chapter 14

253 12 0
                                    

♠♣♠♣♠♣♠♣
     ♠♣♠♣♠♣
            ♠♣♠♣
                  ♠♣

*BAN TSANESHI BA*

♠♣♠♣♠♣♠♣
      ♣♠♣♠♣♠
            ♣♠♣♠
                 ♠♣

*story and written by*
*Asmau jafar*
  *(Ummu abdulhakim)*
             &
*zainab mukhtar*
        *(ummu maryam)*

Muna matuqar godiya sosai fans dinmu masu yimna sharhi iya wuya ana tare💪🤝

Wannan page din sadaukarwane agareku masoyan gaske
*Mom sa'adarht madoubee*, *anty juwairiya*, *sis adama aliyu*, *sis hauwa'u umar muh'd* (takwarar jiddalo)
Allah yabar qauna

🅿️-1️⃣4️⃣

.... Cike da tsananin mamaki zee ta bi qofar da kallo, ai ranta inyayi dubu to dukansu sun 6aci murmushin dake cike da bacin rai tayi tace "adai juri zuwa rafi wata rana tulu zai fashe"
Kwafa tayi sanban ta tashi ta fito da qarfin gaske ta doki qofar office din har sai da ta janyo hankalin mutane akanta, tana fita direct inda tayi parking ta nufa da qarfin gaske ta taka motar tabar asibitin,

.......gudu kawai yake shararawa kan titin cikin abinda baifi minti goma ya qaraso gidan anty salma dan ya riga yaya salim isowa, kasancewar mai gadin yayi mai farin sani yasa ya wangalemai gate din ya shigo daga ciki yayi parking,

Yaya deeni na matuqar qaunar yara shiyasa ya za6i yayi karatu bangaren da zai rika kula da yaran, a falo ya tarar dasu yana shiga falon bai tsaya wata wata ba ya kar6i yaron  yafara gudanarda  aikinshi,

sai da ya dauki tsawon lokaci yana dubashi yana yiwa anty ma'u tambayoyi, har fada sai da yyi mata akan arage cika daki da sanyi dan kuwa harda mura acikin ciwon nashi gashi tayi masa mummunan kamu, mik'a mata yaron yayi saboda zaije ya siyo magani, sannan a lokacin suka gaisa da kyau da anty,
Ai ko tace "ka riqe gaisuwarka deeni tunda baka ganniba sai yanzun da kagama da yaronka ko?
Murmushi yayi sannan yace" ba haka bane anty ina da niyyar mu gaisa da kyau ne shiyasa na bari har in gama da yarona,
Kai dai ba wani nan idonka ne ya rufe tunda dank'a ba lafiya, gashi sai faman fada kake tayiwa asma'un, ta fada tana dariya,
Ai anty ba fada kawai ba zaneta  zanyi idan tasake kai Ac qarshe allah,

Yaya salim data shigo yanzu ne ya tarar ana cewa za'a zane wani ya gaishe da anty har qasa ya durqusa, amsawa tayi cike da fara'a,

Sai da suka gama gaisawa sannan yake tambayar kai kuma fa wa zaka daka ne? Naji kana fadin zaka zane...

Bai barshi y qarasa ba yace au ashe kaji to matar ka zan zane matsawar bata daina saka min yaro acikin iskar fanka ko ac ba,

Sanin halinsu da anty salma tayi yasa ta tashi ta barmusu gurin, dan tasan yanzu zasu fara,

Ai ko tana fita yaya salim kamar mai jira sai cewa yayi " kana nufin sai ta zauna acikin zafi kawai dan yaronka to zaneta kasha mamaki dan wlhi allah rama mata zanyi, tsaki yayi yace banda lokacinka yanzun,

Fita yayi ya nufi parking lot kai tsaye wani babban chemist ya wuce sai da ya hado komai da komai sannan ya dauki hanyar dawowa,

Koda ya dawo anty kawai ya tarar a falon, ita ke gaya masa cewar suna falon baqi,
can ya zarce dan dakko khalil yasha magani,
Tun bakin qofar yake sallama amma shiru hakan yasa ya murda handle din kawai ya shiga,
Tsaye yayi cike da mamaki yana kallon salim yanda ya taqarqare yana romance dinta ai bai san lokacin da yaja wani wawan tsaki ba, yana fadar kai fa dan iskane fa shine kadawo nan dan kaji dadin yin iskancin ka ko?
Ai kunya kamar qasa ta tsage ma'u ta shige haka ta miqe jiki ba qwari ta nufi kofar fita, yaya salim ne yace "ka ga ka korar min baby ko?
"Mtswww" a hakan kake cewa abar ma matarka ai kafin ta gama wankan ka dirka mata wani dan iska kawai,
"Eh" naji dai,

Yaya deeni yace "zo nan big boy kasha magani ko? Ya fada yana yimasa wasa, maganin ya ciro sai da ya bashi ko wanne sannan yace wa yaya salim dan rike min shi in gyara wannan, ya fada yana miko shi, yaya salim da ya baje akan kushin yana wani lumshe ido ya dago ya karbeshi,
"Mtsww an dai ji jiki"
Eh din ina ruwanka ne?
Saida ya gama mayarda komai a muhallinsa sannan ya mika hannu "zonan yaron daddy mu tafi ko? wannan daddyn baya cikin hayyacinsa,
Dariya sosai yaya salim yayi sannan yace kana nufin anan zaka barni?
To baka isaba wlhi k'afarka k'afata,

