chapter 13

244 13 0
                                    

♠♣♠♣♠♣♠♣
     ♠♣♠♣♠♣
            ♠♣♠♣
                  ♠♣

BAN TSANESHI BA

♠♣♠♣♠♣♠♣
      ♣♠♣♠♣♠
            ♣♠♣♠
                 ♠♣

story and written by
Asmau jafar
  (Ummu abdulhakim)
             &
zainab mukhtar
        (ummu maryam)

Kai gaskya comments dinku ya bani dariya sosai, wannan hadin Kai dazakuyiwa anty hajara to Ni dai gasky Zan shigawa anty uwargida sarautar Mata ne😎😎
Tunda har ita ummu Maryam tana bayan jiddalo to muma fa muna qarfi Dan haka kuzu muna jira💪🤣🤣

🅿️-1️⃣3️⃣

........Baki bude haka anty hajara ta shiga kallonshi har ya 6acewa ganinta, ta cika da matuqar mamaki Wai yau ita deeni yayiwa haka?
Had a ingizata ta fada Kan gadon, wani kukan baqin ciki ta Sanya tare da dukan katifa tana fadar NO! NO! Bazai yiwuba, wlhi bazai ta6a yiyuwaba dukanku zaku sani, haka taita surutai barka tai ita kadai a daki, Yan aikinta ma duk sunyi tsuru Jin hayaniyar kukanta,

Koda yayah deeni ya koma gurin yah Salim ma baice Masa wani Abu ya faruba Amma daka ganshi zaka shaida cewar ransa a 6ace yake,

**************

Su jidda kuwa Koda suka Isa shagon Mai dinkin bai qarasaba har sunce zasuje su dawo Kuma suka yanke hukuncin Zama a shagon har ya qarasa, Dan haka fita hafsat tayi ta sallami driver tare da cewar in angama zata kirasa,

Mj Yana dinkinsa su Kuma suna ta6a firarsu jefi jefi, sai dai duk a takure jidda kejin kanta sakamakon irin kallonda taga want dake cikin shagon nayi mata duk waiwayowar da zatayi sai sun had'a ido har abin yafara Bata haushi, daman Kuma ga haushin dukan da anty hajara tayi Mata Aiko suna had'a ido ta wurga Mai harara Hadi da juya Dan k'aramin bakinta,
Murmushi yayi Mata Dan shi ko kadan baiji haushin abinba hasalima dariya tabashi,
ganin haka sai kawai ta shareshi Bata sake dago Kai ta kalli gefenshiba,
Cewa hafsat tayi "ki Kira mna Bala kafin ya qaraso angama ko?
"Ok Tau"
Cikin mintuna qalilan da basufi 30 bala ya iso Kuma aka sa'a angama, godiya suka yimasa sannan suka fito daga shagon,
"Ganin zasu tafi kuma gashi baisamu damar yin magana da itaba yasa Shima ya fito, har MJ na fadin ranka ya dad'e tafiya zakayi ne?

Jinjina Masa Kai kawai yayi yafice, ko da ya fito tuni harsun shige mota da sauri ya shiga tashi ya tayar tare da bin bayansu, sai da yaga gidan da suka shiga sannan ya juya tare da fadin till we meet again my baby.

**************

Yaune ranar suna yaron yaci sunan baba Ibrahim wato Ibrahim khalil suna kiransa da Khalil, biki yayi biki anci ansha Mai jego da baby sun tashi da kyaututtuka na alfarma, abin sai dai muce mashaallah Allah ya raya Khalil,

**************

Rayuwar gidan yaya deeni kuwa sai dai muce Allah ya kyauta, Dan yayi matuqar daukar zafi da hajara ga Rashin kunyar da tayi agidansu gakuma maganganunda ta jefeshi dasu, iya tsawon rayuwarsa ba'a ta6a aibatashi koyimasa zargin Zina ba, Amma ace matarshi ta Sunnah CE tazama ta farkon gaya  Masa haka,
Kuma tarasa da wacce zatayimai wannan mummunan tunanin sai da qaramar qanwarshi da aka Haifa a hannunsu, to yaushe ma jidda tayi girman da namiji zai nemeta, Kuma ko za'a nemeta ma ace shi, shida inda yayi auran wuri da yanzu Yana kamarta, ranshi ya 6aci da abinnan sosai,
Gashi ba gwanin dukan mace ba, Dan ya dauki hakan amatsayin raini,

Dan haka tun lokacinda abinnan yafaru bata sake ganema kanshiba,
Kwata kwata yabar zaman gidan, bacci kawae KE kawoshi duk wani wasa da dariya dayake yimata ya daina, coffee da yake sakata ta hadamai duk ya daina saidai yayi da kanshi, abinci ma dayake yiyomsu take away suci a gida ya daina sai dai yaci abinshi can restaurant tunda dama bacin abincin gidan yake yiba yanzu haka ko ruwa yakeso bazaice ta Miko mashiba saidai yayi komai da kanshi gaba daya yafita harkar ta,
Daman Kuma hukuncin da yayi nufin yimata kenan ba duka ba zagi duk da cewar Shima Yana azabtuwa sai dai Dole yanuna Mata tayi kuskure,

Abangarenta kuwa tashiga damuwa sosai Amma girman kanta ya Hana tabashi hkr a cewarta Bata da laifi Dan munafintarta yayi Dan haka shizai Bata hkr,

Sai dai ganin yafita sabgarta kwata kwata sai abin yafara damunta hakan yasa ta Yankee hukuncin zata nemi qawarta Nadiya tanemi shawarar ta.

