chapter 11

264 15 0
                                    

♠️♣️♠️♣️♠️♣️♠️♣️                     
      ♠️♣️♠️♣️♠️♣️
           ♠️♣️♠️♣️
                ♠️♣️

*BAN TSANESHI BA*

♠️♣️♠️♣️♠️♣️♠️♣️    
      ♠️♣️♠️♣️♠️♣️.
            ♠️♣️♠️♣️
                  ♠️♣️

*STORY AND WRITTEN BY *ASMAU JAFAR*
*(ummu abdulhakim)*
            *&*

*ZAINAB MUKHTAR*
*(Ummu maryam)*
Aminan juna 👭🏻

*Sister juwairiya barda thanks alot for caring Allah yabar qauna*🙏

🅿️1️⃣1️⃣

........Sun tarar dasu maman jidda a tare kamar ko yaushe,  kafin su K'arasa ciki anty ma'u ta k'ara gyara zaman mayafinta tana Kara sunkuyar da Kanta k'asa, har kasa ta durkusa ta gaishedarda sarakunnanta, Mama ce tace' ohni! Shikenan dai Salim ya shiga tsakaninmu da ke, to ai sai ki tashi kihau kujera ko asma'u Kin zauna a kasa?, murmushi tayi tana cigaba da wasa da yatsun hannunta batareda ta tashi ba,

Sai a lokacin mmn jidda tace' auta kuje dakinki tunda tak'i sakin jikinta Anan kuje can zatafi sakewa,

Jidda tace' anty ma'u Wai muje dakina? Ta fada tana dariya, hararar wasa anty ma'u tayi mata,
Mama tace "ance ki tashi shine sai kin tsaya wani tmbyrta dan salo, kafin ta karashe maganar ma har sun bar falon.

Fira sukeyi cike da nishadi dayake kuma ba wasu shekaru masu yawa anty ma'u ta basu ba, gashi bata da girman kai ko kadan,
Fira sukeyi jidda na basu labarin fitarsu da yayah deeni,
baby tace" dallah malama munji sai kiyi shiru haka ai,
Hafsat tace" ke dai baby fito fili kice kinji haushi ba'aje dakeba,
Baby tace" fada mata dai hafsy kuma taqi tabarni haka duk aka tada zancen sai tayi jinini,
Kuma fa nazo mata d tsaraba, inaga inda acan na cinye abini da sai ta sume akan haushi,
Suka kwashe d dariya dukansu,

Haka suka yi ta nishadinsu dan anty ma'u wuni zir tayi musu sai yamma sannan ta wuce,

***************

A kwana a tashi har hutunsu ya qare su jidda an zama manya an shida aji shida a makaranta,

Ta qara kyau da girma mashaallah makerin budurci y gama qerata tsaf daman can gata da shegen kyau, ba abinda yafi daukar hnkli a fuskar  jidda irin siririn hancinta ga dimple ko murmushi tayi sai sun lotsa, tana da madaidaitan breast kasanta kuwa ai in ta juya baya bazaka taba dauka yarinyace yar 17 ba, gata da fara'a kuma sam jidda bata da son jikinta ko  kadan dan zuwa ynzu kome za'a dafa a gidansu ko gidan umma itace  ke yin rabin aikin dan wani lokaci ma sai umma ko mamam jidda sunyi tayi mata fada akan ta zauna ta huta hakanan, sai dai tace tau kawai amman badan ta yarda zata daina ba takance to ne kawai, daga baya kuma da umma ta rutsata tana fada sai tace" to umma zan rage kinga yan aiki daga yau su riqa dafa shinkafa ko tuwo ni kuma sai indingayin miya ko? To qarshe dai a haka aka ajiye dan tasan jidda da kafiya ko an ce a'a sai tayi tunda tayi niyya.

************

A bangaren yayah deeni kuwa har ynzu shiru kakeji kamar an aiki bawa garinsu dan ko ko 6atan wata bata ta6ayiba tun bai damuwa sosai har yazo ya fara damuwa amna ita madam din ko ajikinta ,

*************

Duka familyn biyu daka gansu zaka karanto tsantar damuwa a kallon farko da zakayi masu,

Domin ko tun jiya da da yamma anty ma'u ke durqushe tana  aikin abu daya, amma shiru har yanzu gashi har 3 na neman yi kuma likitoci sunce qarfe 1:30 zata haihu,

Yaya salim zarya kawai yake yi a qofar labour room din,

Yaya deeni ya tari dr. Yazid yanas tmbyrshi har ynzun, kasancewar a asibitin da yake aiki a ka kaita, dr. yake inshaallah ynz zata haihu ku qara hkr, Sauri sauri haka ya barsu anan y koma ciki, har suna shawarar yi mata aiki  sai allah yyi ikonshi akanta dan ko tanayin wani nishi sai ga yaro ya fado kukanshi ya karade dakin, ajiyar zcy ta sauke tana furta alhmdllh, likita na tsaye kanta yana gyarata yayinda nurses suka dauki yaron sukaje su gyarashi shima, dr na fitowa umma da mama har rigerigen tambayar shi baby sukeyi, dan sunji kukanshi lokacinda yazo duniya, murmushi yayi yaba deeni da salim hannu suka yi musabha yana rike da hannun yyah salim yace "congratulations ansami baby boy",

