chapter 23

237 9 0
                                    

♠♣♠♣♠♣♠♣
     ♠♣♠♣♠♣
            ♠♣♠♣
                  ♠♣

*BAN TSANESHI BA*

♠♣♠♣♠♣♠♣
      ♣♠♣♠♣♠
            ♣♠♣♠
                 ♠♣

*story and written by*
*Asmau jafar*
  *(Ummu abdulhakim)*
             &
*zainab mukhtar*
        *(ummu maryam)*
*Aminan juna 👭🏻*

*_________________________________________*

*Dedicated to mom sa'aderht madoubee 🌹iya wuya muna together besty Allah ya bar qauna*

*_______________________________________*

*Big sis munyi kewarki sosai da sosai muna Miki fatan alkhaeri da Kuma fatan gamawa da duniya lafiya @anty juwairiya barda, luv you so much 🥰😍❤️antynmu Allah yaraya mki zuri'a ysa musu albarka*

*_____________________________________*

*Jinjina ga sis adama aliyu, sis hauwa'u Umar takwarar jidda auta Allah yabar qauna😂*

*_____________________________________*


*🅿️-2️⃣3️⃣*

.........................Saboda tsananin kukan da tasha yasa bata ko yi ta Kan wayar ba sai da safe Allah yasa dai ta jona wayar charge, sun da safe sai ga kiran umma ya shigo wayar, bayan sun gaisane umma ke tambayarta yanayin rayuwar ta agidan sai dai juyin duniya umma tayi amma jidda taqi fada mata komai dan tsoron abinda zaije ya dawo hakan yasa umma tabarta duk da Sadiq ya gayamata komai.

Kwanci tashi babu wuya har su jidda sun zana exam din first semester sunje break, wannan hutun zan iya cewa dama ba'ayiba dan yazamar jidda wani qangi kasancewar kullum tana gidan ba school wahala da zagi kuwa sai abinda ya qaru batajin dadin gidan ko kadan damar guda yanzu Yar wayar dake gareta inta shige daki taita game kuma gashi halima ta Buda Mata WhatsApp to fa Nan ne kawai takejin Dan sanyi, Tasha saka no hydar a wayar da niyar ta Kira sai Kuma wata zuciyar ta kwa6eta ta fasa, tasan da ace shita aura da duk wannan abin bai faruba.

A daren wata ranar assabar ne bayan magrib Gama sallarta kenan tana zaune Kan darduma hajara ta qwalo Mata Kira da sauri ta fito tace taje ta kawo musu abinci Anan falon zasuyi dinner, sai da ta gama jere komai a gabansu sannan ta durqusa gefe dan tayi serving nasu, tsautsayi yasa miyar stew ta zube a qafar hajara kuma gashi Bata dade da sauketa ba da zafinta, ai wani irin ihu da hajara tayi,
tasaka  dayar qafar ta hankadata itama jidda ba 6ata lokaci tasaki nata kukan cikeda baqin ciki hajara ta miqe tayo kanta gadan gadan da sauri ta tashi tayi Kan deeni dake kan kajuera qanqameshi tayi sosai tana cewa,

"Yaya Dan Allah kace Mata tayi hakuri wlh ban yi da niyya ba, Dan Allah karka bari ta dakeni Banda lfy tun safe yaya, pls kiyi haquri anty wlh tsautsayi ne,

Baci ran hajara ya qara yi ganin jidda kwance Kan mijinta harda qanqameshi aiko tayo kansu,

Miqewa deeni yayi da jidda a jikinshi itako sai qara shigemai take Kuma da gaske ne batada lfy Dan jikinta har da zafi yafarayi Kuma Shima yaji dumin jikinta,

"Pls ki barta batada lfy tsautsayine Kar ki daketa.

Baki bude hajara ke kallon shi cike da mamakinsa dan tunda jidda take gidan Bai taba Sanya baki a maganar suba idan jiddar tayi Mata wani laifi,

" yanzu dear kana gani a gabanka a Kan idonka yarinyar nan ta watsamin miya Mai zafi Dan baqin ciki da iya munafurcinta amma kake gayamin wani tsautsayine wato bayanta zaka bi kenan Dan taji dadin yimin wata muguntar a gobe Koh? to wlhi yau ka janyo mata bala'i da masifa a gidannan Dan yau ko na lahira sai yafita Jin dadi,

Fizgo ta tayi yayinda ita Kuma jidda ta qara rigeshi gam, janyota tayi da qarfin gaske sai da ta baro jikinshi kan dole haka ta dinga janta har qofar fita ta zare key din suna fita ta kulle qofar ta baya,

Deeni yayi bugun duniyar nan amma taqi bude mai qofar Kuma tabar key din a jikin door din yanda bazai iya bud'ewa ba,

Tun kafin ta fara dukanta ta fara ihun neman agaji kasancewar anyi magrib dare ya farayi yasa garin  shiru, kabiru driver ne yajiyo ihunta daga inda yake da sauri ya taso Yana baiwa hajara hakuri Amma kasancewar mutunci yayi Mata qaranci yasa ta fatattakeshi taci Mai mutunci dole yabar gun,

Duka sosai tayiwa jidda har saida taga tana fitarda numfashi sama sama sannan ta barta a nan yashe a qasa ta Kuma rufe qofar,

Bata tarar dashi a falon ba dakinta ta wuce Kai tsaye Dan ya bata haushi sosai ba kadan ba.