Au ai na dauka anan zaka kwana shiyasa, suna tafe suna.  shaqiyancinsu dasuka saba har babban falon gidan,

************

A bangaren anty hajara kuwa koda ta karbi kwaryar sai ganin fuskar yaya deeni tayi aciki da qarfi bokan yace ki kira sunanshi nace,
*NURADEEN* *NURADEEN* *NURADEEN*
Sai da ta kira sunanshi sau uku sannan ta dakata,

Yaya deeni har sun shigo falon sun kai zaune yana yiwa anty ma'u bayanin yanda zata baiwa khalil maganin sai ji yaji kamar  ana buga mashi guduma akai  dafe kanshi yayi da hannunsa yana furta kalmar innalillahi wa'inna ilayhi raji'unn,
Duk suka mayarda hankalinsu kanshi, kirana biyu da tayi yasake dafe kanshi da qarfi ai tanayin na uku ya zube gurin asume, cike da tashin hnkli anty ta mike ta nufo shi tana jijjigashi, ai yaya salim da gudu ya kwasa yayi waje mai gadin gidan y kira suka kamashi sukayi mota dashi a guje ya bar gidan sai asibitinda yaya deeni ke aiki ya yi parking,

Duk abinda ya faru ba wanda su gajara basu ganiba acikin qwaryar wata dariya yayi yace aiki y kammala, daga yau bazai sake ganin laifinki ba komai kikayi kuma zai tsani yarinyar tsana mafi muni, wani abu ya miko mata adunkule yace wannan zakije ki binneshi acikin gidanki duk bayan wata uku zaki budeshi ki fasa kwai daya ki juye ki sake rufeshi, koda suka tambayi ladar aiki sai cewa yayi suje sai bayan wata uku su dawo su kawo mai,

Hankali kwance suka fito daga bukkar cike da farin cikin samun nasara, basu suka isa gidaba sai yamma,

Yaya deeni kuwa direct emergency aka wuce dashi sai dai duk bincikensu basu gano komai ba hakan yasa suka daura mai drip akayi mai allurar bacci, bashi ya tashiba sai yamma mika yayi tare da mikewa zaune yanason karanta addu'ar tashi daga bacci yanajin bakinsa yayi mai nauyi, kallon dakin ya shiga yi cike da mamakin me kuma ya kawoshi hospital duk iya tunaninsa yakasa tunowa sai kawai y basar,

Yaya salim ne ya shigo dakin tare da doctor dubashi yayi sannan yabasu sallama.

Gidanshi ya wuce dashi har ciki ya kaishi sannan yace zai kawo mai motarshi zuwa anjima.

Kwanci tashi babu wuya agurin allah abubuwa da dama sun faru ko ince suna kan faruwa domin ko abangaren anty hajara  sai dai muce komai zam zam, tasamu biyan buqata yanda takeso haka takeyi, godiya ko tayi wa nadiya ita fin kwantena,
Daman can yaya deeni ba mutum bane daya cika son mace ta dinga fita anyhow ba, yanzu kuwa damar farko da hajara tafara samu shine kullum tana waje yau batanan gobe bata can,

Kwata kwata yaya deeni ya rasa abinda ke damunshi abadini ranshi bai yi mishi dadi amna kuma azahiri yakasa yi mata fadan ta daina,

Yau ma kamar kullum zaune yake a falon umma yana tunanin rayuwa, su jiddane suka shigo suna kwasar dariya ai jin muryarta kawae dayayi yaji wani 6acin rai mai tsanani ya kawo mai ziyara tsawa ya daka musu sai da suka firgita umma tace lafiyarka kuwa deeni? Metasa zaka rikitamin yara?

Ganin sunyi cirko cirko gashi kuma umma nayi masa fada yasa ranshi y qara zafi wata tsawar ya daka musu yace su bace mai da gani, ai da sauri suka bar falon,

Fada umma tashiga yimai na tanda yake saurin daukar zafi yanzu, sai da ta gama  yi mai fada sannan ta dora da yimai nasiha, har cikin ransa yaji dadin nasihar da umma tayi mai dan har yanayin fuskarshi ya sauya yadan saki ranshi,

Sai dai jin umma tace "bari insa qanwarka ta kawo ma abinci kaji!

Ai tare da umma ma suka miqe yana cewa " no am ok abarshi kawai,
Ba yanzu kace kuma akawo maka abincinba?
No na fasa umma zanje restaurant inci acan,
Jin ya ambaci restaurant yasa ta kalleshi sosai, kamar ya zakaje restaurant? Gidan ka fa?
Cike da qosawa da maganar yace to innaje gidan zanci, yana fada yasa kai yafice a falon,

Kasake umma tayi tana kallonshi tabbas a 'yan kwanakin nan ya sauya mata sosai to me ke damunshi ne haka?

Ajiyar zuciya ta sauke tana fadar komenene inshaalaah zanci gaba da yi maka addu'a deeni.

Koda ya iso gidanshi kamar dai yanda ya tsamnata bai iskota a gidan ba......

Comnent
    and
share pls🙏

BAN TSANESHI BAWhere stories live. Discover now