Ai murnar da yaya salim yayi bata faduwa alhmdllh yake ta furtawa yana tmbayar ina matarshi,
Dr yace " calm down tana hutawane anjima kadan zaka ganta, baby kuma ynzu nurse zata kawoshi ku gunshi in an gama kimtsashi,

Yayah deeni yayi carab yace wane babyn za'a kawo a ganshi?
Tabb ai sai dai su hakura inje indauko masu hoto su gani dan baza'a fito dashi ba cikin iskan nan, kalan yaje mura ta kamashi,

Umma ce tayi mai daquwa, ungu ban deeni, ja'irin yaro kai, haka kawai kace baza'a fito mana da maigidan mu gani ba?
Duk jiran nan da mukayi kace sai mun sake wani jiran to maza je ka fito mana dashi mu ganshi,

Yaya deeni yace" allah umma iskan nan tayi mai yawa fa,

Sai a lokacin mama tace" to mu kam indai ma'u nanan lfy ai shikenan, d'a kuma kuyi ta rokon abinku, dama ni ban son mijin, na barwa umman taku, dariya sukayi dukansu yayinda deeni ya shiga ya fito musu da yaron, yasha tufafinsa masu kyau da laushi sai motsa dan karamin bakinshi yakeyi,
Yaya Deeni sai qara rufa mai towel din yakeyi yana mitar umma ta dage sai anfito dashi, huduba yayi mai a kunne tare da sumbatarshi a gishi ya miqa shi ga yayah salim, ai yayah salim baki yaqi rufuwa sai washeshi yakeyi,
Shima dai a karshe addu'a yati mai ya sunbaceshi sannan ya bada shi ga deeni, yaya deeni yace" to umma gashi amma fa wannan maigidan tsada gareshi dan haka next time bazai zo ba sai dai ki tarar dashi inda yake, y fada yana murmushi,

Umma tace'  to bazan karba ba sai da kuka gama rashin kunyarku dasu sumba da komai sannan zaku kawo mna shi,
Yace " yi khr ki karba mna umma wayake fushi da na qarfen... Hhhh
Koda aka basu sallama direct gidan umma suka wuce salim baiso b a amma ya ya'iya,
Hidima akeyi kala kala, sai kace yaune sunan,

Su anty jidda kuwa ai ba'a magana domin ko yaushe tana nanike da yaron in yaya deeni suka shigo yayi ta fada wai adaina jagwalgwalashi a ajiyeshe ya huta,
Aiko jidda ta fara 6ata Rai kenan,

Ran kwana na hudu da haihuwar ne aka kawo kayan fitar suna, wooooo ho hooo tsayawa misalta kayan zai daukemu lokaci Mai tsawo kawai dai ku qiyasta d kanku, domin ko ko Yayah deeni set din akwati Mai shida yayiwa baby da Mai jego, Kaya sai dai muce Masha Allah,

Ana gobe suna kowa ka gani a gidan cikin safa da marwa yake anata faman aiki, can kuryar dakin da Mai jego take na hango anty hajara ansha wani lafiyayyen leshi daka ganta kaga matar manya, Kiri Kiri taqi tashi ayi aiki da ita,

Misalin qarfe 4:30 su Yaya deeni da yayah Salim suka shigo kawo drinks, bayan sun aje ne suka K'arasa ciki wurin maijegon Dan dama tace tanason magana da Yaya Salim sai suka shigo,

Karbar babyn Yaya deeni yayi yace to angon karni sai kuje kaji menene Dan baza'aje da yarona ba, eh din ai ko bakace ba bazamuje dashiba wayasani ko kasaka Mai camerar da zata yo make satar amsar soyayyarmu, kanka akeji Ni dai Inka Dade Allah bazaka tarar Dani ba,

Wayarsa ya dauko Yana daukar babyn pic wani Kuma ya daukesu tare, ko da Yaya Salim ya dawo wayarshi na hannun anty hajara tana ganin pic din bisa tsautsayi shi Kuma ya fito ya manta wayar a hannun anty hajara suka wuce Dan dama suna ta fafutukar masaukin bakinsu, inda zasu gudanar da reception dinsu.

Ci gaba tayi da kallon wayar wani tayi murmushi wani tayi dariya, a zucciyar ta takecewa gsky honey kyakkyawan qarshe ne, wani pic dinshine taketa zooming ya bala'in yi mata kyau, dakyar dai ta wuceshi ta tafi gaba sai dai Nan take numfashinta yafara barazanar daukewa saboda tozali da tayi da hoton wacce tafi tsana a Kan komai a duniyar Nan, kasake tayi tana ci gaba da kallo Aiko sai ga videon ranar ta gani, kwalalo ido tayi cike fargaba tare da mikewa tsaye ta nufi hanyar waje gadan gadan.......

Asmy jafar ce da ummu Maryam KE muku fatan alkhaeri🤝

More Comments

More typing 🤸🏻‍🤸🏻‍

Comments
     And
Share pls🙏🙏

BAN TSANESHI BAWhere stories live. Discover now