi da alama bata da lafiya fuska duk ta kumbura saboda duka, haba deeni bansan ka da wannan halin ba, akan me zaka dora hannun ka akan mace? Ko mace ma wae ace jidda! To duka duka ma nawa jiddar take ne,

"Kallonshi kawae deeni ya tsayayi cikeda mamakin Jin cewar auta ta fita to Ina taje ne?
Sai da gaban shi ya Fadi dayayi tunanin ko tana wurin umma,

Amma Jin yace"sai kaje tanacan gidana ka dakkota in Kuma Sadiq ya wuce da ita can gidane toh,

Sai hankalinshi ya dan kwanta dan yasan in ta Isa gaban umma da shatin duka to allah ne kadai zai wankeshi,

Hanyar da zata kaisu gidan Salim suka miqe har sun kusa Yaya deeni yayi tunanin Kila fa har Sadiq ya dauketa ganin Basu tare da shi Kuma tun fitowarsu a masallacin yayi gaba abinshi,

Wannan tunanin yasanya shi qara d'aga qafa har suka iso gidan aiko hasashen shi ya tabbata dan kusan yin karo sukayi dashi a qofar parlorn sai sauri yake zabgawa ga jidda biye dashi abaya anty ma'u na janye da hannun ta, kauce musu yayi suka shiga shi Kuma yacewa anty ma'u riqota muje,

Ganin yayah deeni ya nufe tane yasa Yaya Salim tokarewa a bakin qofar dan yau za'ayi ta qare tun da yayi rantsuwa to fa sunyi su qare amma bazata bishi ba inshallah,

ita Kuma jidda ganin yayo gunta da sauri tayi gun Yaya Salim
tun Kan suce komai tace,

"yaya meyasa ka zo dashi ni bazan bishi ba dan Allah kaji Yaya,

"Kiyi haquri kinji jidda Allah yabaki lafiya Kuma Kar ki sake shiga shirgin kowa Kar ki sake ki maimaita abinda kikayi bale asake yimiki wannan dukan kiyi harkar gabanki kawae kinji?

"Ni Yaya ban ta6a shiga shirgin ta ba itace take samuna tayita dukana ba laifin komai Kuma ko kasheni zatayi Yaya bazai amsheni ba Kuma ko lafiya banda tun safe saida Kuma na gayamasu,

Zaunawa Yaya Salim yayi ba shiri yana cewa" me kike nufi ne auta? Yi min bayani inji meya faru? Kina nufin hajara ce tayi Miki wannan dukan?

"Daga kanta tayi alamar eh'

"Me kikayi mata ne?

"Ta kawo bayani tiryan tiryan na abinda ya faru ta qara da cewa Kuma ka tambayi yaya kaji Yana gun Shima Kuma Allah ba da gangan naiyiba,

"Ajiyar zuciya ya sauke ya kalli ma'u kuje dakin ki,

Tashi tayi ta Kama jidda da jikinta yayi zafi rau suka nufi dakin,

Ran Yaya Salim in yayi dubu to dukansu sun baci Jin wai dukan jidda hajara keyi Kuma a gaban idonshi, shiru yayi tare da jinginar da bayanshi a kan kujerar da yake kai baice komai ba Kuma bashida niyyar yin magana saima lumshe ido da yayi,

Yaya deeni dake tsaye tun lokacin ya zauna Kan kujerar da ke facing din Yaya Salim yace" kayi haquri Salim,

Batareda ya dago kanshi ba yace "me ka yi min dazaka bani haquri deeni?

"Komai ma nayi Kuma nasani nakuma amshi laifina amma kasani wlhi ba'ason raina abubuwan da suka faru suke faruwa ba,

"Ni komai ba kayimin ba deeni dan haka no need ka tsaya kana wasu maganganu amma kasani nayi baqin ciki matuqa da faruwar hakan dan ko da auta bata aurenka kai mai iya tsayawa al'amarin tane matuqar kaga akwae cutarwa a ciki,  amma kasani wlhi wlhi wlhi kaji rantsuwa uku ko?
To duk matarka tasake ta sake d'ora hannunta akan jidda zatasan jidda tanada gata gaba da baya dan saimun dauki mummunan mataki akanta,

Shiru yayi ya lumshe idonshi ya dade ahaka shikadai yasan yanda yakeji aranshi na 6acin rai musamman yanda yaga bacin rai qarara a fuskar yaya Salim ya manta rabon da su sami sa6ani a tsakaninsu ko lokacin da suke yara basu cika samun matsala ba sai dai ma su hadu suyi fada tare idan anta6a dayansu,

Jikinshi yayi sanyi ainun, idanunshi har wani kadawa sukayi, sukayi jajir dasu, miqewa tsaye yayi sannan yace,

"Zan koma ka tadota mu wuce, sai lokacin Yaya Sadiq yayi magana yace,

"Yaya inaga zaifi kyau ka tafi kawai ni zan wuce da ita, ko kallonshi bai yiba ya dauki hanyar room dinda yaga sunshiga,

Tsayarda shi Yaya Sadiq yayi yace" brother na yi rantsuwa akan bazata bika ba, kaje kawai har tasami sauqi,

Janye shi yayi yacigaba da tafiya har dakin, tarar da ita yayi lullube anty ma'u na fama da ita tasha Koda tean data hada matane amma taqi,

Yaye bargon yayi ya Kai hannunshi a goshinta da sauri ya dauke Jin jikin nata yayi zafi sosai,

Kar6ar tean yayi ya tada ita zaune daqyar tasha kadan tasake kwanciya,

Cewa ma'u yayi ta samo Mata hijab tasaka, sai sannan tayi magana murya can qasa tace" Dan Allah yaya ka tafi abinka ni bazan bika ba, Ni bazan koma wannan gidan ba daga yau,

Murya can qasa shima yace "kiyi haquri kinji auta bazata sake dukanki ba kinji,

Ni dai ka tafi Yaya Sadiq zan bi, Ni wurin umma Zan koma,

Suna haka ma'u ta dawo da hijab din, tada ita yayi ya saka mata hijab din tana kuka ya riqo hannunta zuwa falo,

A bangaren yayah Sadiq kuwa bayan wucewar deeni yaya Salim yayi mishi magana ta hankali akan basai sunjewa iyayensu da wannan maganar ba koma menene ya kamata suyi settling din abin basai iyayen sun shiga cikiba amma tunda yarigaya rantse sai ya kaita hospital tunda bata da lafiya, akan haka suka tsayar da maganar,

Dukansu suna mamakin sauyawar deeni lokaci daya Dan ko amafarki bazakata6a mafarkin wani zai hantari jidda ya qyaleba bare akai ga duka, fitowa yayi da ita a gefen kafadarshi gud night kawae yace musu ya nufi qofa,

Tasowa sukayi dukansu inda Yaya Salim yace mishi ka bari Sadiq ya kaita hospital tunda jikin nata yaqi,

Zan kaita ya tafi kawae, saida suka Kai ruwa rana sannan ya yarda ta shiga motar Sadiq suka dunguma zuwa hospital bayan sunyi sallama da salim.

#comments

#votes

And

#share pls🙏

BAN TSANESHI BAWhere stories live. Discover now