Wani yammaci da nadiyar tazo gidan hajara take labarta Mata komai dayake faruwa,

Nadiya ta numfasa sannan tace kinyi kuskure hajara aibai kamata ki daketaba dakin sani kawai ki shareta sai kin dawo gida ki kirani, gashi yanzu kinja deenin na neman rainamiki hankali, ai ko dukanta zakayi Kya jira har mu rufe idonshi yanda bazaiga laifinkiba gashi yanzu kinso ki lalata komai,

"Ni fa Nadiya ba abinda ya 6ata min Rai kamar wannan qauracemin da yayi Akan banzar yarinyar nan, har yayarsa na neman ta zageni kawai Dan naci uban yarinyar, Kuma kinsanni dai wlhi gabadaya ji nayi zuciya ta rufe da banci ubanta ba da kila sai na kwanta ciwo,

Babu damuwa ko yanzu zamuyiwa abin tufkar hanci,
Duk ki barni dasu zanyi Maki maganinsu, daman can Dan kince bakya ra'ayin zuwa neman taimako ga malamaine, da duk haka Bata faruba, ai Daman nace watarana sai kin nemeni da kanki,

"Ni dai yanzu mubar wannan maganar mafita kawai nake nema, badai wannan Yar iskar yayarshi anty Haj, take ko wa? Tace ban isaba , Aiko Zan nuna Mata na Isa Dan ba iya jidda ba har ita sai tasan tanemi ciman mutunci,

haka suka yita saqa da warwara daga qarshe suka yanke shawarar zuwa jibi zasuyi komai da komai, 

Da haka suka Yi sallama Nadiya ta wuce.

**************

A bangaren masu jego kuwa komai natafiya lafiya Lau, Dan yanzu haka ma umma ta gama tsare tsarenta Dan anty ma'u can gidansu zata koma tacigaba da wankan acan,

Duk da anty Salma taso tati zamanta acan amna umma take danan da can duk dayane,

Misalin qarfe 4 yayah Salim da yayah deeni suka shigo harabar gidan gaida umma suka yi a tsaitsaye sukace ta fito suwuce,
umma tace "su shiga suyiwa Mama maganah Dan tare zasu tafi,
Suka amsa da Tau, har harabar gidan su jidda suka rakosu, jidda kamar tayi kuka za'a tafin mata da Khalil dinta,
Fadin take anty ma'u
Zan dinga zowa duk weekend inaganin babana Khalil, duk sukayi dariya, suna daga masu hannu har suka fita gidan.

**************

Yau ce ranar da Nadiya zatakai hajara gurin malamin Dan shi qa'idarsace Mai lalura shiyake zuwa da kanshi, sunyi tafiya Mai nisa kafin suka Isa wani qaramin qauye duk da haka saidaa suka yi parking sukayi tafiya Mai tsawo sannan suka shiga wani wuri dakeda bukka kwaya daya tal,

Duk wani sharadi dazai gindaya masu ya gindaya ya Kuma Basu wata qwarya yace ta kalli tsakiyar ta Kira sunanshi da qarfi,

*****************

Yaya deeni ne zaune a office dinsa sai ganin yayi anturo qofar anshigo, dago da kanshi yayi cike d mamakin waye ya shigo Mai office without taking excuse,

Lokaci guda fara'ar fuskarshi ta dauke tamkar Wanda baita6a dariya ba sakamakon ganin zee da yayi qawar hajara cikin wasu damammun Kaya da suka bayyanarda tsiraicinta,

Cike dason ta dauki hankalinsa ta fara wani taku tana girgiza har ta kawo kusa dashi, Jan kajuerar da marar lafiya KE Zama tayiwa kanta masauki tana tamnar cingam,

Ci gaba da abinda yakeyi yayi tamkar baiga wani mutum agun ba, cikeda kissa tana karairaya harshe tace "my man kana qara burgenifa, wannan ko in kula da sham qamshi haka aidai ka dago kanka ko gaisawa muyi,

Tamkar tana magana da dutse haka yayi Mata shiru, tanata zuba ko lokacinta baiyiba, miqewa yayi zaifita a daidai lokacin Kuma Kiran Yaya Salim ya shigo wayarsa, dauka yayi Yana fadar "mamman ya ne?
Daga dayan bangaren yayah Salim yace "kana inane nazo gidanka bakanan,
Gani hospital amma yanzu zanfito ya ake cikine?

Ya fada lokacin da yakawo bakin qofar tareda baiwa Mai kula da office dinshi umarnin ya rufe Masa office din,

Yaya Salim yace" yaronka ne ba lfy dear tace jiya kwanan zaune sukayi....
Ai bai qarasaba yace subhanallahi mu hadu gidan yanzu.....

More Comments

More typing🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️

Comments
      and
share pls 🙏

BAN TSANESHI BAWhere stories live. Discover now