Jidda taci kuka har ta gode Allah zazzafan zazza6i ne ya sauko mata da qyar ta tashi tana layi tayi hanyar falon dan wani irin sanyi takeji sosai sai dai tana murda handle din tajishi a rufe duqawa tayi agun ta dade tana knocking amma shiru gashi ko hijab babu a jikinta bale tayi tafiyarta,

Qarshe dai dataga ba sarki sai Allah haka ta tashi ta Kama hanyar barin gidan bayan tasaka silifas dinda ke gurin, dankwalin ta ta warware ta rufa a kanta,

Tsayarda ita Kabiru driver yake sonyi amma fir taqi tsayawa bale ta saurareshi fita gidan tayi a yanda take babu hijab ko baba Mai gadi yayi iya yinshi amma bata saurareshiba,

Baba yace wa Kabiru ya dakko mota ya je ya kaita inda zataje tunda ba mayafi a jikinta,

Tana fita hanyar gidan Yaya Salim ta dosa kasancewar unguwa daya suke, tafiya takeyi tana kuka qasaqasa hasken mota tare da horn taji a bayanta Kuma tanada tabbacin motar gidan yy deeni ce hakan yasa gabanta ya Fadi dan ta qudurta a ranta bazata koma gidan ba,

Muryar Kabiru taji Yana cewa "kiyi haquri hajiya ki shigo insauke ki a gida Kinga dare yayi,

Ko kallonshi batayiba tace yatafi kawae ta gode, daga haka tacigaba da tafiyarta yayi magiya har ya gaji Amma taqi shiga dolenshi ya barta ya koma gida bayan yaga shigarta a gidan Yaya Salim,

Tun a compound din gidan taga motar Yaya Salim da qarfi ta sauke ajiyar zuciya dan dama Rashin na transport ne yasa tazo gidan Yaya Salim dake kusa yanzu kuwa ga Yaya Sadiq Nan in yatashi tafiya su wuce tare.

Knocking tashigayi da qarfi Dan ta qagu ta nemi guri ta Dan kwanta saboda zazza6in da take fama dashi.

Anty ma'u na bude qofar ta zaro ido ganin auta da dare Kuma ba hijab sannan ga fuskar ta duk shatin mari da duka ne hawaye faca faca a Kan fuskar,

"Lafiya jidda meya sameki?

"Jin ta ambaci sunan jidda yasa suka miqe suka nufo gun qofar, ra6awa jidda tayi ta gefenta ta shigo falon tana kuka,

Zubewa tayi Kan kushin tana kuka sosai kamar ranta zai fita,

Dukansu suka rufo Mata baya suka dawo falon, kallon ta Yaya Salim yakeyi cike da tausayi qanwar tashi Wanda ko ba'a fada maka ba kasan dukanta ne akayi,

Zaunawa yayi a gefenta yace,

"Jidda me akayimiki?
Me ya sameki haka ne Kika fito ko hijab babu a jikinki eyye?

Muryar ta har ta dashe tace" sanyi nakeji ku rufamin bargo daga haka ta qara dunqule jikinta guri daya tana Sheshekar kuka, da sauri ma'u tace to tashi muje daki zakifi Jin dadin kwanciya kasa tashi tayi saida anty ma'u ta kamata ta kaita dakin ta rufa Mata bargo ta kashe Ac sannan ta fito,

Tarar dasu tayi kowa da abinda yake tunani duk sunyi jigum dasu,

Tacewa Yaya Salim ko dai a hada Mata tea ne tasha sai tasha magani,

Miqewa Yaya Sadiq yayi yace" ki barta kawae ba komai in munje gida can sai tasha daganan ma sai mu wuce hospital, daukar key dinshi yayi yace"ki tasota mu tafi,

Kallon shi Yaya Salim yayi kafin yace "Ina zakaje da ita Sadiq? Ashe baka da tunani kallon anty ma'u yayi yace"dakko min phone dina in ji meke faruwa,

Yaya Sadiq da ranshi ya gama 6aci ya kalli Yaya Salim yace" Kar ka kirashi Yaya kabarshi kawai dan wlhi ko ka kirashi bazai koma da ita gidanshi ba,

Shareshi yayi kasancewar wayar har tafara ringing, ganin baiyi picking ba yasa ya kalli time yaga lokacin isha yayi yace" zo mu tafi masallaci har an tada sallah may be Shima Yana masallacin..........

#comments

#votes
    
And

#share pls

BAN TSANESHI BAWhere stories live. Discover now